Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 9/15 pp. 25-29
  • Kana Ɗaukan Tanadin Da Jehobah Ya Yi Don Ya Cece Ka Da Tamani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Ɗaukan Tanadin Da Jehobah Ya Yi Don Ya Cece Ka Da Tamani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ya Sa Muke Bukatar Ceto
  • Sadaukarwar da Yesu Ya Yi Don Ya Cece Mu
  • Abin da Jehobah Ya Yi Don Ya Cece Mu
  • Yaya Za Ka Nuna Cewa Kana Godiya don Ceton?
  • Abin da Jehobah Ya Yi don Ya Cece Mu Daga Zunubi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Hadayu Na Yabo Da Ke Faranta Wa Jehovah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 9/15 pp. 25-29

Kana Ɗaukan Tanadin Da Jehobah Ya Yi Don Ya Cece Ka Da Tamani?

“Albarka ga Ubangiji, Allah na Isra’ila; Gama ya ziyarci mutanensa, ya yi masu fansa.”—LUK 1:68.

1, 2. Yaya za a iya kwatanta tsananin yanayi da muke ciki, kuma waɗanne tambayoyi za mu tattauna?

A CE kana kwance a kan gado a asibiti. Kana sashen da kowa da ke wajen yana irin ciwo ɗaya, ciwon da ba shi da magani. Sa’ad da ka ji cewa wani likita yana ƙoƙari ya samo maganin ciwon, sai ka kasance da bege. Kana son ka san kome game da binciken da likitan yake yi. Wata rana sai ka ji cewa an samo maganin! Likitan da ya samo maganin ya yi sadaukarwa sosai don ya yi hakan. Yaya za ka ji? Babu shakka za ka daraja da kuma nuna godiya ga mutumin da ya sa ya yiwu kai da kuma mutane da yawa ku samu ceto daga mutuwa.

2 Wannan yanayin zai zama kamar zugugu, amma ya yi daidai da yanayin da dukanmu ke ciki. Kowanenmu yana cikin yanayin da ya fi wanda aka kwatanta a nan tsanani. Muna bukatar mai ceto sosai. (Karanta Romawa 7:24.) Jehobah ya yi sadaukarwa sosai don ya cece mu. Ɗansa ma ya yi sadaukarwa sosai. Bari mu bincika tambayoyi huɗu masu muhimmanci. Me ya sa muke bukatar ceto? Menene Yesu ya yi don ya cece mu? Menene Jehobah ya sadaukar? Yaya za mu nuna cewa muna daraja tanadin ceto da Allah ya yi?

Abin da Ya Sa Muke Bukatar Ceto

3. Yaya zunubi yake kama da annoba?

3 Bisa wani kimantawa da aka yi kwanan nan, ɗaya cikin cututtuka da suka fi halakarwa a tarihin ’yan adam shi ne annoba da ake kiran Spanish influenza na shekara ta 1918, wadda ta kashe miliyoyin mutane. Wasu cututtuka sun fi kisa a wani azanci. Ko da yake mutane kalilan suna iya kamuwa da waɗannan cututtuka, yawancin waɗannan mutane suna mutuwa.a Amma, idan muka gwada zunubi da irin wannan annoba kuma fa? Ka tuna da kalmomin Romawa 5:12: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da shi ke duka sun yi zunubi.” Dukan mutane sun kamu da zunubi, tun da yake dukan ’yan adam ajizai suna zunubi. (Karanta Romawa 3:23.) Mutane nawa ne suke mutuwa don zunubi? Bulus ya rubuta cewa zunubi yana jawo mutuwa ga ‘dukan mutane.’

4. Menene ra’ayin Jehobah game da tsawon rayuwarmu, ta yaya ra’ayinsa ya yi dabam da na mutane da yawa a yau?

4 Mutane da yawa suna ganin cewa zunubi da mutuwa fasaloli ne na rayuwa. Suna damuwa game da mutuwar kadangatse, amma suna gani mutuwa da mutane suke yi don tsufa daidai ne. Yana da sauƙi ’yan adam su mance da ra’ayin Mahaliccin. Tsawon rayuwarmu ya ragu sosai fiye da yadda ya nufa. Hakika, babu ɗan adam da ya rayu na “rana ɗaya” a gaban Jehobah. (2 Bit. 3:8) Shi ya sa Kalmar Allah ta ce rayuwarmu kamar ciyawa take ko kuma shaƙar iska. (Zab. 39:5; 1 Bit. 1:24) Muna bukatar mu tuna da wannan ra’ayin. Me ya sa? Idan muka fahimci tsananin “cutar” da muka kamu da ita, za mu fi fahimtar amfanin “warkarwar” wato, cetonmu.

5. Menene muka yi hasararsa domin zunubi?

5 Don mu fahimci tsananin zunubi da sakamakonsa, dole ne mu yi ƙoƙari mu fahimci hasarar da zunubi ya kawo mana. Hakan zai yi wuya da farko domin zunubi ya sa mun yi hasarar abin da ba mu taɓa samu ba. Adamu da Hauwa’u da farko sun more kamiltaccen rai. Suna da kamiltaccen hankali da jiki, suna iya zaɓan su kame tunaninsu, yadda suke ji, da ayyukansu. Da haka za su iya su ci gaba da koyan halaye masu kyau a matsayin bayin Jehobah Allah. Maimakon haka, suka ƙi wannan kyauta mai tamani. Ta wajen zaɓan su yi zunubi ga Jehobah, da su da ’ya’yansu sun yi hasarar irin rayuwa da Jehobah yake so su yi. (Far. 3:16-19) Sun kawo wa kansu da mu kuma “cuta” da muke tattaunawa game da ita. Ya yi daidai da Jehobah ya hukunta su. Amma, ya miƙa mana begen ceto.—Zab. 103:10.

Sadaukarwar da Yesu Ya Yi Don Ya Cece Mu

6, 7. (a) Ta yaya Jehobah ya soma nuna cewa cetonmu zai bukaci sadaukarwa mai girma? (b) Menene za mu iya koya daga hadayu da Habila ya miƙa da kuma ubanni da suka rayu kafin a ba da Dokar?

6 Jehobah ya san cewa zai yi sadaukarwa sosai don ya ceci ’ya’yan Adamu da Hauwa’u. A cikin annabci da ke rubuce a Farawa 3:15, mun koya abin da ceton ya ƙunsa. Jehobah zai yi tanadin “zuriya,” mai ceto, wanda wata rana zai halaka Shaiɗan. Amma, wannan mai ceto zai sha wahala, za a ji masa rauni na alama a dudduge. Mun fahimci cewa ƙuje dudduge yana da zafi kuma zai iya rage abin da mutum zai iya yi ko kuma ya raunana shi, amma menene hakan yake nufi a wannan annabci? Menene Zaɓaɓɓe na Jehobah zai jimre?

7 Domin a ceci ’yan adam daga zunubi, mai ceton zai yi tanadin hanyar kafara, wato, yadda zai sulhunta ’yan adam ga Allah ta wajen kawar da sakamakon zunubi. Menene hakan zai ƙunsa? Da akwai abubuwa da suka nuna da farko cewa za a bukaci hadaya. Sa’ad da Habila, mutum na farko mai aminci ya miƙa hadayun dabbobi ga Jehobah, ya samu amincewar Allah. Daga baya ubanni masu jin tsoron Allah kamar su Nuhu, Ibrahim, Yakubu, da Ayuba sun miƙa irin waɗannan hadayu da suka faranta wa Allah rai. (Far. 4:4; 8:20, 21; 22:13; 31:54; Ayu. 1:5) Ƙarnuka bayan haka, Dokar Musa ta sa mutane su san game da batun hadayu sosai.

8. Menene babban firist yake yi a Ranar Kafara da ake yi kowace shekara?

8 Hadayu mafi muhimmanci da Dokar take bukatar a miƙa sune waɗanda ake miƙawa a Ranar Kafara kowace shekara. A wannan ranar, babban firist yana yin ayyuka na alama masu yawa. Yana miƙa hadayu ga Jehobah don kafarar zunubai, na farko na rukunin firistoci ne, bayan hakan sai ya miƙa na ƙabilu da ba firistoci ba. Babban firist yana shigan Wuri Mafi tsarki na mazauni ko kuma haikali, wannan wurin ne kawai zai shiga kuma a wannan rana na shekarar kawai. A wajen yana yayyafa jinin hadayu a gaban akwatin alkawari. A saman wannan akwati mai tsarki, a wani lokaci gajimare mai haske da walƙiya da ke wakiltar bayanuwar Jehobah Allah yakan bayyana.—Fit. 25:22; Lev. 16:1-30.

9. (a) A Ranar Kafara, wanene babban firist yake wakilta, kuma menene hadayu da ya miƙa yake nunawa? (b) Menene yadda babban firist ya shiga cikin Wuri Mafi Tsarki yake wakilta?

9 An hure manzo Bulus ya bayyana ma’anar waɗannan ayyuka na alama. Ya nuna cewa babban firist yana wakiltar Almasihu, Yesu Kristi, kuma miƙa hadayun yana nuni ga mutuwar hadaya ta Kristi. (Ibran. 9:11-14) Wannan kamiltacciyar hadaya za ta yi tanadin kafara na gaske ga rukuni biyu, wato, rukunin firistoci na ’yan’uwan Kristi shafaffu na ruhu guda 144,000 da kuma “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16) Sa’ad da babban firist ya shiga Wuri Mafi Tsarki, yana wakiltar yadda Yesu ya shiga cikin sama kanta don ya miƙa wa Jehobah Allah amfanin hadayar fansa.—Ibran. 9:24, 25.

10. Annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Almasihu zai fuskanci menene?

10 A bayane yake cewa ceton ’ya’yan Adamu da Hauwa’u zai bukaci sadaukarwa mai girma. Almasihu zai ba da ransa! Annabawan Nassosin Ibrananci sun ba da ƙarin bayani game da wannan. Alal misali, annabi Daniel ya faɗa kai tsaye cewa za a “datse” ko kuma kashe “Masiya sarki” domin a “yi aikin sulhu saboda mugunta.” (Dan. 9:24-26) Ishaya ya annabta cewa za a ƙi Almasihu, a tsananta masa, a kashe shi, ko kuma a ji masa rauni, domin ya ɗauki zunuban ’yan adam ajizai.—Isha. 53:4, 5, 7.

11. A waɗanne hanyoyi ne Ɗan Jehobah ya nuna yana shirye ya ba da kansa don cetonmu?

11 Kafin ya zo duniya, Ɗan Allah makaɗaici ya san abin da cetonmu zai bukaci daga wajensa. Zai sha wahala sosai kuma a kashe shi. Sa’ad da Ubansa ya gaya masa abubuwan da zai fuskanta, ya ja da baya ne ko kuma ya yi tawaye? Bai yi hakan ba, amma ya miƙa kai da yardan rai ga nufin Ubansa. (Isha. 50:4-6) Hakan nan ma, sa’ad da yake duniya, Yesu ya yi biyayya ta yin nufin Ubansa. Me ya sa? Ya ba da amsa guda da waɗannan kalaman: “Ina ƙaunar Uba.” Ya ba da wani amsa da waɗannan: “Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya bada ransa domin abokansa.” (Yoh. 14:31; 15:13) Saboda haka, Ɗan Jehobah ya cece mu domin yana ƙaunarmu. Ko da yake ya ba da ransa kamiltacce, ya yi farin cikin yin hakan domin cetonmu.

Abin da Jehobah Ya Yi Don Ya Cece Mu

12. Nufin wanene cewa a yi fansa, kuma me ya sa ya yi tanadinta?

12 Ba Yesu ba ne ya tsai da shawarar ba da hadayar fansa ko kuma yadda za a ba da hadayar. Maimakon haka, wannan hanyar ceto fanni ne na musamman wajen cika nufin Jehobah. Manzo Bulus ya nuna cewa bagadi da ke cikin haikali, inda ake miƙa hadayun, yana wakiltar nufin Jehobah. (Ibran. 10:10) Saboda haka, ceto da muka samu ta hanyar hadayar Kristi abu ne na farko kuma mafi muhimmanci da za mu biya Jehobah. (Luk 1:68) Abin da ya yi ya nuna cikakken nufinsa da kuma ƙaunarsa ga mutane.—Karanta Yohanna 3:16.

13, 14. Ta yaya misalin Ibrahim zai taimaka mana mu yi godiya ga abin da Jehobah ya yi dominmu?

13 Menene Jehobah ya sadaukar don ya nuna ƙaunarsa a gare mu a wannan hanyar? Yana da wuya mu fahimci abin da hakan ya ƙunsa? Amma, da akwai labarin Littafi Mai Tsarki da zai taimaka mana mu fahimci batun da kyau. Jehobah ya gaya wa Ibrahim mutum mai aminci ya yi wani abu mai wuya sosai, wato, ya miƙa ɗansa Ishaƙu hadaya. Hakika, Ibrahim uba ne mai ƙauna. Jehobah ya yi masa magana game da Ishaƙu a matsayin “tilonka, wanda ka ke ƙaunarsa.” (Far. 22:2) Duk da haka, Ibrahim ya ga cewa yin nufin Jehobah ya fi muhimmanci da ƙaunarsa ga Ishaƙu. Ibrahim ya yi biyayya. Amma, Jehobah bai bar Ibrahim ya yi abin da shi da kansa zai yi wata rana ba. Allah ya aika mala’ika ya tsayar da Ibrahim kafin ya yi hadaya da ɗansa. Ibrahim ya ƙuduri aniya ya yi biyayya ga Allahnsa a wannan gwaji mai wuya har da ya tabbata cewa begen ganin wannan saurayin kuma shi ne ta wurin tashin matattu. Amma yana da cikakkiyar bangaskiya cewa Allah zai yi irin wannan tashin matattu. Hakika, Bulus ya ce Ibrahim ya sake karɓan Ishaƙu ta wajen tashin matattu “cikin misali.”—Ibran. 11:19.

14 Yana da wuya mu ƙage baƙin ciki da Ibrahim ya yi sa’ad da yake shirya ya miƙa ɗansa. A wani azanci, abin da Ibrahim ya fuskanta ya kwatanta abin da Jehobah ya fuskanta sa’ad da yake ba da hadayar wanda ya kira ‘Ɗana ƙaunatacce.’ (Mat. 3:17) Ka tuna cewa azaba da Jehobah ya sha ya fi tsanani. Da shi da Ɗansa sun more cuɗanya tare na shekaru aru-aru. Ɗan ya yi aiki da farin ciki tare da Uban a matsayin “gwanin mai-aiki” ƙaunatacce da kuma Kakakinsa, “Kalman.” (Mis. 8:22, 30, 31; Yoh. 1:1) Ba za mu iya sanin abin da Jehobah ya jimre sa’ad da ake gana wa Ɗansa azaba, yi masa ba’a, kuma aka kashe shi kamar mai laifi. Jehobah ya yi sadaukarwa sosai don ya cece mu! To, ta yaya, za mu iya nuna cewa muna godiya don wannan ceton?

Yaya Za Ka Nuna Cewa Kana Godiya don Ceton?

15. Yaya Yesu ya kammala aiki mai girma na kafara, kuma menene hakan ya sa ya yiwu?

15 Yesu ya kammala aiki mai girma na kafara bayan an ta da shi zuwa sama. Da ya sake saduwa da Ubansa ƙaunatacce, ya miƙa masa amfanin hadayarsa. An samu albarka sosai bayan hakan. Hakan ya sa ya yiwu a gafarta zunubai gabaki ɗaya, na farko zunuban ’yan’uwa shafaffu na Kristi, sai kuma na “duniya duka.” Domin wannan hadaya, a yau dukan waɗanda suka tuba daga zunubansu da gaske kuma suka zama tabbatattun mabiyan Kristi suna iya more dangantaka na kud da kud da Jehobah Allah. (1 Yoh. 2:2) Yaya hakan ya shafe ka?

16. Ta yaya za mu kwatanta abin da ya sa ya kamata mu nuna godiya don ceto da Jehobah ya yi mana tanadinsa?

16 Bari mu koma ga kwatancin da aka ba da ɗazu. A ce likita da ya samo maganin ciwon ya koma wajen majiyyata da suke sashe ɗaya da kai kuma ya gaya musu: Duk majiyyaci da ya karɓi magani kuma ya sha daidai yadda aka gaya masa zai warke. Idan yawancinsu suka ƙi bin ja-gorar likitan kuma fa, suna faɗa cewa zai yi musu wuya ainun su sha maganin kuma su bi daidai yadda aka gaya musu? Za ka bi su ne, ko da yake kana da tabbacin cewa maganin zai yi aiki sosai? Ko kaɗan! Babu shakka, za ka nuna godiya kuma ka bi umurnin likitan sosai, wataƙila ma ka gaya wa wasu game da zaɓin da ka yi. Fiye da haka, ya kamata kowannenmu mu yi ɗokin nuna wa Jehobah yawan yadda muke godiya don ceto da ya sa ya yiwu ta wurin hadayar fansa na Ɗansa.—Karanta Romawa 6:17, 18.

17. A waɗanne hanyoyi ne za ka nuna godiya don abin da Jehobah ya yi don ya cece ka?

17 Idan muna godiya don abin da Jehobah da Ɗansa suka yi don su cece mu daga zunubi da mutuwa, za mu nuna ta. (1 Yoh. 5:3) Za mu yi yaƙi da halinmu na yin zunubi. Ba za mu taɓa faɗa wa halin yin zunubi da ganga ba kuma mu yi rayuwa iri biyu da sau da yawa hakan yakan kawo. Bin irin wannan tafarkin zai nuna cewa ba ma ɗaukan fansar da muhimmanci ko kuma ba ma godiya don fansar. Maimakon haka, za mu nuna godiya ta yin ƙoƙari sosai mu kasance da tsabta a gaban Allah. (2 Bit. 3:14) Za mu nuna hakan ta wajen gaya wa mutane game da begenmu na ceto, don su ma su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma begen rai madawwami a nan gaba. (1 Tim. 4:16) Babu shakka, Jehobah da Ɗansa sun cancanci mu ba su kowane lokaci da kuzari da za mu iya bayarwa don mu yabe su! (Mar. 12:28-30) Ka yi tunani! Muna sauraron lokacin da za a warkar da mu gabaki ɗaya daga zunubi. Za mu iya yin rayuwa yadda Allah ya nufa, mu zama kamiltattu har abada, domin abin da Jehobah ya yi don ya cece mu!—Rom. 8:21.

[Ƙarin bayani]

a An ce annobar Spanish influenza ta kama mutane daga kashi ashirin zuwa hamsin da ke duniya a lokacin. Mai yiwuwa cutar ta kashe mutane kashi ɗaya zuwa goma da suka kamu da ita. Akasin haka, ƙwayar cutar Ebola ba ta yawan kama mutane, amma a inda ta kama mutane ta kashe kusan dukan mutane da suka kamu da ita.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa kake bukatar ceto da gaggawa?

• Yaya yadda Yesu ya sadaukar da kansa ya shafe ka?

•Yaya kake ji game da kyautar fansa da Jehobah ya ba da?

• Menene ka motsa za ka yi don ka nuna godiya ga tanadin da Jehobah ya yi don ya cece ka?

[Hotunan da ke shafi na 27]

A Ranar Kafara, babban firist na Isra’ila ya zama rayayyen misali na Almasihu

[Hotunan da ke shafi na 28]

Miƙa ɗansa da Ibrahim ya yi da yardan rai ya koya mana abubuwa da yawa game da sadaukarwa mafi girma da Jehobah ya yi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba