Ƙage Na 5: Maryamu Mahaifiyar Allah ce
Menene tushen ƙagen? “An soma bauta wa mahaifiyar Allah sa’ad da . . . kafirai da yawa suka shigo cikin coci. . . . Imaninsu da abin da suka gaskata [wato, na kafirai da suka zama Kiristoci] an samo su ne tun shekaru dubbai daga borin ‘babbar mahaifiya’ allahiya da ‘budurwa daga allah.’”—The New Encyclopædia Britannica (1988), Volume 16, shafuffuka na 326 da 327.
Menene Littafi Mai Tsarki ya ce? ‘Za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. . . . Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.’—Tafiyar tsutsa tamu ce; Luka 1:31-35, Littafi Mai Tsarki.
Waɗannan kalaman Nassi sun bayyana dalla-dalla cewa Maryamu mahaifiyar “Ɗan Allah” ce, ba Allah da kansa ba. Zai yiwu ta dauƙi Wanda ‘samman sammai ba su da ikon su karɓe shi’ a cikinta kuwa? (1 Sarakuna 8:27) Bata taɓa yin irin wannan da’awar ba. Koyarwar Allah Uku Cikin Ɗaya ne ya ruɗar da mutane game da ainihin matsayin Maryamu. Ta kiranta Theotokos (kalmar Hellenanci wanda ke nufin “mai-ɗauke da Allah”), ko “Mahaifiyar Allah,” Majalisar Afisa, a 431 A.Z., ta sa mutane su soma yi wa Maryamu sujjada. An daɗe ana bautar gunki da bauta wa allahiyar ni’ima Artimas a birnin Afisa inda majalisar coci take.
Hakan ya sa fasalolin bautar sifar Artimas wadda ta “‘faɗo daga sama,” kamar rukuni, suka shigo cikin bautar Maryamu. (Ayyukan Manzanni 19:35, LMT) Wani abu kuma da ya shigo cikin koyarwar Kiristoci shi ne yin amfani da siffofin Maryamu da na wasu a bauta.
Ka gwada waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki: Matta 13:53-56; Markus 3:31-35; Luka 11:27, 28
GASKIYA:
Maryamu mahaifiyar Ɗan Allah ce, ba Allah ba da kansa. Ƙagen Allah Uku Cikin Ɗaya ne ya haifar da bauta wa Maryamu a matsayin Mahaifiyar Allah