Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/1 pp. 5-9
  • Babu Shakka Za A Kawo Ƙarshe Ga Miyagun Ayyuka!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Babu Shakka Za A Kawo Ƙarshe Ga Miyagun Ayyuka!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mutane Suna Canjawa, Yanzu Ma Hakan
  • Annabcin Rayuwarmu Ta Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Jehobah Yana Son Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
    Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
  • Sabuwar Duniya—Za Ka Kasance A Can?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/1 pp. 5-9

Babu Shakka Za A Kawo Ƙarshe Ga Miyagun Ayyuka!

ALLAH ya ba mu hurarriyar Kalmarsa, wadda ta bayyana dalilin da ya sa mutane suke yin miyagun ayyuka. Ya kuma ba mu ’yancin yin zaɓi da kuma ingancin iya kame kanmu, wanda ya sa ya kasance mana da sauƙi mu ƙi yin miyagun ayyuka. (Kubawar Shari’a 30:15, 16, 19) Da hakan, za mu fahimci kowane ɗigon mugunta da muke da shi kuma mu yi gyara a kai. Daga baya, ƙin yin mugunta zai sai mu da waɗanda suke kusa da mu su samu farin ciki.—Zabura 1:1.

Miyagun ayyukan da ’yan Adam suke yi ya ci gaba da damun duniyar nan duk da cewa wasu suna ƙoƙarin ƙin yin miyagun ayyuka. Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi: “Ka san wannan, cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo.” Don nuna abin da ya sa “miyagun zamanu” suke da wuya sosai, ya ci gaba da cewa: “Mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, mafiya son annishuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta: daga wajen waɗannan kuma sai ka bijire.”—2 Timotawus 3:1-5.

Wataƙila ka lura da furcin nan “kwanaki na ƙarshe” a cikin wannan annabcin da aka yi ƙaulinsa a sama. Mene ne hakan yake nufi a gareka? Kamar yadda mutane da yawa suka fahimta, furcin nan “kwanaki na ƙarshe” yana nufin cewa akwai abin da zai zo ƙarshe. Amma mene ne zai zo ƙarshe? Ka lura da alkawarin da Allah ya yi a cikin Kalmarsa.

Za a cire miyagun mutane gabaki ɗaya.

“In an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; Za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—ZABURA 37:10, 11.

“Ubangiji yana kiyayar da dukan waɗanda ke ƙaunarsa; Amma za ya halaka dukan miyagu.”—ZABURA 145:20.

Ba za a sake yin zalunci kuma ba.

“Za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: Matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.”—ZABURA 72:12, 14.

“Ana bege halitta da kanta kuma za ta tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.”—ROMAWA 8:21.

Za a biya bukatun zahiri na mutane.

“Amma kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratar da su.”—MIKAH 4:4.

“Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba; gama kamar yadda kwanakin itace su ke, hakanan kwanakin mutanena za su zama, zaɓaɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”—ISHAYA 65:21, 22.

Shari’a za ta kasance.

‘Allah fa ba za ya rama ma zaɓaɓunsa ba, da su ke yi masa kuka dare da rana . . . ? Ina ce maku, da sauri za ya rama masu.’—LUKA 18:7, 8.

“Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba; ana kiyaye su har abada.”—ZABURA 37:28.

Za a sauya son kai da adalci.

“Mazaunan duniya su kan koyi adalci.”—ISHAYA 26:9.

“Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.”—2 BITRUS 3:13.

Mutane Suna Canjawa, Yanzu Ma Hakan

Babu shakka, dukanmu za mu yi farin ciki game da wannan alkawuran. Amma wane tabbaci ne muke da shi cewa za ya cika? Hakika, muna da alamar da ta nuna cewa Allah zai cika alkawuransa. Mece ce alamar? Alamar ita ce cewa miliyoyin mutane a dukan duniya sun riga sun samu nasara wajen magance son kai, zina, ko halin nuna ƙarfi kuma sun koya kasancewa masu gaskiya, salama, da kuma kirki. A yau, Shaidun Jehobah, da adadinsu ya fi miliyan bakwai, sun zama ’yan’uwa na dukan duniya da suka magance wariyar launin fata, ƙabilanci, kishin ƙasa, siyasa, tattalin arziki, waɗanda a yau suna jawo ƙiyayya, nuna ƙarfi, da kuma zubar da jini a dukan zamani.a Da yake ana yin waɗannan canje-canje a yau ya ba da dalilin gaskata cewa alkawuran Allah za su cika a dukan duniya.

Mene ne ke kawo irin waɗannan canje-canjen? Amsar tana cikin wani alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, wanda annabi Ishaya ya rubuta. Ya rubuta:

“Kerkeci za ya zauna tare da ɗan rago, damisa kuma za ta kwanta tare da ɗan akuya; da ɗan maraƙi da ɗan zaki da kiyayayyen ɗan sā za su zauna wuri ɗaya; ɗan yaro kuwa za ya bishe su. . . . Zaki kuwa za ya ci ciyawa kamar sā. Jariri mai-shan mama za ya yi wasa a bakin ramin kumurci, ’ya’yayyen yaro kuma za ya sa hannu a gidan kāsa. Ba za a yi cuci kuwa ba; kuma ba za su yi ɓarna ko’ina cikin dutsena mai-tsarki ba: gama duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.”—Ishaya 11:6-9.

Shin wannan annabcin yana magana ne game da lokacin da dabbobi za su kasance cikin salama da ’yan Adam? A’a, ya fi hakan. Ka lura cewa sashe na ƙarshe ya nuna abin da ya kawo canjin: “Duniya za ta cika da sanin Ubangiji.” Shin ilimi game da Jehobah zai canja halayen dabbobi? Da kyar. Amma zai iya canja mutane! Wannan annabcin ya faɗa cewa waɗanda suke da halayen dabbobi za su daina halayen kuma za su koya halaye irin na Kristi domin suna koya da kuma yin amfani da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

Ka yi la’akari da misalin Pedro.b Yana tunanin cewa yana neman shari’a sa’ad da ya shiga ƙungiyar ta’addanci. Bayan an koyar da shi, aka ce masa ya sa bam a barikin ’yan sanda. Sa’ad da yake yin shirin ya yi hakan, aka kama shi. Pedro ya yi watanni sha takwas a gidan fursuna, inda ya ci gaba da ayyukan ta’addancin. Yayin nan kuma, matar Pedro ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Sa’ad da aka sake shi, Pedro ma ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma abin da ya koya game da Jehobah Allah ya motsa shi ya yi canje-canje sosai a halayensa da kuma salon rayuwarsa. “Ina wa Jehobah godiya don ban taɓa kashe kowa ba a waɗannan shekaru da nake ta’addanci,” in ji Pedro. “Yanzu ina yin amfani da takobin ruhun Allah, wato, Littafi Mai Tsarki, don na gaya wa mutane saƙon salama da kuma shari’a ta gaske, wato, bishara game da Mulkin Allah.” Har ma Pedro ya je ya yi wa’azin salama da kuma yadda duniya za ta kasance ba tare da nuna ƙarfi ba a barikin da ya so ya sa wa bam.

Canje-canje da Kalmar Allah take sa mutane su yi yana ba da ƙarin dalilin da ya sa za mu kasance da bangaskiya ga alkawarin Allah cewa hakika ƙarshen dukan miyagun ayyuka zai zo. Hakika, mutane ba za su yi mugunta har abada ba amma za su yi canji. Jim kaɗan Jehobah zai cire tushen mugunta, wato, Shaiɗan Iblis, wanda ke ja-goran abubuwan da ke faruwa a duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.” (1 Yohanna 5:19) Amma ba da daɗewa ba, za a kawar da shi. Za a halaka waɗanda suka ƙi barin mugun halayensu. Zai zama abin ban al’ajabi mu yi rayuwa a lokacin!

Mene ne ya kamata mutum ya yi don ya kasance a irin wannan yanayin a nan gaba? Ka tuna cewa “sanin Ubangiji” ne ke sa mutane su yi canje-canje a yau kuma wannan sanin zai kawo canji a dukan duniya a nan gaba. Ta samun cikakken sani na Littafi Mai Tsarki da kuma yin amfani da shi, kamar yadda Pedro ya yi, za ka samu tabbacin yin rayuwa a duniyar da “adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13) Muna ƙarfafa ku ku yi amfani da zarafin da kuke da shi don ku san Allah da Yesu Kristi, domin hakan zai iya sa a samu rai na har abada.—Yohanna 17:3.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayyani, ka duba mujallar nan Shaidun Jehovah—Su Wanene ne Su? Mene ne Suka Gaskata? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

b An canja sunan.

[Bayanin da ke shafi na 9]

Kai ma za ka samu tabbacin yin rayuwa a duniyar da “adalci yake zaune.”—2 BITRUS 3:13

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba