Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Satumba p. 3
  • Ka Guji Yada Karya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Guji Yada Karya
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • “Marar Wayo Yana Gaskata Kowace Magana”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Ci Gaba Da Aikata Abubuwa Da Ka Koya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka San Gaskiyar Lamarin Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Intane Yadda Za Mu Yi Amfani da Shi a Hanyar da Ta Dace
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Satumba p. 3

RAYUWAR KIRISTA

Ka Guji Yaɗa Ƙarya

Wata mata tana mamakin wani abu da ta gani a wayarta sa’ad da take cefane.

A yau, za a iya tura wa miliyoyin mutane saƙo da wuri ta rediyo da talabijin da intane ko kuma ta wasu hanyoyi. Amma bai kamata mutanen da suke bauta ma “Allah na gaskiya” su riƙa yaɗa ƙarya ko ba da gangan ba. (Za 31:​5, Littafi Mai Tsarki; Fit 23:1) Idan muka yaɗa ƙarya, za mu iya ɓata sunayen mutane. Idan kana so ka san ko wani abin da ka ji gaskiya ne, ka tambayi kanka:

  • ‘Na tabbata da wanda ya faɗi abin?’ Wataƙila wanda ya ba da labarin bai san ainihin gaskiyar batun ba. Mutane suna yawan ƙara gishiri a labari, don haka ka yi hankali wajen yaɗa labarin da ba ka san tushensa ba. Da yake an yarda da dattawan ikilisiya cewa suna faɗan gaskiya, zai dace su yi hankali wajen yaɗa labarai musamman waɗanda ba su san tushensu ba

  • ‘Maganar gulma ce?’ Idan labarin zai ɓata sunan mutum ko wani rukuni, zai dace kada mu yaɗa shi.​—K. Ma 18:8; Fib 4:8

  • ‘Za a iya gaskata da labarin?’ Ka yi hankali sa’ad da ka ji jita-jita

KU KALLI BIDIYON NAN TA YAYA ZAN GUJI YAƊA GULMA? SAI KU AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

  • Wani yaro rike da katako da takuba ke harba.

    Bisa ga Karin Magana 12:​18, ta yaya kalmominmu za su iya yi wa mutane illa?

  • Wasu mutane sun taru suna gulma.

    Ta yaya Filibiyawa 2:4 take taimaka mana mu san abubuwan da ya kamata mu faɗa game da wasu?

  • Wani mutum ya juye ma wani mai gulma baya.

    Me ya kamata mu yi sa’ad da mutane suka soma faɗan abubuwan da ba su dace ba game da wasu?

  • Wani mutum yana gulma, wani kuma ya saka tufafi kamar dan jarida yana rubutu.

    Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu kafin mu soma magana game da wasu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba