Tsarin Ayyuka na Makon 24 ga Mayu
MAKON 24 GA MAYU
Waƙa 37
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh rataye shafi na 197-199
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sama’ila 13 zuwa 15
Na 1: 2 Sama’ila 13:23-33
Na 2: Iblis Shi Ne Masaraucin Duniya Marar Ganuwa (td 22B)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Ba Za Mu Cika Moriyar Duniya Ba (1 Kor. 7:31)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 128
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Ka Yi Shirin Gabatar da Mujallu a Watan Yuni. Tattaunawa da masu sauraro. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don yin bitar abin da ke cikin mujallun. Sai ka zaɓi talifofi biyu ko uku, kuma ka gayyaci masu sauraro su faɗi tambayoyi da nassosi da za a iya amfani da su wajen gabatarwa. Ka gwada yadda za a iya gabatar da kowanne talifi.
Minti 20: “Za Ka Iya Zama Majagaba Mai Kyau!” Tambaya ana ba da amsa.
Waƙa ta 85