Ku Bi Gurbin Annabawa—Nahum
1. Mene ne muka koya daga littafin Nahum?
1 Kangon birnin Nineveh na dā tabbaci ne na cikar annabcin da Nahum ya yi cewa Jehobah yana ɗaukan fansa a kan magabtansa kuma ko mafi ƙarfi a cikinsu ma ba zai iya ja da Jehobah ba. (Nah. 1:2, 6) Akwai darussa da yawa da za mu iya koya daga annabcin Nahum da za su taimaka mana a wa’azi.
2. Ta yaya za mu sa saƙonmu ya zama da ban ƙarfafa?
2 Ku Ƙarfafa Mutane Kuma Ku Sa Su Kasance da Bege: Idan ba mu bincika littafin Nahum sosai ba, muna iya gani kamar yana ɗauke da saƙon hukunci ga Nineveh babban birnin Assuriya ne kawai. (Nah. 1:1; 3:7) Amma, mutanen Jehobah sun karɓi wannan saƙon hannu bibbiyu. Nahum, wanda ma’anar sunansa “Ƙarfafa” ne, ya gaya wa ’yan’uwansa Yahudawa cewa ba da daɗewa ba za a hallaka magabtansu. Nahum ya tabbatar musu cewa Jehobah “kagara ne cikin ranar wahala.” (Nah. 1:7) Yayin da muke yin wa’azin bishara, muna gaya wa mutane su nemi mafaka a wurin Jehobah.—Nah. 1:15.
3. Ta yaya za mu bi gurbin Nahum a yin amfani da misali da kuma kwatanci?
3 Ku Ba Da Misali da Kuma Kwatanci: Jehobah ya sa Nahum ya kwatanta hallakar Nineveh da yadda Assuriyawa suka hallaka birnin Thebes (Noamon) na ƙasar Masar. (Nah. 3:8-10) Yayin da muke gaya wa mutane yadda za a kawo ƙarshen wannan zamanin, zai dace mu nuna musu wasu annabcin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa Jehobah yana cika dukan alkawuransa. Alal misali, sa’ad da Babila da Midiya suka zo yaƙar Nineveh a shekara ta 632 kafin zamaninmu, an yi ruwa mai ƙarfi sosai da ya jawo ambaliya a Kogin Tigris kuma ya rushe wani ɓangaren katangar birnin Nineveh. A sakamakon haka, an hallaka birnin Nineveh da sauƙi kamar yadda Jehobah ya annabta.—Nah. 1:8; 2:6.
4. Yayin da muke wa’azi, ta yaya za mu yi bayani dalla-dalla yadda za a fahimce mu?
4 Ku Yi Bayani Dalla-dalla Yadda Za A Fahimce Ku: Nahum ya yi rubutunsa dalla-dalla kuma a hanyar da mutane za su ji daɗin karantawa. Bayanansa sun fita sarai. (Nah. 1:14; 3:1) Hakazalika, zai dace mu riƙa amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta. (1 Kor. 14:9) A ziyararku ta farko, ku bayyana dalilin zuwanku dalla-dalla. Yayin da kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, ku taimaka musu su ba da gaskiya ga Jehobah da kuma Kalmarsa kuma su ga amfanin abin da suke koya.—Rom. 10:14.
5. Wane kalami mai ban ƙarfafa ne annabcin Nahum ya ƙunsa?
5 Littafin Nahum gabaki ɗaya ya ba da tabbaci cewa Nahum ya gaskata cewa alkawuran Jehobah za su cika. Yayin da ƙarshen zamanin Shaiɗan yake kusatowa, bari mu sami ƙarfafa daga abin da Jehobah ya faɗa, cewa: “Wahala ba za ta taso so biyu ba.”—Nah. 1:9.