Bala’i Ba Zai Ƙara Faruwa Ba!
IDAN wani ya gaya maka cewa, “Ba da daɗewa ba, bala’i ba zai ƙara faruwa ba,” me za ka ce? Mai yiwuwa za ka ce, “Mafarki kake yi. Ba za a taɓa rabuwa da bala’i ba.” Ko kuma kana iya cewa a zuciyarka, ‘Wannan da gangan yake.’
Ko da yake bala’i yana faruwa kamar ba zai taɓa ƙarewa ba, akwai tabbataccen begen cewa za a samu canji. Amma, ba ’yan Adam ba ne za su kawo wannan canjin. ’Yan Adam ba su da cikakken fahimi na yadda abubuwa suke faruwa a halitta da kuma dalilin hakan, balle a ce su sarrafa su ko su canja su. Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā, wanda aka san shi da hikima da kuma lura, ya rubuta: “Mutum ba shi da iko shi gane dukan aikin da Allah ya ke yi a cikin duniya: gama komi yawan abin da mutum ya ke yi garin yin bincike, ba za ya gane ba; i, ko da mai-hikima yana tsammani za ya gane, ba za ya iya gāne ba.”—Mai-Wa’azi 8:17.
Idan ’yan Adam ba za su iya sarrafa bala’in da yanayi yake jawo ba, wane ne zai iya yin hakan? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mahaliccinmu ne zai kawo wannan canjin. Shi ne ya tsara yanayin duniya, kamar su faɗuwar ruwan sama. (Mai-Wa’azi 1:7) Akasin ’yan Adam, Allah yana da iko marar iyaka. Irmiya ya tabbatar da wannan gaskiyar sa’ad da ya ce: “Ya Ubangiji Yahweh! ga shi, ka yi sama da duniya bisa ga ikonka mai-girma, da zira’arka a miƙe; babu wani abin da ya fi ƙarfinka.” (Irmiya 32:17) Tun da yake Allah ne ya halicci duniya da dukan abubuwan da ke cikin ta, ya san yadda zai sarrafa su domin mutane su zauna cikinta lafiya da kwanciyar rai.—Zabura 37:11; 115:16.
Ta yaya Allah zai kawo wannan canji? Idan za ka tuna, talifi na biyu na jerin bayanan nan ya ambata cewa abubuwa masu firgitawa da suke faruwa a duniya a yau sun ƙunshi “alamar” da ke nuna “ƙarewar zamani.” Yesu ya ce: “Lokacin da kun ga waɗannan al’amura suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya kusa.” (Matta 24:3, LMT; Luka 21:31) Mulkin Allah, wanda gwamnati ce ta samaniya da Allah ya kafa, zai kawo gagarumin canje-canje a duniya, har da sarrafa ruwa, iska da makamantansu a yadda ba za su yi wa kowa illa ba. Ko da yake Jehobah Allah yana da ikon yin hakan da kansa, ya danƙa wa Ɗansa wannan aikin. Da yake yin magana game da wannan, annabi Daniyel ya ce: “Aka ba shi sarauta da daraja, da mulki, domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa.”—Daniyel 7:14.
An ba Ɗan Allah, Yesu Kristi, ikon kawo dukan canje-canjen da ake bukata domin a mai da duniya wuri mai daɗin zama. Shekaru dubu biyu da suka shige, sa’ad da Yesu yake duniya, ya ɗan nuna ikon da yake da shi na sarrafa iska, ruwa da makamantansu. Akwai lokacin da shi da almajiransa suke cikin kwalekwale a kan Tekun Galili, “babban hadari kuwa na iska ya tashi, raƙuman ruwa suka bubbuga har cikin jirgi, har jirgi yana ta cika.” Almajiransa suka firgita. Domin sun gan cewa za su halaka, sai suka juya ga Yesu. Mene ne Yesu ya yi? Ya “tsauta wa iska, ya ce wa teku, ka natsu, ka yi shuru. Iska ta kwanta, babbar natsuwa ta samu.” Almajiransa suka yi mamaki kuma suka yi tambaya: “Wanene wannan fa wanda har iska da teku suna biyayya da shi?”—Markus 4:37-41.
Tun daga lokacin, an ɗaukaka Yesu a sama kuma an ƙara masa iko. A matsayin Sarkin Mulkin Allah, yana da iko da kuma ƙwarewar kawo dukan canje-canjen da ake bukata domin ’yan Adam su zauna cikin lumana da kwanciyar rai a duniya.
Amma, kamar yadda muka gani, mutane ne suke jawo yawancin matsaloli da bala’in da suke addabar mutane, suna haddasa hakan ne saboda son kai da haɗama. Mene ne Mulkin zai yi game da waɗanda suka nace da yin waɗannan abubuwan kuma suka ƙi canja halinsu? Littafi Mai Tsarki ya yi maganar bayyanuwar Ubangiji Yesu “daga sama tare da mala’ikun ikonsa cikin wuta mai-huruwa, yana ɗaukan ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.” Babu shakka, zai “hallaka waɗanda ke hallaka duniya.”—2 Tasalonikawa 1:7, 8; Ru’ya ta Yohanna 11:18.
Bayan haka, wannan “Sarkin Sarakuna,” Yesu Kristi, zai sarrafa iska, da ruwa da makamantansu yadda ya ga dama. (Ru’ya ta Yohanna 19:16) Zai tabbatar da cewa talakawan Mulkin ba za su ƙara fuskantar bala’in da yanayi yake jawowa ba. Zai yi amfani da ikonsa ya daidaita yanayin ƙasa da kuma lokacin shekara, kamar su bazara, damuna, da sauran su a yadda za su amfane ’yan Adam. Sakamakon wannan shi ne cikar annabcin da Jehobah Allah ya yi ga mutanensa da daɗewa: “Ni ma sai in ba ku ruwan sama a cikin kwanakinsa, ƙasa za ta bada anfaninta, itatuwan saura kuma za su bada ‘ya’yansu.” (Levitikus 26:4) Mutane za su iya gina gidaje ba tare da jin tsoron cewa wani irin bala’i zai halaka su ba: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci anfaninsu.”—Ishaya 65:21.
Mene ne Kake Bukatar Ka Yi?
Babu shakka, kamar mutane da yawa, kana sha’awar yin rayuwa a duniyar da babu bala’in da ke jawo halaka. Amma, mene ne kake bukatar ka yi don ka kasance a wurin? Tun da yake “waɗanda ba su san Allah ba” da ‘waɗanda suka ƙi yin biyayya da bishara’ ba za su samu shiga cikin duniyar da bala’i ba za ta ƙara kasancewa ba, hakan ya nuna sarai cewa dole ne mutum ya koya game da Allah kuma ya goyi bayan tsarinsa na sarautar duniya tun yanzu. Allah yana son mu san shi kuma mu yi biyayya ga bisharar Mulkin da ya tsara ta wurin Ɗansa.
Hanya mafi kyau na yin hakan ita ce yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Yana ɗauke da umurnin da za su sa mu cancanci zama a mahalli mai kyau da zai wanzu a ƙarƙashin sarautar Mulkin. Me zai hana ka ka gaya wa Shaidun Jehobah su taimake ka don ka san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Za su yi farin cikin yin hakan. Gaskiyar ita ce, idan ka yi yunƙurin sanin Allah da kuma yin biyayya ga bishara, za ka shaida cikar kalmomin Misalai 1:33: “Amma dukan wanda ya saurara gareni za ya zauna lafiya, za ya zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa.”