Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/1 pp. 18-19
  • Lokacin da Ya Kamata Mu Kasance a Farke

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Lokacin da Ya Kamata Mu Kasance a Farke
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Yaro Da Ya Yi Barci
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • “Ku Yi Tsaro”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/1 pp. 18-19

Ku Koyar da Yaranku

Lokacin da Ya Kamata Mu Kasance a Farke

WATAƘILA za ka yarda cewa kasancewa a farke sa’ad da kake makaranta yana da muhimmanci. Yara da yawa suna jin barci sa’ad da suke cikin aji, amma dole ne ka kasance a farke idan kana son ka fahimci abin da ake koyarwa. Mai yiwuwa kana zuwa taro inda kake nazarin Littafi Mai Tsarki.

Mene ne kake bukatar ka yi don ka kasance a farke?—a Wani abin da zai taimaka maka shi ne ka riƙa yin barci da wuri da dare. Wataƙila barcin rana kaɗan zai taimaka. Bari mu ga abin da za mu iya koya daga abin da ya faru da wani matashin da barci ya ɗauke shi a wata tsakiyar daren da manzo Bulus yake ba da jawabi. Ka duba Littafi Mai Tsarki a Ayyukan Manzanni sura 20, ayoyi 7 zuwa 12, domin ka ga abin da ya faru.

Bulus ya ziyarci ikilisiyar da ke Taruwasa, wani birni da ke bakin teku inda jirage suke tsayawa. Littafi Mai Tsarki ya ce Bulus “yana da niyar tashi washegari” da jirgin ruwa. Saboda haka, “ya tsawanta zancensa har tsakiyar dare.” Mun karanta: ‘Wani saurayi kuma, wai shi Aftikos, yana zaune a kan taga, sai barci mai nauyi ya rinjaye shi; tun Bulus yana ƙara yin huɗuba tukuna.’ Me ya faru bayan haka?—

Aftikos ya faɗo daga tagar “bene na uku.” Bulus da sauran mutane suka sauko daga benen a guje. Amma Aftikos ya riga ya mutu! Ka yi tunanin irin baƙin cikin da suka yi!— Littafi Mai Tsarki ya ce Bulus ya ɗauki Aftikos kuma ya rungume shi. Bayan haka, cike da farin ciki Bulus ya ce musu, ‘kada ku damu, lafiyarsa ƙalau!’ Allah ya ta da Aftikos daga matattu!

Mene ne muka koya game da Allah daga abin da ya faru da Aftikos?— Jehobah, Ubanmu na sama, zai iya ta da waɗanda suka mutu daga matattu, har da yara. Irin sani da ƙaunar da Jehobah yake maka sun fi na iyayenka. Sa’ad da Yesu yake duniya, ya bayyana irin halin Ubansa, sa’ad da ya rungumi yara ƙanana kuma ya yi musu albarka. Kuma ya ta da yara daga matattu, har da wata yarinya ’yar shekara 12.

Yaya kake ji da ka san cewa Ubanka na sama yana ƙaunar ka?— Hakika, hakan yana sa mu ƙaunace Jehobah kuma mu bi abin da Ya faɗa. Ka san yadda za mu iya nuna cewa muna ƙaunar Shi?— Hanya ɗaya ita ce mu riƙa faɗin cewa muna ƙaunarsa. Yesu ya ce: “Ina ƙaunar Uba.” Amma, ba da baki kawai Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar Allah ba. Ya nuna hakan ta wajen abin da ya yi.

Yesu ya yi biyayya ga Allah. “Gama kullum ina aika abin da ya gamshe shi,” in ji Yesu. Domin mu faranta ran Jehobah da na Ɗansa, Yesu, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu mu kasance a farke a lokacin da ya kamata mu yi hakan.

Ka karanta wuraren nan a cikin naka Littafi Mai Tsarki

Ayyukan Manzanni 20:7-12

Luka 8:49-56

Yohanna 8:29; 14:31

[Hasiya]

a Idan kana karatun ne da yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata kuma ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba