Abin Da Muke Da Shi A JW.ORG
LABARAN SHAIDUN JEHOBAH
Tana Ci-gaba da Jimre Matsalolinta
Virginia ta yi fiye da shekaru 23 tana fama da ciwon da ke hana ta magana da kuma motsa jiki, amma begen da take da shi yana ƙarfafa ta da kuma kāre ta.
A jw.org, ka duba LABURARE > TALIFOFI > LABARAN SHAIDUN JEHOBAH > JIMREWA DA MATSALOLI.
KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU
Ruhu mai tsarki ya hure Maryamu ta ja-goranci matan Isra’ila don yin waƙar nasara a Jar Teku. Za mu iya koyan yadda za mu kasance da ƙarfin zuciya da bangaskiya da kuma sauƙin kai daga misalinta.
A jw.org, ka duba LABURARE > TALIFOFI > KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU.