DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 LABARBARU 33-36
Jehobah Yana Son Tuban Gaske
Hoto
MANASSA
Jehobah ya ƙyale Assuriyawa su kai shi bauta a Babila
SARAUTARSA KAFIN A KAMA SHI
Ya gina bagadai ga allolin ƙarya
Ya yi hadaya da ‘ya’yansa
Ya kashe mutane
Ya ƙarfafa yin sihiri a ƙasar gabaki ɗaya
SARAUTARSA BAYAN AN SAKO SHI
Ya nuna sauƙin kai sosai
Ya yi addu’a ga Jehobah kuma ya yi hadaya
Ya halaka bagaden allolin ƙarya
Ya ce al’ummar ta bauta wa Jehobah
JOSIAH
SARAUTARSA GABAKI ƊAYA
Ya biɗi Jehobah
Ya tsarkake Yahuda da Urushalima
Ya gyara gidan Jehobah kuma ya samo littafin Shari’a