Ƙage Na 6: Allah Ya Amince Da Yin Amfani Da Gumaka Da Siffofi A Bauta
Menene tushen wannan ƙagen? “Kiristocin zamanin dā ba sa yin amfani da gumaka a bauta . . . An bayyana cewa soma bauta da gumaka a coci da aka yi a ƙarni na huɗu da na biyar ya dace domin wai jahilai za su fi koyo game da Kiristanci daga su fiye da daga huɗuba da kuma littattafai.”— Cyclopedia of Biblical, Theological, and Ecclesiastical Literature, na McClintock and Strong, Volume 4, shafuffuka na 503 da 504.
Menene Littafi Mai Tsarki ya ce? “Ba za ka misalta wata ƙira, ko surar abin da ke cikin sama daga bisa, ko abin da ke cikin duniya daga ƙasa, ko kuwa abin da ke cikin ruwa daga ƙarƙashin ƙasa: ba za ka yi sujada garesu ba, ba kuwa za ka bauta musu ba.” (Fitowa 20:4, 5) Manzo Yohanna ya rubuta wa Kiristocin ƙarni na farko: “’Ya’yana ƙanƙanana, ku tsare kanku daga gumaka.”—1Yohanna 5:21.
Shin gumaka kamar yadda coci suke da’awa, hanya ce ta kusantar da kuma ɗaukaka abin da suka wakilta ne? “Da farko,” in ji The Encyclopedia of Religion, “wataƙila ana yin amfani da gumaka ne don koyar da mutane da kuma don ado, musamman, abin da suka ce ke nan. Amma ba da daɗewa ba aka soma amfani da su don bauta. Musamman hakan ya bayyanu sosai a siffofin da ake amfani da su a cocin Orthodox a Gabas.” Amma dai, annabi Ishaya ya yi tambaya: “Da wa za a iya kwatanta Allah? Wa zai iya faɗar yadda yake?”—Ishaya 40:18, Littafi Mai Tsarki.
Ka gwada waɗannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki: Ishaya 44:13-19; Ayyukan Manzanni 10:25, 26; 17:29; 2 Korintiyawa 5:7
GASKIYA:
Allah bai amince da yin amfani da gumaka da siffofi ba
KA ƘI ƘAGE, KA MANNE WA GASKIYA
Menene za mu iya kammalawa daga ’yan bayanai game da ƙagen da coci da yawa suke koyarwa? Waɗannan “tatsuniyoyi [Hellenanci, myʹthos] da aka ƙaga da wayo” ba za su iya musanya gaskiya mai sauƙi da mai ban ƙarfafa da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba.—2 Bitrus 1:16.
Saboda haka, da zuciya ɗaya, kada ka yi jinkirin gwada abin da aka koya maka daga tushen gaskiya, wato, Kalmar Allah. (Yohanna 17:17) Da haka, wannan alkawarin zai kasance gaskiya a gare ka: ‘Za ka san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da kai.’—Yohanna 8:32.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 15]
Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.