Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 8/1 pp. 4-7
  • Me Ya Sa Biyayya ga Masu Iko—Ke Da Muhimmanci?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Biyayya ga Masu Iko—Ke Da Muhimmanci?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Iko a Jiha
  • Iyali da Kuma Iko
  • Ikklisiyar Kirista da Kuma Iko
  • Me Ya Sa Za a Girmama Hukuma?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ku Girmama Waɗanda Suke Da Iko Bisa Kanku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Amince Da Ikon Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 8/1 pp. 4-7

Me Ya Sa Biyayya ga Masu Iko—Ke Da Muhimmanci?

WANENE ba ya farin ciki cewa ’yan sanda suna da iko su kama waɗanda suka saci kayayyakinmu ko kuma suka yi wa iyalinmu burga? Ba ma farin ciki cewa kotu suna da iko su ba da horo ga masu laifi kuma su kare jama’a?

Za mu iya tuna da wasu wurare da suke taimaka wa jama’a, kamar su kula da hanya, share mahalli, da kuma ilimi—da ake biya ta wurin haraji da gwamnati take ɗora wa jama’a. Kiristoci na gaskiya su ne farko wajen fahimtar cewa wannan biyayya ga masu iko da aka naɗa muhimmin abu ne. Amma yaya yawar biyayyar nan? Kuma a waɗanne fasalolin rayuwa ake bukatar yin biyayya ga masu iko?

Iko a Jiha

Littafi Mai-Tsarki ya gaya wa dukan mutane, masu bi da marasa bi, su yi wa masu iko da ƙasa biyayya domin ayyuka masu amfani da suke yi wa jama’a. Kirista manzo Bulus ya rubuta wa ’yan’uwansa masu bi a Roma game da wannan, kuma zai yi taimako mu bincika abin da ya faɗa a Romawa 13:1-7.

Bulus ɗan ƙasar Roma ne, kuma Roma ce take mulkin duniya a lokacin. Wasiƙar Bulus da ya rubuta a kusan shekara ta 56 A.Z., ya gargaɗi Kiristoci su zama mazauna ƙasa masu hali nagari. Ya rubuta: “Bari kowane mai-rai shi yi zaman biyayya da ikon masu-mulki: gama babu wani iko sai na Allah; ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah.”

A nan Bulus ya ba da bayani cewa da ba a sami wani ikon ’yan Adam da a ce Allah bai ƙyale hakan ba. A haka yana nufin cewa manyan masu iko suna da ƙaramin matsayi cikin ƙudurin Allah. Saboda haka ya bi da cewa “wanda ya yi tsayayya da iko fa, yana tsayayya da umurnin Allah ke nan.”

Ko da yake mazauna ƙasa waɗanda suke yin nagarta sukan sami yabo daga manyan masu iko, waɗannan ikoki suna da ikon su horar da masu laifi. Waɗanda suke yin mugunta suna da dalilan jin tsoron masu iko don ikon da suke da shi na “mai-ramawa” ne, da yake na gwamnati, suna yin haka su ‘masu-hidiman Allah.’

Bulus ya kammala zancensa da cewa: “Domin wannan fa ya wajaba gareku ku yi zaman biyayya, ba domin fushi kaɗai ba, amma sabili da lamiri kuma. Gama saboda wannan kuma ku ke bada gandu; gama su masu-hidiman bautar Allah ne, kullum suna la’akari da wannan abu.”

Amfani da haraji hakki ne da yake rataye a wuyar masu iko, ba ta mai biyan haraji ba. Kirista, mazauna mai gaskiya a ƙasa, yana riƙe lamiri mai kyau. Ya san cewa ta wurin yin biyayya ga masu iko da biyan haraji, ba kawai yana bin ƙa’idar ƙasar da yake ciki ba ne amma yana bin farillan Allah daidai.

Iyali da Kuma Iko

Me kuma za a ce game da iko cikin iyali? A farkon rayuwarsa, jariri zai yi kuka ko kuma kara sosai don a kula da shi. Amma mahaifiya mai hikima za ta fahimci bukatar jaririn kuma ba za ta jira kukansa ya gaya mata bukatarsa ba. An ƙyale wasu yara su yi nasu abubuwa yayin da suke girma kuma su kafa nasu mizanai. Tun da yake ba su da fahimi, za su iya faɗawa cikin yin laifi ko wasu lalata, suna damun iyali da kuma yankin da suke, kamar yadda wasu mahukunta suka sani sosai.

