Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 5/1 pp. 4-14
  • Alherin da Allah Ya Yi Maka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Alherin da Allah Ya Yi Maka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “SABODA ƘAUNAR DA ALLAH YA YI WA DUNIYA”
  • “YA BA DA MAKAƊAICIN ƊANSA”
  • “DUK WANDA YA GASKATA DA SHI”
  • “KADA YA HALAKA, SAI DAI YA SAMI RAI MADAWWAMI”
  • ALLAH YA YI MANA ABUBUWA DA YAWA
  • Me Ya Sa Yesu Ya Sha Wahala Kuma Ya Mutu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Wane Ne Yesu Kristi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ta Yaya Mutuwar Yesu Za Ta Cece Mu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Wace Kyauta Ce Ta Fi Tamani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 5/1 pp. 4-14

ABIN DA KE SHAFIN FARKO

Alherin da Allah Ya Yi Maka

“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.”—Yohanna 3:16, Littafi Mai Tsarki.

Wannan nassin yana ɗaya daga cikin nassosin da aka fi sani da kuma ƙaulinsu a cikin Littafi Mai Tsarki. Mutane da yawa sun yarda cewa wannan ayar ce ta bayyana dangantaka da ke tsakanin Allah da ’yan Adam da kuma hanyar samun ceto fiye da duk sauran ayoyin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, a wasu ƙasashe, mutane suna yawan rubuta “Yohanna 3:16” ko kuma su yi ƙaulin ayar kuma su manna ta a jikin motoci da bango da inda ake taro, da dai sauransu.

Babu shakka, waɗanda suke ƙaulin nassin nan sun tabbata cewa ƙaunar Allah ce za ta sa su sami ceto. Kai kuma fa? Mene ne ra’ayinka game da ƙaunar Allah a gare mu? Kuma mene ne kake ganin Allah ya yi da ya nuna cewa yana ƙaunar ka?

“SABODA ƘAUNAR DA ALLAH YA YI WA DUNIYA”

Mutane da yawa sun amince cewa Allah ne ya halicci sama da ƙasa da ’yan Adam da kuma sauran halittu. Yadda halittu suke da fasali da kuma wuyar fahimta tabbaci ne cewa akwai Mahalicci mai basira sosai. Yawancin mutane suna gode wa Allah kowace rana domin suna da rai. Sun kuma fahimci cewa Allah ne yake tanadar da dukan abubuwan da suke bukata a rayuwa, wato abubuwa kamar su ruwa da iska da abinci da dai sauransu.

Ya kamata mu riƙa gode wa Allah don waɗannan tanadin, domin shi ne Mahaliccinmu kuma shi yake rayar da mu. (Zabura 104:10-28; 145:15, 16; Ayyukan Manzanni 4:24) Idan muka yi tunani a kan dukan abubuwan da Allah yake tanadar mana don mu rayu, za mu san cewa yana ƙaunar mu. Manzo Bulus ya ce: ‘[Allah] da kansa yana ba kowa rai, da numfashi, da abu duka; gama ta wurinsa mu ke rayuwa, mu ke motsi, mu ke zamanmu.’—Ayyukan Manzanni 17:25, 28.

Amma, ban da biyan bukatunmu na zahiri, akwai wasu hanyoyi kuma da Allah yake nuna cewa yana ƙaunar mu. Ya ɗaukaka mu ta wajen ba mu damar ƙulla dangantaka mai kyau da shi da kuma taimaka mana mu yi hakan. (Matta 5:3) Ta hakan, bayin Allah masu aminci sun kasance da begen zama ‘’ya’yansa.’—Romawa 8:19-21.

Kamar yadda Yohanna 3:16 ta ce, Allah ya nuna mana cewa yana ƙaunarmu ta wajen aiko da Ɗansa Yesu, zuwa duniya don ya koya mana game da Allahnsa da kuma Ubansa kuma ya ba da ransa domin mu. Mutane da yawa za su iya cewa ba su fahimci ainihin dalilin da ya sa ya kasance da muhimmanci Yesu ya mutu a madadin ’yan Adam da kuma yadda mutuwarsa ta nuna cewa Allah yana ƙaunarmu ba. Bari mu ga yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalili da kuma muhimmancin mutuwar Yesu.

“YA BA DA MAKAƊAICIN ƊANSA”

Babu ɗan Adam da ya fi ƙarfin ciwo da tsufa da kuma mutuwa. Amma hakan ba asalin nufin Jehobah ba ne. Ya ba Adamu da Hawwa’u damar zama har abada a cikin aljanna a duniya. Amma hakan ya dangana ga wani abu guda, wato, suna bukata su yi masa biyayya. Allah ya ce idan suka ƙi yin hakan, za su mutu. (Farawa 2:17) Adamu ya ƙi yi wa Allah biyayya, kuma ta hakan ya jawo wa kansa da kuma ’ya’yansa mutuwa. Manzo Bulus ya bayyana cewa: “Kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.”—Romawa 5:12.

Amma, Allah “yana son shari’a.” (Zabura 37:28) Ko da yake Allah bai gafarta wa Adamu don zunubin da ya yi da gangan ba, Allah ya ba ’ya’yansa begen zama a duniya har abada, a lokacin da ba za a sha wahala ba balle ma a mutu. Allah ya bi ƙa’idodin adalci daidai wa daida ta wajen ba da “rai don rai,” domin ya buɗe wa ’yan Adam masu biyayya hanyar zama har abada a duniya. (Fitowa 21:23) Yanzu tambayar ita ce, Ta yaya mutane za su iya zama kamilai? Ga kuma amsarta: Wajibi ne mutum kamili kamar Adamu ya sadaukar da ransa.

Hakika, babu wani ɗan Adam ajizi da zai iya yin hakan, sai Yesu. (Zabura 49:6-9) Yesu kamili ne kamar Adamu, domin bai gāji zunubi ba sa’ad da aka haife shi. Ta wajen ba da ransa, Yesu ya ceci ’yan Adam daga zunubi, kuma hakan ya ba su damar kasancewa da begen zama kamiltattu kamar yadda Adamu da Hawwa’u suke a dā. (Romawa 3:23, 24; 6:23) Shin akwai abin da muke bukata mu yi don mu amfana daga irin wannan ƙaunar da Allah ya nuna mana?

“DUK WANDA YA GASKATA DA SHI”

Bari mu sake duba Yohanna 3:16 don mu yi la’akari da kalmomin nan, “duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.” Waɗannan kalmomin sun nuna cewa akwai abin da muke bukatar yi kafin mu rayu har abada. Idan muna so mu “sami rai madawwami,” muna bukata mu gaskata da Yesu kuma mu yi masa biyayya.

Kana iya yin tunani cewa: ‘Me ya kawo zancen biyayya, tun da yake Yesu ya ce “duk wanda ya gaskata da shi” zai sami rai na har abada?’ Hakika, yana da muhimmanci mu ba da gaskiya. Amma, ba yin imani cewa Yesu ya wanzu ne kawai abin da ake bukata ba. Wani ƙamus da ya yi bayyani a kan kalmomin Littafi Mai Tsarki ya ce kalmar Helenanci da Yohanna ya yi amfani da ita tana nufin “dogara ga wani abu, ba amincewa da abin kawai, babu gaira babu dalili ba.” Ko da yake yana da kyau mutum ya san cewa Yesu ne mai ceto, wajibi ne ya duƙufa wajen bin koyarwar Yesu idan yana so Allah ya yi masa alheri. Idan mutum ya ce ya gaskata da wani abu, amma ayyukansa ba su nuna hakan ba, da’awarsa banza ce. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.” (Yaƙub 2:26) Hakan yana nufin cewa mai bi yana bukata ya nuna cewa ya gaskata da Yesu ta wajen yin rayuwar da ta jitu da imaninsa.

Bulus ya bayyana wannan batun sa’ad da ya ce: “Ƙaunar Almasihu gare mu ita ke mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da ya ke wani [Yesu] ya mutu saboda dukan mutane, . . . Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda ke raye, kada su yi zaman ganin dama nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.” (2 Korintiyawa 5:14, 15, LMT) Idan muna godiya ga Yesu domin ya ba da ransa a madadinmu, za mu daina neman burin kanmu kuma mu ci gaba da binsa, da yake ya mutu a madadinmu. Ya kamata bin koyarwar Yesu ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Hakan zai shafi shawarwarinmu da zaɓinmu da kuma dukan abubuwan da muke yi a rayuwa. Wane lada ne waɗanda suka yi imani da Yesu kuma suka nuna hakan ta ayyukansu za su samu?

“KADA YA HALAKA, SAI DAI YA SAMI RAI MADAWWAMI”

A ƙarshe, littafin Yohanna 3:16 ya ambata alkawarin da Allah ya yi ga waɗanda suka ba da gaskiya ga hadayar fansa kuma suka bi dokokinsa. Nassin ya ce nufin Allah shi ne ‘kada su halaka, sai dai su sami rai madawwami.’ Amma, waɗanda za su amfana daga ƙaunar Allah suna da bege dabam-dabam.

Ga wasu a cikinsu, Yesu ya yi alkawari cewa za su zauna har abada a sama. Ya gaya wa almajiransa cewa zai je ya shirya musu wuri don su yi sarauta tare da shi. (Yohanna 14:2, 3; Filibiyawa 3:20, 21) Waɗanda aka tashe su zuwa sama “za su zama firistoci na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi shekara dubu.”—Ru’ya ta Yohanna 20:6.

Mabiyan Kristi kaɗan ne za su mori wannan gatan. Yesu ya ce: ‘Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi shi ba ku mulkin.’ (Luka 12:32) Wannan ‘ƙaramin garken’ ya ƙunshi mutane nawa ne? Littafin Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4 ya ce: “Na duba kuma, ga Ɗan ragon [Yesu Kristi wanda ya tashi daga mutuwa] yana tsaye bisa dutsen Sihiyona [na sama], tare da shi kuma mutum dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu, suna da sunansa, da sunan Ubansa, a rubuce bisa goshinsu. . . . Aka fanshi waɗannan daga cikin mutane, su zama nunan fari ga Allah da Ɗan rago.” Hakika waɗannan mutane 144,000 “ƙaramin garke” ne idan aka kwatanta jimlarsu da biliyoyin mutane da suka taɓa rayuwa. Tun da aka ce da waɗannan mutanen sarakuna, su wa za su zama talakawansu?

Yesu ya kuma yi magana game da rukuni na biyu wanda ya ƙunshi amintattun bayin Allah da za su amfana daga wannan Mulkin. A littafin Yohanna 10:16, Yesu ya ce: ‘Ina da waɗansu tumaki kuma, waɗanda ba na wannan garke ba ne: su kuma dole zan kawo, za su kuma ji muryata: su zama garke ɗaya, makiyayi ɗaya.’ Waɗannan ‘tumakin’ suna ɗokin zama har abada a duniya, kamar yadda da ma ya kamata Adamu da Hawwa’u su yi. Ta yaya muka sani cewa waɗanda suke wannan rukunin za su zauna har abada a duniya?

Sau da yawa, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa duniya za ta zama Aljanna. Idan kana so ka tabbatar da hakan, za ka iya karanta nassosin da ke ƙasa a naka Littafi Mai Tsarki ko kuma a dandalin www.jw.org: Zabura 37:9-11; 46:8, 9; 72:7, 8, 16; Ishaya 35:5, 6; 65:21-23; Matta 5:5; Yohanna 5:28, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:4. An annabta a waɗannan nassosin cewa za a kawo ƙarshen yaƙi da fari da rashin lafiya da kuma mutuwa. An kuma ambata cewa za a kai lokacin da mutane masu yin nagarta za su ji daɗin gina gida na kansu, su yi noma a gonakinsu kuma su yi renon ’ya’yansu a cikin salama.a Babu shakka za ka so ka more irin wannan rayuwar, ko ba haka ba? Muna da tabbaci cewa waɗannan alkawuran za su cika nan ba da daɗewa ba.

ALLAH YA YI MANA ABUBUWA DA YAWA

Idan ka yi tunani a kan dukan alherin da Allah ya yi maka da kuma ’yan Adam gabaki ɗaya, za ka ga cewa ya yi abubuwa da yawa. Muna da rai da basira da lafiyar jiki iya gwargwado da kuma abubuwan da muke bukata don mu rayu. Kamar yadda muka koya a littafin Yohanna 3:16, mutuwar fansa da Yesu ya yi kyauta ce daga wurin Allah da zai buɗe mana hanyar samun albarka sosai.

Babu shakka, zama a duniya har abada a cikin lumana, ba tare da jin tsoron yiwuwar rashin lafiya ko yaƙi ko yunwa ko kuma mutuwa ba, zai sa mu farin ciki sosai. Samun waɗannan albarkar ya dangana a gare ka. Tambayar da ta rage yanzu ita ce, Mene ne kake yi wa Allah?

a Don ƙarin bayani a kan waɗannan alkawuran, ka duba babi na 3 a cikin littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba