Gabatarwa
Don Soma Nazari da Mutane a Asabar ta Farko a Watan Satumba
“Mun zo ne don mu tattauna wani abu da yawancin mutane suke yi. Kusan kowa yana yin addu’a, ko da wane addini ne mutumin yake bi. Ka san dalilin da ya sa ya kamata mu yi addu’a ga Allah?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa abin da ke bayan Hasumiyar Tsaro ta Satumba-Oktoba, sai ku tattauna sakin layi na farko a ƙarƙashin tambaya ta farko kuma ku karanta aƙalla nassi ɗaya a cikin waɗanda aka rubuta a wurin. Ka ba da mujallun kuma ka shirya ranar da za ka dawo don ku tattauna sakin layin da ke gaba.
Hasumiyar Tsaro Satumba–Oktoba
Ka ambata wani labarin da ke damun mutane a yankin. Sa’an nan ka ce: “Ka taɓa tunani a kan dalilin da ya sa mutane suke yin irin wannan muguntar? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya gaya mana wani abu da zai sa mu kasance da bege. [Karanta 2 Bitrus 3:13.] Wannan mujallar ta bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da sanadin mugunta da kuma yadda Allah zai kawar da mugunta nan ba da daɗewa ba.”
Awake! Satumba
“Muna tattauna wani batun da ke damun mutane da yawa. Wasu da shugabanninsu suke tara musu gajiya da yawan aiki sukan rasa mafita. Masana sun ce yin aiki kamar jaki yakan kashe jiki kuma ya jawo baƙin ciki. Me kake ganin zai taimaki mutum ya yi rayuwa daidai ƙarfinsa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga wata aya mai kyau da zan so mu karanta. [Karanta Mai-Wa’azi 4:6.] Wannan mujallar ta tattauna hanyoyi guda huɗu da za mu iya daidaita ayyukanmu don mu warware matsalar gajiyar aiki.”