Kiristoci Masu Hidima Suna Bukatar Yin Addu’a
1. Menene muke bukata don mu cim ma hidimarmu?
1 Ba za mu iya cim ma hidima da kanmu ba. Jehobah ne ke ba mu ƙarfin yin aikin. (Filib. 4:13) Yana amfani da mala’ikunsa wajen taimaka mana mu samu masu kama da tumaki. (R. Yoh. 14:6, 7) Jehobah ne yake sa iri na gaskiya da muka shuka kuma muka ba ruwa ya girma. (1 Kor. 3:6, 9) Yana da muhimmanci Kiristoci masu hidima su dogara ga Ubanmu na samaniya cikin addu’a!
2. Za mu iya yin addu’a game da waɗanne abubuwa?
2 Don Kanmu: Ya kamata mu riƙa yin addu’a a duk lokacin da muke wa’azi. (Afis. 6:18) Menene wasu abubuwan da ya kamata mu roƙa? Muna iya yin addu’ar kasancewa da ra’ayi mai kyau game da yankinmu da kuma gaba gaɗi. (A. M. 4:29) Za mu iya roƙi Jehobah ya ja-gorance mu ga masu zukatan kirki da za mu iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Idan maigidan ya yi mana tambaya, za mu iya yin gajeriyar addu’a a zuciyarmu mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu ba da amsar da ta dace. (Neh. 2:4) Za mu kuma iya yin addu’ar samun hikima don saka hidima farko a rayuwarmu. (Yaƙ. 1:5) Ƙari ga haka, Jehobah yana yin farin ciki sa’ad da muka furta godiya a addu’armu domin gatar da ya ba mu na zama masu yi masa hidima.—Kol. 3:15.
3. Ta yaya yi wa wasu addu’a yake faɗaɗa aikin wa’azi?
3 Don Wasu: Ya kamata kuma mu “yi ma juna addu’a,” har da ambata sunayen ’yan’uwanmu masu hidima idan da bukata. (Yaƙ. 5:16; A. M. 12:5) Shin rashin lafiya ya rage abin da za ka iya yi a aikin wa’azi ne? Sai ka yi wa ’yan’uwanka masu hidima da suke da lafiya addu’a. Kada ka taɓa raina yadda addu’arka za ta iya shafarsu! Ya dace kuma mu yi wa hukumomi addu’a don su kasance da ra’ayi mai kyau game da wa’azi, saboda ’yan’uwanmu su yi ‘rayuwa mai-natsuwa da hankali kwance.’—1 Tim. 2:1, 2.
4. Me ya sa ya dace mu lizima cikin addu’a?
4 Yin shelar bishara a dukan duniya aiki ne mai girma. Idan mun “lizima cikin addu’a,” za mu cim ma aikin da taimakon Jehobah.—Rom. 12:12.