Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
MENE ne ya motsa wata matashiya wadda ta fanɗare daga tarbiyyar addininta ta koma cikin hankalinta? Ka karanta abin da ta ce.
“Yanzu rayuwata tana da ma’ana.”—LISA ANDRÉ
SHEKARAR DA AKA HAIFE TA: 1986
ƘASAR DA AKA HAIFE TA: LUXEMBOURG
TARIHI: ƊIYA MUBAZZARA
RAYUWATA A DĀ: Na girma ne a Bertrange, wani ƙaramin gari mai tsabta da arziki da kwanciyar hankali, kusa da birnin Luxembourg. Ni ce ’yar auta a cikin yara biyar. Iyayena Shaidun Jehobah ne, kuma sun yi ƙoƙarin koya wa ni da ’yan’uwana maza da mata tarbiyyar Kirista.
Kafin na kai ’yar shekara 15, na soma shakka sosai game da abubuwan da Shaidun Jehobah suke koyarwa. Da farko na yi watsi da wannan shakkar da nake yi, amma da sannu a hankali bangaskiyata ta fara mutuwa. Iyayena sun yi iya ƙoƙarinsu domin su taimake ni in bi tafarkin gaskiya, amma na ƙi amincewa da taimakon. Ba tare da sanin su ba, ina fita yawo da matasan da ba sa daraja iyayensu da hukuma. Ina son irin ’yancin da ke tattare da rayuwar da suke yi . Muna yawan zuwa fati da yin lalata kuma muna mugun shan giya da ƙwayoyi masu sa maye. Da farko, na yi farin cikin cewa ina tarayya da mutanen da nake ganin suna more rayuwa sosai.
Amma a gaskiya ba na farin ciki. Yin tarayya da waɗannan abokan ba ta da wata ma’ana; babu wanda ya damu da komi. Akasin haka, na damu sosai da al’amura irin su rashin adalci da ya zama ruwan dare a duniya. Da shigewar lokaci, na ƙara dulmuya cikin baƙin ciki.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Wata rana sa’ad da nake ’yar shekara 17, na samu kaina cikin wani hali na baƙin ciki. Ganin irin baƙin cikin da ke damu na, mahaifiyata ta gaya mini cewa na sake yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ta ƙarfafa ni in bincika abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa sa’an nan in yanke shawarar ko zan yi rayuwar da ta jitu da hakan ko a’a. Wannan tattaunawa ta kud-da-kud da muka yi ce ta canja rayuwata. Na yarda yayata Caroline da mijinta, Akif, su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ba a yi renonsa a matsayin Mashaidin Jehobah ba, amma ya zama hakan ne sa’ad da ya girma. Saboda irin rayuwar da Akif ya yi a dā, na ga cewa zan iya gaya masa dukan abubuwan da ke zuciyata, saboda hakan yana da muhimmanci sosai a gare ni.
Na san cewa irin rayuwar da nake yi ba ta cancanci Mashaidiya ba, amma da farko, na ɗauka cewa babu ruwan kowa da yadda nake tafiyar da rayuwata. Amma, daga nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi na fahimci cewa halina yana shafan yadda Jehobah yake ji. (Zabura 78:40, 41; Misalai 27:11) Na kuma fahimci cewa yana shafan mutane.
Yayin da nake ƙara bincika Littafi Mai Tsarki, na sami hujjoji masu gamsarwa da suka sa na gaskata cewa Kalmar Allah ce. Alal misali, na ga annabce-annabce da dama na Littafi Mai Tsarki da suka cika daidai. Wannan fahimtar ya taimake ni na warware shakkar da nake yi a dā.
Wajen shekara guda bayan na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ni da iyayena mun ziyarci yayana da ke hidima na ba da kai a ofishin reshe na Shaidun Jehobah a ƙasar Jamus. Sa’ad da na ga yadda yayana yake farin ciki, abin ya motsa ni sosai. Irin wannan farin cikin da nake nema ke nan! Sauran Shaidun da suke hidima a wurin ma sun burge ni. Sun bambanta sosai da mutane marar gaskiya, masu yawan son nishaɗi da nake tarayya da su. Ba da daɗewa ba bayan haka, na yi addu’a ga Jehobah daga zuciyata, na yi alkawarin cewa zan bauta masa har ƙarshen rayuwata. Sa’ad da na kai ’yar shekara 19, na nuna alamar keɓe kaina ga Jehovah ta wajen yin baftisma.
YADDA NA AMFANA: Yanzu rayuwata tana da ma’ana. Ina jin daɗin koya wa mutane Littafi Mai Tsarki domin su san Jehobah da kuma alkawuransa na nan gaba. Iyalita ma sun amfana, sun daina irin muguwar damuwar da suke yi saboda ni.
Ina sane da zunuban da na yi a dā, amma ina ƙoƙarin kawar da su daga zuciyata. A maimakon haka, ina mai da hankali a kan jin ƙai na Jehobah da kuma ƙaunar da yake nuna mini. Na amince da abin da aka rubuta a Misalai 10:22 inda aka ce: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”
[Bayanin da ke shafi na 20]
“Muna yawan zuwa fati da yin lalata kuma muna mugun shan giya da ƙwayoyi masu sa maye”
[Bayanin da ke shafi na 21]
“Ina sane da zunuban da na yi a dā, amma ina ƙoƙarin kawar da su daga zuciyata”