“Iyaye suna makara wajen horon yaransu,” in ji Rosalind Miles, mawallafiyar littafin nan Children We Deserve. “Ya kamata a soma da zarar yaro ya faɗo duniya.” Idan tun farko iyayen suna magana da murya mai laushi na alheri na iko, kuma suna yin wannan daidai da halayensu, ba zai daɗe ba yaransu za su yi biyayya da iko da kuma horo da zai biyo baya.

Littafi Mai-Tsarki yana ɗauke da koyarwa mai yawa game da iko cikin iyali. A cikin littafin Misalai, mutum mai hikima Sulemanu ya jawo hankali ga haɗin kan iyaye masu tsoron Allah a gaban yaransu, yana cewa: “Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yarda ita.” (Misalai 1:8) Yayin da iyaye sun kafa haɗin kan nan, yaran za su san abin da ake bukata a garesu. Za su so su yi wa iyayensu wayo don su sami abin da suke so, amma haɗin kan iyaye a zancen iko tsari ne ga yara.

Littafi Mai-Tsarki ya bayyana cewa maigida ne ke da hakkin lafiyar ruhaniyar ba na yaransa kawai ba amma kuma har da ta matarsa. An kira wannan ikon shugabanci. Yaya za a yi amfani da ikon shugabancin nan? Bulus ya nuna cewa kamar yadda Kristi ne Shugaban ikklisiya haka ma mutum ne shugaban matarsa. Sai kuma Bulus ya daɗa: “Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikklisiya, ya bada kansa dominta.” (Afisawa 5:25) Idan mutum ya bi misalin Yesu kuma ya yi ja-goranci da kyau, zai sami ‘ladabi’ daga matarsa. (Afisawa 5:33) Yara da suke cikin iyalin nan za su ga darajar ikon da Allah ya bayar kuma su sami ƙarfafa na yin na’am da shi.—Afisawa 6:1-3.

Ta yaya iyaye gwauraye, har da waɗanda mazansu ko matansu suka rasu za su iya bin wannan zancen? Ko baba ko mama, za su iya biɗan ikon Jehovah Allah da na Yesu Kristi kai tsaye. Maganar Yesu kullum da iko yake yin ta—na Ubansa da na hurarun Nassosi.—Matta 4:1-10; 7:29; Yohanna 5:19, 30; 8:28.

Littafi Mai-Tsarki ya tanadar da ƙa’idodi masu yawa da ke da alaƙa da matsaloli da yara suke fuskanta. Ta wurin bincika waɗannan ƙa’idodi da kuma bin su, mahaifi zai iya tanadar da gargaɗi mai kyau na taimakawa ga yara. (Farawa 6:22; Misalai 13:20; Matta 6:33; 1 Korinthiyawa 15:33; Filibbiyawa 4:8, 9) Iyaye suna iya amfani da littattafai da aka shirya bisa Littafi Mai-Tsarki musamman don ya taimake su su yi renon yaransu su zo ga fahimtar fa’idodin yin biyayya ga iko na Nassosi.a

Ikklisiyar Kirista da Kuma Iko

“Wannan Ɗana ne ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai; ku ji shi.” (Matta 17:5) Waɗannan kalmomi da Jehovah Allah kansa ya furta ya tabbatar da cewa Yesu wanda yake magana da ikon Allah ne. An rubuta abin da ya faɗa a cikin labaran Lingila huɗu da za mu iya dubawa da sauƙi.

Ba da daɗewa ba kafin ya tafi sama, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayar gareni.” (Matta 28:18) Shi wanda shi ne shugaban ikklisiyarsa, ba kawai Yesu yana zuba ido a kan shafaffu mabiyansa a duniya ba, amma tun lokacin da aka zubo ruhu mai-tsarki a Fentakos na 33 A.Z., ya kuma yi amfani da su su zama hanyar yaɗa gaskiya, su zama “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45-47; Ayukan Manzanni 2:1-36) Menene ya yi ya cim ma dukan wannan don ya ƙarfafa ikklisiyar Kirista? “Sa’anda ya hau bisa . . . , Ya bada kyauta ga mutane.” (Afisawa 4:8) Waɗannan “kyauta ga mutane” dattiɓai Kiristoci ne da aka naɗa su ta wurin ruhu mai-tsarki kuma aka ba su iko su kula da damuwar ruhaniya na ’yan’uwa masu bi.—Ayukan Manzanni 20:28.

Saboda dalilin nan Bulus ya yi gargaɗi: “Ku tuna da waɗanda su ke shugabannanku, waɗanda suka faɗa maku maganar Allah; kuma ku yi koyi da bangaskiyarsu, kuna tuna da matuƙar tasarrufinsu.” Tun da yake waɗannan maza masu aminci suna bin sawun Yesu a tsanake, lallai hikima ce mu yi koyi da bangaskiyarsu. Sai kuma Bulus ya daɗa: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu: [“ku ci gaba da fahimtar suna da iko a kanku,” The Amplified Bible] gama suna yin tsaro sabili da rayukanku, kamar waɗanda za su amsa tambaya; su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan mara-amfani ne gareku.”—Ibraniyawa 13:7, 17.

Menene ya kan faru idan aka yi banza da umurnin nan? Wasu cikin ikklisiyar Kirista na ƙarni na farko sun yi hakan kuma sun zama ’yan ridda. An ambata Himinayas da Filitas maza waɗanda suka ja mutane zuwa rashin bin bangaskiya kuma waɗanda maganganunsu na banza ‘sun lalatar da abu mai-tsarki.’ Ɗaya cikin gardamarsu ita ce wai an riga an yi tashin matattu, watau na ruhaniya ko ta alama ke nan, saboda haka babu wani tashin matattu a nan gaba cikin Mulkin Allah kuma.—2 Timothawus 2:16-18.

Masu iko da aka naɗa suka taimaka. Dattiɓai Kirista sun iya bayyana irin musun, domin yadda su wakilan Yesu Kristi ne, suna yin amfani da ikon Nassi. (2 Timothawus 3:16, 17) Haka ma yake cikin ikklisiyar Kirista a yau, wadda aka kwatanta “jigon gaskiya da ƙarfinta.” (1 Timothawus 3:15) Kada koyarwa na ƙarya ya ɓata “sahihiyan kalmomi,” da aka adana mana wanda ya zama amana mai kyau cikin shafofin Littafi Mai-Tsarki.—2 Timothawus 1:13, 14.

Yayin da biyayya ga masu iko take ɓacewa a duniya, mu Kiristoci mun gane sarai cewa iko cikin ƙasa, cikin iyali, da kuma cikin ikklisiyar Kirista an kafa su ne domin amfaninmu. Yin biyayya ga masu iko yana da muhimmanci domin lafiyarmu ta jiki, jiye jiye, da kuma ta ruhaniya. Ta wurin yarda da kuma yin biyayya ga irin ikon nan da Allah ya bayar, za mu samu kariya daga wurin masu iko mafi girma—Jehovah Allah da kuma Yesu Kristi—domin madawwamin lafiyarmu.—Zabura 119:165; Ibraniyawa 12:9.

[Hasiya]

a Duba littattafan nan Questions Young People Ask—Answers That Work da Asirin Farinciki na Iyali, waɗanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.

[Bayanin da ke shafi na 5]

Littafi Mai-Tsarki yana ɗauke da koyarwa mai yawa game da iko cikin iyali

[Hoto a shafi na 6]

Iyaye gwauraye, waɗanda mazansu ko matansu suka rasu za su iya biɗan ikon Jehovah Allah da na Yesu Kristi kai tsaye

[Hotuna a shafi na 7]

Kiristoci sun gane sarai cewa iko cikin ƙasa, cikin iyali, da kuma cikin ikklisiyar Kirista an kafa su ne domin amfaninsu

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 4]

Photo by Josh Mathes, Collection of the Supreme Court of the United States

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba