DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 7-9
Jehobah Ya Albarkaci Babban Taro da ba Za A Iya Ƙirga Ba
7:9, 14-17
Me ya sa Jehobah ya albarkaci babban taron?
“Suna tsaye a gaban kujerar mulkin [Jehobah],” suna nuna goyon bayansu ga matsayinsa na maɗaukaki
“Suna sanye da fararen riguna,” hakan ya nuna cewa suna da tsabta a gaban Jehobah domin sun ba da gaskiya ga hadayar Kristi
“Suna yi masa hidima dare da rana,” suna bauta ma Jehobah da ƙwazo kuma babu fasawa
Me zan yi domin in kasance cikin babban taron?