DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 102-105
Jehobah Yakan Tuna Cewa Mu Turɓaya Ne
Dauda ya yi amfani da kwatanci don ya nuna yadda jin ƙan Jehobah yake.
103:11
Ba za mu iya kwatanta iyakar ƙaunar da Jehobah yake nuna mana ba, kamar yadda ba za mu iya fahimtar nisan da ke tsakanin duniya da sama ba
103:12
Jehobah yana nisanta mu daga zunubanmu, kamar yadda gabas take nesa da yamma
103:13
Jehobah yana tausaya wa waɗanda suke baƙin ciki don zunubansu, kamar yadda uba yake tausaya wa ɗansa da ke cikin matsala