Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Janairu p. 8
  • Ku Rika Addu’a a Madadin ‘Yan’uwan da Ake Tsananta Musu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Rika Addu’a a Madadin ‘Yan’uwan da Ake Tsananta Musu
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Farin Ciki Idan Ana Tsananta Muku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Suna Farin Ciki Duk Da Ana Tsananta Musu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Mu Riƙa Yin Adduꞌa a Madadin Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Kuna Bincika JW.ORG/HA don Samun Shawarwari na Yau da Kullum?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Janairu p. 8

RAYUWAR KIRISTA

Ku Riƙa Addu’a a Madadin ‘Yan’uwan da Ake Tsananta Musu

Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Shaiɗan zai tsananta mana domin yana so mu daina bauta wa Jehobah. (Yoh 15:20; R. Yoh 12:17) Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwanmu Kiristoci waɗanda ake tsananta musu a ƙasarsu? Za mu iya yin addu’a a madadinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Addu’ar mai-adalci tana da iko da yawa cikin aikinta.”​—Yaƙ 5:16.

Za a shigar da wani dan’uwa da aka saka masa sarka a hannu cikin fursuna; wasu ‘yan’uwa; wani dan’uwa yana addu’a

Me za mu iya yin addu’a a kai? Za mu iya ce Jehobah ya taimaka wa ‘yan’uwanmu su kasance da gaba gaɗi. (Ish 41:​10-13) Za mu kuma iya roƙan Jehobah ya sa mahukunta su fahimci muhimmancin bisharar da muke yi, domin mu riƙa ‘zama lafiya, rai kwance.’​—1Ti 2:1, 2, Littafi Mai Tsarki.

Sa’ad da ake tsananta wa Bulus da Bitrus a ƙarni na farko, Kiristocin sun ambata sunayen kowannensu a addu’a. (A. M. 12:5; Ro 15:​30, 31) A yau, ko da ba mu san sunayen dukan waɗanda ake tsananta musu ba, shin za mu iya ambata ikilisiyar su da ƙasarsu da kuma yankinsu a addu’o’inmu?

  • Za a iya samun bayanai na kwana-kwanan nan game da Shaidun da ake tsananta musu a dandalin jw.org/ha. (Ka duba ƙarƙashin DAKIN WATSA LABARAI > LABARAN SHARI’A.)

  • Talifofin jw.org mai jigo “Shaidun Jehobah da Aka Tsare a Kurkuku Saboda Imaninsu​—Bisa ga Kasa,” tana ɗauke da jerin sunayen ‘yan’uwan da ke fursuna a kowace ƙasa. (Ka duba ƙarƙashin DAKIN WATSA LABARAI > LABARAN SHARI’A. Ka danna sunan kasa don samun karin bayani da kuma ganin sunayen mutanen da ke cikin fursuna.)

Ka rubuta kasashen da ake tsananta wa Shaidun Jehobah da za ka so ka yi addu’a a madadinsu:

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba