Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Oktoba p. 8
  • Jehobah Yana Son Mu Kasance da Tsabta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Son Mu Kasance da Tsabta
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Tsabta—Mecece Ainihi Take Nufi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Yaya Muhimmancin Tsabta Take?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Allah Yana Kaunar Mutane Masu Tsabta
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Tsabta Me Ya Sa Take Da Muhimmanci?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Oktoba p. 8
Wani dan’uwa yana tsabtace wurin ba haya a Majami’ar Mulki

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Yana Son Mu Kasance da Tsabta

Iyaye da yawa suna koya wa yaransu yadda za su kasance da tsabta. Shi ya sa sukan gaya musu: “Ka wanke hannunka. Ka share ɗakinka. Ka wanke kwano. Ka zubar da datti.” Amma Jehobah ne ainihin wanda ya koya wa dukanmu yadda za mu kasance da tsabta. (Fit 30:​18-20; M.Sh 23:14; 2Ko 7:1) Idan muna tsabtace jikinmu da kayanmu, muna ɗaukaka Jehobah ne. (1Bi 1:​14-16) Gidajenmu da mahallinmu fa? Wasu mutane suna zubar da datti duk inda suka ga dama, amma mu Kiristoci muna iya ƙoƙarinmu wajen tsabtace gidajenmu da mahallinmu. (Za 115:16; R. Yar 11:18) Yadda muke zubar da ledar minti ko gwangwani ko kuma cingam zai nuna ko muna da tsabta ko a’a. Muna so mu yi iya ƙoƙarinmu “mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne” a dukan abubuwan da muke yi.​—2Ko 6:​3, 4.

KU KALLI BIDIYON NAN ALLAH YANA SON MU KASANCE DA TSABTA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa wasu suke ƙin tsabtace jikinsu da mahallinsu?

  • Ta yaya Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta nuna cewa Jehobah yana son tsabta?

  • Ta yaya za mu ɗaukaka Jehobah a ayyukanmu?

Wani mutum zai shiga motar dansa mai datti; uban da dansa suna tattauna ka’idodin Jehobah game da tsabta; wasu firistoci biyu na Isra’ila ta dā suna kusa da bahon wanki; ’yan’uwa da za su je wa’azi sun fito daga motar yaron kuma motar ta yi kyau yanzu

Ta yaya zan nuna cewa ina son tsabta kamar Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba