Kada Ku Hana Kanku Samun Ɗalibai —Yadda Za Ku Shawo Kan Jin Cewa Ba Ku Cancanta Ba
1. Me ya sa wasu suna jinkirin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane?
1 Kana jinkirin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane ne domin kana ganin ba za ka iya gudanar da nazarin da kyau ba? Amintattun bayin Allah na dā kamar su Musa da Irmiya, sun taɓa jin cewa ba za su iya yin aikin da Allah ya ba su ba. (Fit. 3:10, 11; 4:10; Irm. 1:4-6) Wannan ya nuna cewa ba kai kaɗai ba ne ka taɓa samun kanka a irin wannan yanayin. Me zai taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi?
2. Me ya sa bai kamata mu mai da hankali kawai ga yin wa’azi gida-gida sa’an nan mu bar wasu da aikin gudanar da nazari da mutane ba?
2 Mu tuna cewa Jehobah ba zai taɓa sa mu yin abin da ya fi ƙarfinmu ba. (Zab. 103:14) Saboda haka, “almajirtar” da mutane da kuma “koya” musu Kalmar Allah aiki ne da za mu iya yi. (Mat. 28:19, 20) Jehobah bai ba da wannan gatan ga waɗanda suke da ƙwarewa da kuma ilimi kawai ba. (1 Kor. 1:26, 27) Don haka, bai kamata mu mai da hankali kawai ga yin wa’azi gida-gida sa’an nan mu bar wasu da aikin gudanar da nazari da mutane ba.
3. Ta yaya Jehobah yake horar da mu don mu ƙware wajen gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki?
3 Jehobah Ne Yake Sa Mu Cancanta: Jehobah ne yake horar da mu don mu almajirtar da mutane da kyau. (2 Kor. 3:5) Jehobah yana amfani da ƙungiyarsa wajen koya mana gaskiyar da ke Kalmarsa wadda manyan masu ilimi na duniya ba su sani ba. (1 Kor. 2:7, 8) Jehobah ya sa an rubuta hanyoyin koyarwa na Babban Malami, wato, Yesu, a cikin Littafi Mai Tsarki don mu yi koyi da shi, kuma Allah ya ci gaba da horar da mu ta ƙungiyarsa. Ƙari ga hakan, Jehobah ya ba mu littattafai da muke bukata don mu koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Ya tanadar mana da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don mu iya koyar da gaskiya bisa tsari kuma cikin sauƙi. Saboda haka, gudanar da nazarin bai da wuya kamar yadda muke tsammani.
4. Me ya sa za mu iya kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah zai taimaka mana?
4 Da taimakon Jehobah, Musa da Irmiya sun cika aikin da Jehobah ya ba su. (Fit. 4:11, 12; Irm. 1:7, 8) Mu ma za mu iya roƙon Jehobah ya taimaka mana. Balle ma, sa’ad da muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki muna koya wa mutane gaskiya game da Jehobah ne kuma hakan yana faranta masa rai. (1 Yoh. 3:22) Saboda haka, ku ƙudura cewa za ku riƙa saka hannu a wannan aiki mafi ƙayatarwa da kuma albarka, wato, aikin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki.