Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Disamba
“Za mu so mu ɗan tattauna da kai game da begen tashin matattu da Allah ya yi mana alkawarinsa. Ka taɓa tunani a kan yadda Allah zai ta da matattu?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa bangon bayan Hasumiyar Tsaro na Nuwamba–Disamba, kuma ku tattauna batun da ke ƙarƙashin tambaya ta biyu da kuma aƙalla ɗaya daga cikin nassosin da aka rubuta a wurin. Ka ba da mujallun kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na gaba.
Hasumiyar Tsaro Nuwamba–Disamba
“Mun zo wurinka don mu ɗan tattauna wani abu mai muhimmanci da kai daga Littafi Mai Tsarki. Batun game da wani shiri ne da Allah ya yi don dukan waɗanda suke son zaman lafiya da kuma adalci su sami albarka. [Karanta Farawa 22:18.] Wane ne zuriyar da aka ambata a nan kuma ta yaya dukan al’ummar duniya za ta sami albarka ta wurinta? Za ka sami amsoshi masu gamsarwa a shafuffuka na 5 da 6 a wannan mujallar.”
Awake! Disamba
“Yawancinmu mukan bi ra’ayoyin da muka ji ko kuma karanta a kafofin yaɗa labarai. Shin kana ganin dukan labarai da muke ji da kuma karantawa daidai ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu yi garajen gaskata abin da muka ji. [Karanta Ayuba 12:11.] Wannan mujallar ta ambata wasu abubuwa da za su taimaka mana mu san ko abin da muka ji da kuma karanta daidai ne.”