“Ayanannen Lokaci” Ya Kusa
KAMAR annabi Habakkuk, almajiran Yesu sun ƙosa su ga ƙarshen wahala. Bayan sun koyi abin da Mulkin Allah zai yi don ya daidaita abubuwa a duniya, sai suka tambayi Yesu: “Yaushe waɗannan abubuwa za su zama? me ne kuma alamar zuwanka [a ikon Mulki] da cikar zamani?” (Matta 24:3) Yesu ya amsa da cewa Jehobah Allah ne kawai ya san daidai lokacin da Mulkin zai soma cikakken sarauta a duniya. (Matta 24:36; Markus 13:32) Amma Yesu da wasu sun annabta wasu aukuwa da za su nuna cewa lokacin ya kusa.—Duba akwatin da ke hannun dama.
Ka amince cewa waɗannan abubuwan suna faruwa a yau? Yesu ya kuma annabta cewa za a cim ma aikin ilimantarwa a dukan duniya. Ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14.
Wannan daidai ne da abin da ke faruwa a duniya yau. Shaidun Jehobah suna yin wannan aikin. A ƙasashe 236, fiye da Shaidu miliyan bakwai suna gaya wa mutane abin da Mulkin zai yi, kuma suna taimaka musu su bi farillan Allahn da ya ƙudurta ya kawo ƙarshe ga wahala da azaba. Ka ci gaba da koyo game da Mulkin Allah, kuma za ka samu zarafin yin rayuwa a duniya ba tare da wahala ba, har abada.
[Akwati da ke shafi na 8]
Nassosi da Suka Yi Magana Game da Kwanaki na Ƙarshe
MATTA 24:6, 7; RU’YA TA YOHANNA 6:4
• Yaƙe-Yaƙen da babu irinsu
• Girgizar ƙasa
• Yunwa
LUKA 21:11; RU’YA TA YOHANNA 6:8
• Annoba
• Ƙaruwar taka doka
• Rashin ƙauna
RU’YA TA YOHANNA 11:18
• Halaka duniya
• Mugun son kuɗi
• Rashin biyayya ga iyaye
• Cika son kai
• Rashin ƙauna irin ta tabi’a
• Masu tsegumi
• Rashin kamewar kai a dukan jama’a
• Rashin nagarta
• Son annashuwa fiye da Allah
• Munafukai da yawa suna da’awar zaman Kirista
• Annabawan ƙarya da yawa za su taso
• Tsananta Kiristocin gaskiya
• Rashin yin biyayya da gargaɗin Littafi Mai Tsarki
[Hoton da ke shafi na 8]
A dukan duniya, Shaidun Jehobah suna koya wa wasu game da Mulkin Allah