RAYUWAR KIRISTA
Me Za Mu Iya Koya Daga Waƙoƙin JW?
Waɗanne waƙoƙin JW ne ka fi so? Kuma me ya sa? Ka lura cewa waƙoƙin nan suna nuna abubuwan da muke fuskanta a rayuwa? Tun da yake waƙoƙin sun tattauna jigo iri-iri da kuma al’adu dabam-dabam, kowa zai ji daɗinsu. Amma ba a shirya waƙoƙin nan don nishaɗi kawai ba.
Kowacce waƙa tana koya mana darasi game da yadda za mu yi rayuwa da kuma wa’azi. Wasu waƙoƙin game da karɓan baƙi ne, da haɗin kai, da abokantaka, da ƙarfin zuciya, da ƙauna, da kuma bangaskiya. Wasu kuma game da yadda mutum zai komo ga Jehobah ne, da gafarta wa mutane, da kasancewa da aminci a koyaushe, da kuma saka ƙwazo a ibadarmu. Akwai wata waƙa ma da ta yi magana game da yadda za mu yi amfani da wayarmu a hanyar da ta dace. Waɗanne darussa ne kuma ka koya daga cikin waƙoƙin JW?
KU KALLI WAƘAR NAN ALJANNA TA KUSA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Waɗanne albarku ne ma’auratan suke tunani a kai?—Fa 12:3
Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu cewa Jehobah zai cika alkawuransa?
Waɗanne abubuwa masu kyau ne za su faru nan ba da daɗewa ba?
Ta yaya begen da muke da shi zai taimaka mana mu jimre matsaloli yanzu?—Ro 8:25