Tsarin Ayyuka na Makon 22 ga Satumba
MAKON 22 GA SATUMBA
Waƙa ta 9 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 13 sakin layi na 11-18 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Littafin Lissafi 30-32 (minti 10)
Na 1: Littafin Lissafi 32:16-30 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Waɗanda Za Su Sami Rai Madawwami a Duniya Ba Su da Iyaka—td 35C (minti 5)
Na 3: Mene Ne Zai Faru Idan Muka Mutu?—lr babi na 34 (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 93
Minti 15: Rayuwa Mai Daɗi na Masu Hidima a Inda Ake Bukatar Masu Shela Sosai. (Mis 10:22) Tattaunawa a kan labarin da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2014, shafuffuka na 3-6. Ka ba masu sauraro dama su faɗi darussan da suka koya.
Minti 15: “Ku Yi Amfani da jw.org Yayin da Kuke Wa’azi.” Tattaunawa. Ka sa a yi gwaji da gabatarwar da ke sakin layi na 2, sa’an nan ka yi wa masu sauraro tambayoyin nan: Me ya sa yake da kyau mu sauƙo da bidiyon a wayarmu ko kuma kwamfutar hannu? Me ya sa zai fi dacewa mu saka wa maigidan bidiyon ba tare da dogon bayani ko kuma neman izini ba? Wane labari ne za ku iya bayarwa a kan yadda kuka yi amfani da wannan bidiyon a wa’azi? A ƙarshe, ka ƙarfafa masu shela su san sassan dandalin jw.org sosai kuma su riƙa amfani da shi yayin da muke yin wa’azi.
Waƙa ta 84 da Addu’a