Tsarin Ayyuka na Makon 9 ga Disamba
MAKON 9 GA DISAMBA
Waƙa ta 84 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
jl Darasi na 17-19 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Yohanna 1-5; 2 Yohanna 1-13; 3 Yohanna 1-14–Yahuda 1-25 (minti 10)
Na 1: 1 Yohanna 5:1-21 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: A Wace Hanya Ce Ya Kamata Mu Tuna da Yesu Kristi?—Luk 1:32, 33; Yoh. 17:3 (minti 5)
Na 3: Ba Ya Yiwuwa A Yi Magana da Matattu—td 34C (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 5
Minti 15: Makarantar Hidima ta Allah a Shekara ta 2014. Mai kula da makaranta ne zai ba da wannan jawabin. Ya bi umurnin da ke cikin takardar umurni don Tsarin Ayyuka na Makarantar Hidima ta Allah na Shekara ta 2014 yayin da yake tattauna batutuwan da ikilisiyar take bukata ta mai da wa hankali. Ka bayyana cewa idan karatun Littafi Mai Tsarki na makon ya kama surorin farko na wani littafi ne, ɗan’uwan da aka ba shi wannan jawabin ba zai yi bayaninsa bisa ga jerin talifofin nan “Maganar Jehovah Rayayyiya Ce,” da aka soma wallafawa a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu 2004 ba. Ka ƙarfafa dukan ’yan’uwa su shirya jawabansu da kyau, su yi kalami daga zuci a lokacin da ake gudanar da karatun Littafi Mai Tsarki na mako, kuma su yi ƙoƙari su bi shawarwarin da ake bayarwa daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education.
Minti 15: “Za A Rarraba Bisharar Mulki ta 38 a Watan Janairu!” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka sa a rarraba wa dukan waɗanda suka halarci taron kofi guda na Bisharar Mulki ta 38. Ka gayyaci mai kula da hidima ya faɗi shirin da ikilisiyar ta yi don a rarraba Bisharar Mulki a dukan yankinku. Ka sa a yi amfani da gabatarwar da ke shafi na 8 wajen nuna yadda za a iya ba da Bisharar Mulki.
Waƙa ta 60 da Addu’a