Ka Daraja Yesu, Wanda Ya Fi Dauda Da Sulemanu Girma
“Ga kuwa wanda ya fi Solomon girma a nan.”—MAT. 12:42.
1, 2. Me ya sa ’yan adam za su yi mamaki sa’ad da aka gaya wa Sama’ila ya naɗa Dauda a matsayin sarki?
BAI yi kama da sarki ba. Amma, ga annabi Sama’ila, shi yaro ne makiyayi kawai. Bugu da ƙari, garin da aka haife shi, Bai’talami, ba sanannen gari ba ne. An kwatanta garin a matsayin ‘ƙanƙanuwa a cikin dangin Yahuda.’ (Mi. 5:2) Duk da haka, annabi Sama’ila yana gab da naɗa wannan matashin da ba sananne ba ne, a matsayin sarkin Isra’ila na gaba.
2 Ba Dauda matashi ba ne ɗa na farko da mahaifinsa, Jesse, ya gabatar ga Sama’ila don naɗawa ba, kuma ba shi ne na biyu ko na uku ba. Dauda wanda shi ne ɗan auta a cikin yara maza guda takwas da Jesse ya haifa, ba ya nan sa’ad da Sama’ila ya isa gidan Jesse don ya naɗa ɗaya daga cikin yaran mutumin nan mai aminci a matsayin sarkin ƙasar na nan gaba. Amma Dauda ne wanda Jehobah ya zaɓa, kuma abin da ya fi muhimmanci ke nan.—1 Sam. 16:1-10.
3. (a) Menene ya fi muhimmanci ga Jehobah sa’ad da yake bincika mutum? (b) Menene ya faru bayan da aka naɗa Dauda sarki?
3 Jehobah ya ga abin da Sama’ila ba zai iya gani ba. Allah ya san abin da ke zuciyar Dauda, kuma hakan ya gamshe shi. Ba kyaun siffa ba ce ke da muhimmanci ga Allah, amma ainihin halayenmu ne yake dubawa. (Karanta 1 Samuila 16:7.) Saboda haka, sa’ad da Sama’ila ya fahimci cewa Jehobah bai zaɓi kowanne cikin ’ya’yan Jesse maza bakwai ba, sai ya ce a je a kawo ɗan autansu daga inda yake kiwo. Labarin ya ce: ‘Sai [Jesse] ya aika, aka zo da shi [Dauda]. Shi dai ja ne, mai-kyaun fuska, mai-daɗin gani kuwa. Ubangiji ya ce, Tashi, ka shafe shi: gama wannan shi ne. Sa’annan Samu’ila ya ɗauki ƙafon mai, ya shafe shi a tsakiyar ’yan’uwansa: ruhun Ubangiji kuma ya jiɗo ma Dawuda da iko ƙwarai daga ran nan zuwa gaba.’—1 Sam. 16:12, 13.
Dauda Ya Wakilci Kristi
4, 5. (a) Ka kwatanta wasu kamanni da ke tsakanin Dauda da Yesu. (b) Me ya sa za a kira Yesu Dauda Mafi Girma?
4 Kamar Dauda, an haifi Yesu a Bai’talami, shekaru 1,100 bayan zamanin Dauda. A gaban mutane da yawa, Yesu bai yi kama da sarki ba. Wato, shi ba irin sarkin da mutane da yawa a Isra’ila suke sa ran gani ba ne. Amma, kamar Dauda, shi ne Jehobah ya zaɓa. Kamar Dauda, Jehobah yana ƙaunarsa.a (Luk. 3:22) Hakazalika, sa’ad da aka shafa Yesu da ruhu, ‘ruhun Ubangiji kuma ya jiɗo da iko ƙwarai’ a kansa.
5 Da akwai ƙarin kamanni tsakanin su biyun. Alal misali, Ahitofel mai ba Dauda shawara, ya ci amanarsa, kuma manzon Yesu, Yahuda Iskariyoti ya ci amanarsa. (Zab. 41:9; Yoh. 13:18) Yesu da Dauda duk suna da ƙwazo sosai ga wurin bautar Jehobah. (Zab. 27:4; 69:9; Yoh. 2:17) Yesu kuma magajin Dauda ne. Kafin a haifi Yesu, wani mala’ika ya gaya wa mamarsa: “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda.” (Luk. 1:32; Mat. 1:1) Amma dai, domin dukan alkawura na Almasihu za su cika a Yesu, ya fi Dauda girma sosai. Shi ne Dauda Mafi Girma, Sarki Almasihu wanda ake jira da daɗewa.—Yoh. 7:42.
Ka Bi Sarki Makiyayi
6. A waɗanne hanyoyi ne Dauda ya zama makiyayi mai kyau?
6 Yesu makiyayi ne. Waɗanne abubuwa ne ke nuna cewa mutum makiyayi ne mai kyau? Shi mutumi ne da yake kula, ciyar da tumakinsa da kuma kāre su da kyau. (Zab. 23:2-4) Sa’ad da yake matashi, Dauda makiyayi ne, kuma ya kula da tumakin babansa sosai. Ya kasance da gaba gaɗi sa’ad da aka kai wa garkensa farmaki kuma ya sadaukar da ransa don ya kāre tunkiyarsa daga zaki da wata muguwar naman daji mai suna bear.—1 Sam. 17:34, 35.
7. (a) Menene ya shirya Dauda don ayyukansa a matsayin sarki? (b) Ta yaya Yesu ya zama Makiyayi Mai Kyau?
7 Shekarun da Dauda ya yi a jeji da kuma kan tuddai yana kiwon tumaki ya shirya shi don ayyuka masu wuya da kuma hakkin zama makiyayin al’ummar Isra’ila.b (Zab. 78:70, 71) Ta ayyukansa, Yesu ya nuna cewa shi makiyayi ne mai kyau. Jehobah yana ƙarfafa shi da kuma yi masa ja-gora sa’ad da yake kiwon ‘ƙaramin garkensa’ da kuma “waɗansu tumaki.” (Luk. 12:32; Yoh. 10:16) Da haka, Yesu ya zama Makiyayi Mai Kyau. Ya san garkensa da kyau da har yana kiran kowace tunkiya da sunanta. Saboda irin ƙaunar da yake yi wa tumakinsa, Yesu ya ba da ransa domin su sa’ad da yake duniya. (Yoh. 10:3, 11, 14, 15) Da yake shi Makiyayi Mai Kyau ne, Yesu ya cim ma abin da Dauda ba zai taɓa yi ba. Hadayar fansa da ya bayar ta buɗe hanyar ceton ’yan adam daga mutuwa. Babu abin da zai hana shi kiwon ‘ƙaramin garkensa’ zuwa rayuwa marar mutuwa a sama kuma zai ja-goranci “waɗansu tumaki” zuwa rai madawwami a sabuwar duniya ta adalci inda babu dabbobi masu kisa da ke da halin karen daji.—Karanta Yohanna 10:27-29.
Ka Bi Sarki Mai Cin Nasara
8. Yaya Dauda ya zama sarki mai cin nasara?
8 A matsayinsa na sarki, Dauda jarumi ne mai gaba gaɗi wanda ya kāre ƙasar mutanen Allah, “Ubangiji kuma ya ba Dauda nasara dukan inda ya nufa.” A ƙarƙashin sarautar Dauda, an faɗaɗa iyakar al’ummar daga kogin Masar zuwa kogin Yufiretis. (2 Sam. 8:1-14) Ta wurin ikon Jehobah, ya zama sarki mafi ƙarfi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Girman sunan Dauda kuwa ya tafi zuwa cikin dukan ƙasashe; Ubangiji kuwa ya sa tsoronsa cikin dukan al’ummai.”—1 Laba. 14:17.
9. Ka bayyana yadda Yesu a matsayin Sarki Mai jiran gado ya yi nasara.
9 Kamar Sarki Dauda, Yesu ba ya jin tsoro. A matsayinsa na Sarki Mai jiran gado, ya nuna ikonsa bisa aljanu, ta wajen ceton mutane daga ikonsu. (Mar. 5:2, 6-13; Luk. 4:36) Har babban maƙiyi, Shaiɗan Iblis, ba shi da iko a kansa. Da taimakon Jehobah, Yesu ya ci nasara bisa duniya, wadda take ƙarƙashin ikon Shaiɗan.—Yoh. 14:30; 16:33; 1 Yoh. 5:19.
10, 11. Menene hakkin Yesu a matsayin Sarki Jarumi a samaniya?
10 Shekara sittin bayan mutuwar Yesu da tashinsa daga matattu zuwa sama, manzo Yohanna ya ga wahayi da ya nuna Yesu a matsayinsa na Sarki Jarumi a samaniya. Yohanna ya rubuta: “Na duba kuma, ga farin doki; wanda ya ke zaune a kansa kuma yana da baka; kuma aka ba shi rawani: a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.” (R. Yoh. 6:2) Yesu ne mahayin farin dokin. An “ba shi rawani” a shekara ta 1914 sa’ad da aka naɗa shi Sarki a Mulki na samaniya. Bayan haka, “a kan nasara ya fita.” Hakika, kamar Dauda, Yesu sarki ne mai cin nasara. Ba da daɗewa ba da aka naɗa shi Sarkin Mulkin Allah, ya ci nasara a kan Shaiɗan a yaƙi kuma ya jeho shi da aljanunsa zuwa duniya. (R. Yoh. 12:7-9) Zai ci gaba da yin wannan hawa har sai ya gama “yin nasara,” ta wajen halaka mugun tsari na Shaiɗan gabaki ɗaya.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 19:11, 19-21.
11 Kamar Dauda, Yesu sarki ne mai juyayi, kuma zai kāre “taro mai-girma” a lokacin Armageddon. (R. Yoh. 7:9, 14) Ƙari ga haka, a ƙarƙashin sarautar Yesu da kuma abokan sarautarsa, wato, mutane 144,000 da aka ta da daga matattu, za a yi “tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (A. M. 24:15) Waɗanda aka ta da daga matattu a duniya za su samu begen rayuwa har abada. Rayuwa mai ban al’ajabi tana jiransu a nan gaba! Bari dukanmu mu kuɗiri aniya mu ci gaba da ‘yin nagarta,’ don mu kasance da rai sa’ad da duniya za ta cika da talakawan Dauda Mafi Girma, masu adalci da farin ciki.—Zab. 37:27-29.
An Amsa Addu’ar Sulemanu ta Hikima
12. Sulemanu ya yi addu’a a ba shi menene?
12 Sulemanu ɗan Dauda shi ma ya wakilci Yesu.c Sa’ad da Sulemanu ya zama sarki, Jehobah ya bayyana masa a mafarki kuma ya gaya masa cewa zai ba shi duk abin da ya roƙa. Sulemanu zai iya cewa a ƙara masa arziki, iko, ko kuma tsawon rai. Maimakon haka, ban da son kai, ya gaya wa Jehobah: “Ka ba ni yanzu hikima da sani, domin in fita, in shiga gaban wannan jama’a: gama wanene za ya iya shar’anta jama’an nan taka mai-girma haka?” (2 Laba. 1:7-10) Jehobah ya amsa addu’ar Sulemanu.—Karanta 2 Labarbaru 1:11, 12.
13. Me ya sa za a ce ba mai irin hikimar Sulemanu, kuma wanene Tushen hikimarsa?
13 Muddin Sulemanu ya kasance da aminci ga Jehobah, babu wani cikin tsaransa da zai kasance da irin kalmominsa na hikima. Sulemanu ya faɗi “karin magana dubu uku.” (1 Sar. 4:30, 32, 34, Littafi Mai Tsarki) An rubuta yawancin waɗannan karin maganar kuma har ila masu neman hikima suna ɗaukan su da tamani. Sarauniyar Sheba ta yi tafiya na mil dubu da ɗari biyar don ta gwada hikimar Sulemanu da “tambaya masu-wuya.” Abin da Sulemanu ya faɗa da kuma ni’imar mulkinsa sun burge ta. (1 Sar. 10:1-9) Littafi Mai Tsarki ya faɗi Tushen hikimar Sulemanu sa’ad da ya ce: “Dukan duniyar fa ta biɗi ganin Solomon, domin a ji hikimassa, wadda Allah ya sa cikin zuciyassa.”—1 Sar. 10:24.
Ka Bi Sarki Mai Hikima
14. A waɗanne hanyoyi ne Yesu “ya fi Sulemanu”?
14 Mutum ɗaya ne kawai ya fi Sulemanu hikima. Wannan Yesu Kristi ne, wanda ya kira kansa “wanda ya fi Solomon girma.” (Mat. 12:42) Yesu ya yi “maganar rai na har abada.” (Yoh. 6:68) Alal misali, Huɗuba na kan Dutse ya ƙara bayyana wasu ƙa’idodin da ke cikin ƙarin maganar Sulemanu. Sulemanu ya faɗi abubuwa da yawa da ke sa mai bauta wa Jehobah farin ciki. (Mis. 3:13; 8:32, 33; 14:21; 16:20) Yesu ya nanata cewa ana farin ciki na gaske ta wurin yin abubuwan da suka shafi bautar Jehobah da kuma cikar alkawuran Allah. Ya ce: “Masu [farin ciki] ne masu-ladabi a ruhu: gama mulkin sama nasu ne.” (Mat. 5:3) Waɗanda suke bin ƙa’idodin da ke cikin koyarwar Yesu suna kusantar Jehobah, wanda shi ne “maɓulɓular rai.” (Zab. 36:9; Mis. 22:11; Mat. 5:8) Kristi na wakiltar “hikimar Allah.” (1 Kor. 1:24, 30) A matsayin Sarki Almasihu, Yesu Kristi yana da “ruhun sani.”—Isha. 11:2.
15. Ta yaya za mu amfana daga hikima ta Allah?
15 Ta yaya ne mu mabiyan Sulemanu Mafi Girma za mu amfana daga hikima ta Allah? Tun da yake an bayyana hikimar Jehobah a Kalmarsa, dole ne mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu samu hikima ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau, musamman kalmomin Yesu, da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. (Mis. 2:1-5) Ƙari ga haka, muna bukatar mu nace wajen roƙon Allah ya ba mu hikima. Kalmar Allah ta tabbatar da mu cewa Allah zai amsa addu’armu ta neman taimako da muka yi da zuciya ɗaya. (Yaƙ. 1:5) Da taimakon ruhu mai tsarki, za mu samu hikima mai tamani a cikin Kalmar Allah da za ta taimake mu sa’ad da muke fuskantar ƙalubale kuma mu tsai da shawarwari masu kyau. (Luk. 11:13) An kira Sulemanu “Mai-wa’azi” wanda “ya yi ta koya ma mutane ilimi.” (M. Wa. 12:9, 10) Yesu a matsayin Shugaban ikilisiyar Kirista, shi ma mai yi wa mutanensa wa’azi ne. (Yoh. 10:16; Kol. 1:18) Saboda haka, yana da kyau mu halarci taron ikilisiya, inda ake ci gaba da ‘koyar’ da mu.
16. Wane kamanni ne ke tsakanin Sulemanu da Yesu?
16 Sulemanu ya cim ma abubuwa da yawa. Ya shirya tsarin gine-gine a dukan ƙasar, ya kula da gine-ginen fada, hanyoyi, gidan ruwa, wuraren ajiya, birane domin karusarsa, da kuma na mahayansa. (1Sa 9:17-19) Dukan al’ummar ta amfana daga ayyukan gine-gine da ya yi. Yesu ma magini ne. Ya gina ikilisiyarsa a kan “dutse,” wato, kansa ke nan. (Mat. 16:18) Zai kuma kula da aikin gini da za a yi a sabuwar duniya.—Isha. 65:21, 22.
Ka Bi Sarkin Salama
17. (a) Menene ya yi fice a sarautar Sulemanu? (b) Menene Sulemanu bai iya cim ma wa ba?
17 Sunan nan Sulemanu ya samo asali daga kalmar da ke nufin “salama.” Sarki Sulemanu ya yi sarauta ne a Urushalima, wadda take nufin “Samun Salama Mai Kashi Biyu.” Sarautarsa ta shekara 40 ta kawo salama da ba a taɓa irin ta ba a ƙasar Isra’ila. Littafi Mai Tsarki ya ce game da shekarun nan: “Yahuda da Isra’ila suka zauna lafiya, kowanne mutum ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa, tun daga Dan har zuwa Beer-sheba, dukan kwanakin Solomon.” (1 Sar. 4:25) Amma, duk da cewa Sulemanu mai hikima ne, bai iya ’yantar da talakawansa daga ciwo, zunubi da kuma mutuwa ba. Amma, Sulemanu Mafi Girma zai ’yantar da talakawansa daga dukan waɗannan abubuwa.—Karanta Romawa 8:19-21.
18. A ikilisiyar Kirista, wace albarka ce muke morewa?
18 Yanzu ma a ikilisiyar Kirista, muna da salama. Hakika, muna more aljanna ta ruhaniya ta gaskiya. Akwai salama a tsakanin mu da Allah da kuma mutane ’yan’uwanmu. Ga abin da Ishaya ya yi annabcinsa game da yanayin da muke morewa a yau: “Za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.” (Isha. 2:3, 4) Ta wajen yin abubuwan da suka jitu da ruhun Allah, muna sa a daɗa kasancewa da salama a aljanna ta ruhaniya.
19, 20. Waɗanne dalilai muke da su na yin farin ciki?
19 Amma, nan gaba za ta fi kyau. Yayin da mutane masu biyayya suke more salama sosai a ƙarƙashin sarautar Yesu, a hankali “za su tsira daga bautar ɓacewa” har su zama kamiltattu. (Rom. 8:21) Bayan sun ci gwaji na ƙarshe a ƙarshen Sarauta na Shekaru Dubu, “masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” (Zab. 37:11; R. Yoh. 20:7-10) Hakika, sarautar Yesu Kristi za ta fi ta Sulemanu a hanyoyin da ba mu sani ba tukun!
20 Kamar yadda Isra’ila ta yi farin ciki a ƙarƙashin shugabancin Musa, Dauda, da Sulemanu, za mu fi farin ciki a ƙarƙashin sarautar Kristi. (1 Sar. 8:66) Godiya ta tabbata ga Jehobah wanda ya aiko mana Ɗansa ƙaunatacce makaɗaici, wato, Musa, Dauda, da kuma Sulemanu Mafi Girma!
[Hasiya]
a Wataƙila sunan nan Dauda yana nufin “Ƙaunatacce.” A lokacin baftismar Yesu da kuma lokacin sake kamanninsa, Jehobah ya yi magana daga sama yana kiransa ‘Ɗana, ƙaunatacena.’—Mat. 3:17; 17:5.
b Dauda ya kuma zama kamar ɗan rago da ya amince da makiyayinsa. Ya dogara ga Makiyayi Mai Girma, Jehobah don kāriya da kuma ja-gora. Da cikakken tabbaci ya faɗi cewa: “Ubangiji makiyayina ne; ba zan rasa komi ba.” (Zab. 23:1) Yohanna Mai Baftisma ya nuna cewa Yesu ne “Ɗan Rago na Allah.”—Yoh. 1:29.
c Abin farin ciki, sunan Sulemanu na biyu shi ne Jedidiah, wanda yake nufi “Ƙaunataccen Yahweh.”—2 Sam. 12:24, 25.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya Yesu ya zama Dauda Mafi Girma?
• Ta yaya Yesu ya zama Sulemanu Mafi Girma?
• Menene ka fi so game da Dauda Mafi Girma, wanda shi ne kuma Sulemanu Mafi Girma?
[Hotunan da ke shafi na 31]
Hikimar da Allah ya ba Sulemanu tana wakiltan hikimar Sulemanu Mafi Girma
[Hotunan da ke shafi na 32]
Sarautar Yesu za ta fi ta Sulemanu da Dauda a hanyoyi da ba za mu iya ambata ba tukuna!