Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yin Shelar Mulkin da Gaba Gaɗi
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: Yana da muhimmanci mu yi shelar Mulkin Allah da gaba gaɗi idan muna so mu bi umurnin da ke 2 Timotawus 1:7, 8. Ta yaya za mu sami gaba gaɗin yin shelar Mulkin?
Ku Bi Shawarar Nan Wannan Watan:
Ku zaɓi wani da za ku so ku yi masa wa’azi. Ku roƙi Jehobah ya ba ku gaba gaɗi kuma ya sa ku sami zarafin yin wa’azi.