Yin Bimbini da Addu’a Suna da Muhimmanci ga Masu Hidima da Ƙwazo
1. Mene ne ya taimaki Yesu don kada ya bijire daga ainihin aikin da ya kawo shi duniya?
1 Yesu ya yi amfani da yamman gabaki ɗaya don ya warkar da mutane da kuma fitar da aljannu daga jikinsu. Washegari sa’ad da almajiransa suka gan shi, sai suka ce: “Dukan mutane suna nemanka,” suna son ya ci gaba da ayyukansa na al’ajabi. Amma dai Yesu bai bar komi ya raba hankalinsa daga ainihin aikinsa na yin wa’azin bishara ba. Ya ce musu, “Bari mu tafi wani wuri zuwa garuruwa na kusa, domin in yi wa’azi a can kuma; gama dalilin zuwa na ke nan.” Mene ne ya sa hankalin Yesu bai rabu biyu ba? Ya tashi da asuba don ya yi addu’a da kuma bimbini. (Mar. 1:32-39) Ta yaya yin bimbini cikin addu’a zai iya taimaka mana mu zama masu yin wa’azi da ƙwazo?
2. Mene ne za mu iya yin bimbini a kai da zai taimake mu mu kasance da ƙwazo a hidima?
2 Yin Bimbini a Kan Me? Yesu ya lura cewa mutane suna “wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Hakazalika, za mu iya yin bimbini a kan yadda mutane suke son bishara. Za mu iya yin tunani a kan gaggawar lokacin da muke ciki. (1 Kor. 7:29) Za mu iya yin bimbini a kan ayyukan Jehobah, halayensa, da kuma gatar da muke da ita na zaman Shaidun Jehobah, da kuma abubuwa na ruhaniya masu tamani da muka koya daga Kalmar Allah da har ila mutane da suke yankinmu ba su sani ba.—Zab. 77:11-13; Isha. 43:10-12; Mat. 13:52.
3. A wane lokaci ne za mu iya yin bimbini?
3 Yin Bimbini a Wane Lokaci? Wasu suna tashiwa da duku-duku kamar yadda Yesu ya yi. Wasu kuma suna ganin amfanin yin bimbini da yamma kafin su yi barci. (Far. 24:63) Ko da muna da ayyuka da yawa, za mu iya mu nemi lokaci don yin bimbini. Wasu suna yin hakan sa’ad da suka shiga motar haya. Wasu kuma suna yin amfani da wasu cikin lokacin cin abincin ranarsu don yin bimbini cikin natsuwa. Wasu sun ga cewa yin bimbini na ’yan mintoci kafin su yi wa’azi, yana taimaka musu su yi wa’azi da ƙwazo da kuma gaba gaɗi.
4. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi bimbini?
4 Yin bimbini cikin addu’a zai zurfafa muradinmu na bauta wa Jehobah, zai kuma taimaka mana mu ɗauki bautarmu da muhimmanci, kuma zai ƙarfafa ƙudurinmu na ci gaba da yin wa’azi. Yesu, Mai Hidima Mai Girma na Allah, ya amfana daga yin bimbini, mu ma za mu yi hakan.