DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 17-23
Yin Wulaƙanci da Ikonmu Zai Sa Mu Rasa Gatanmu
Shebna ne bawa wanda ke “bisa kan gida,” wataƙila gidan Sarkin Hezekiya. Shi ne mutum na biyu mafi iko a ƙasar.
22:15, 16
Ya kamata Shebna ya kula da bukatun bayin Jehobah
Amma ya biɗar wa kansa girma
22:20-22
Jehobah ya ba Eliakim matsayin Shebna
An ba Eliakim “makullin gidan Dauda,” wanda ke wakiltar iko
Ka yi tunani: Yaya ya kamata Shebna ya yi amfani da ikonsa don taimaka wa wasu?