Na Sami Rayuwa Mai Ma’ana
Gaspar Martínez ne ya ba da labarin
A wasu hanyoyi, labari na na yaro ne talaka daga karkara wanda ya samu arziki a birni. Amma za ka ga cewa arziki da na tara ba ainihin abin da nake tsammani ba ne.
NA YI girma a karkara marar ni’ima a tsakanin shekaru 1930 da 1939 a yankin Rioja a arewancin ƙasar Spain. Na bar makaranta sa’ad da nake ɗan shekara goma, amma a lokacin na riga na koyi yadda ake rubutu da karatu. Tare da ’yan’uwana maza da mata guda shida, muna kwana ne a daji muna kiwon tumaki ko kuma yin noma a ɗan ƙaramin filin mu.
Talauci ya sa mu yin tunani cewa kuɗi da dukiyoyi suna da muhimmanci sosai. Muka soma kishin waɗanda suke da abubuwa fiye da mu. Duk da haka, wani bishop ya taɓa cewa “ƙauyenmu ne ya fi yin ibada a cikin wuraren da ke ƙarƙashin shugabancinsa.” Abin da bai sani ba shi ne, a kwana a tashi, mutane da yawa za su bar addinin Katolika.
Neman Abin da Ya Fi Muhimmanci
Na auri Mercedes, wata yarinya daga ƙauyenmu. Ba da daɗewa ba, muka samu ɗa da za mu kula da shi. A shekara ta 1957, mun ƙaura zuwa birnin Logroño da yake kusa, kuma daga baya dukan iyalinmu suka yi hakan. Ba da daɗewa ba na fahimci cewa da yake ba ni da wata fasaha, ba zan samu isasshen kuɗin da zan kula da iyalina ba. Na yi tunani inda zan samu ja-gora. Sai na soma bincike a laburare na birnin, ko da yake ban san ainihin abin da nake nema ba.
Bayan haka, wani ya gaya mini game da shirin rediyo inda ake gabatar da yin nazarin Littafi Mai Tsarki ta hanyar wasiƙa. Ban daɗe da kammala nazarin ba, sai wasu Masu Wa’azi ’yan Farostatan suka ziyarce ni. A ziyarce-ziyarcen da na kai wurin bautarsu, na lura cewa akwai kishi tsakanin manyan da ke rukunin. Ban sake komawa ba, kuma na kammala cewa haka dukan addinai suke.
Idanu Na Sun Buɗe
A shekara ta 1964, wani saurayi mai suna Eugenio ya ziyarci gidanmu. Shi Mashaidin Jehobah ne, addinin da ban taɓa jin sunan sa ba a dā. Amma ina a shirye na tattauna game da Littafi Mai Tsarki. Na ɗauka cewa na san Nassosi sosai. Na amsa masa ta wajen yin amfani da wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da na koya a nazarin da na yi ta hanyar wasiƙa. Ko da yake na yi ƙoƙari na kāre wasu koyarwan Farostatan, amma a zuciya ta ban gaskata da su ba.
Bayan mun yi doguwar tattaunawa sau biyu, na yarda cewa Eugenio gwani ne a yadda yake amfani da Kalmar Allah. Na yi mamakin yadda yake karanta nassosi kuma ya bayyana abin da suke nufi, ko da yake na fi shi ilimi. Eugenio ya nuna mini a cikin Littafi Mai Tsarki cewa muna cikin kwanaki na ƙarshe kuma ba da daɗewa ba Mulkin Allah zai kawo aljanna a duniya. Abin ya burge ni sosai.—Zab. 37:11, 29; Isha. 9:6, 7; Mat. 6:9, 10.
Nan da nan na yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Kusan dukan abin da na koya sabo ne a gare ni, kuma hakan ya motsa zuciyata sosai. Na samu sabon zarafi mai muhimmanci sosai, wanda yake da tamani sosai. Na daina neman aiki. Yanzu na ga cewa yin ƙoƙari na kyautata matsayina ba shi da amfani, kuma kokawa da nake yi don na samu isasshen aiki ba shi muhimmanci. Za a kawar da ciwo da mutuwa balle ma sauran matsaloli.—Isha. 33:24; 35:5, 6; R. Yoh. 21:4.
Nan da nan na soma gaya wa dangina abin da nake koya, cike da himma, na bayyana musu cewa Allah ya yi alkawari zai kawo aljanna a duniya inda ’yan adam masu aminci za su rayu har abada.
Iyalina Sun Karɓi Gaskiyar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki
Ba da daɗewa ba, wajen mu sha biyu muka tsai da shawara mu riƙa yin taro a kowane Lahadi da rana a gidan kawuna don mu tattauna alkawuran Littafi Mai Tsarki. Muna yin sa’o’i biyu ko uku a kowane mako wajen yin hakan. Sa’ad da Eugenio ya ga cewa dangogi na da yawa suna son sanin Littafi Mai Tsarki, sai ya shirya mai da hankali ga kowace iyali.
Ina da wasu dangogi a Durango, wani ƙaramin gari da ke da nisan mil 80 daga namu, kuma babu Shaidu a wajen. Bayan watanni uku, na ɗauki hutu na ’yan kwanaki don na kai musu ziyara domin na bayyana musu sabon imanin da nake bi. A wannan lokacin, wajen mu goma ne muke taruwa a kowace yamma, kuma ina tattaunawa da su har tsakar dare. Su duka sun yi farin cikin saurarawa. Sa’ad da na kammala ziyara ta, na bar musu wasu littattafai da kuma Littafi Mai Tsarki. Bayan hakan, mun ci gaba da tattaunawa.
Sa’ad da Shaidu suka isa garin Durango, inda babu wani da ya taɓa yin wa’azi a dā, sun samu mutane sha takwas suna jira a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Shaidun sun yi farin cikin yin hakan da kowace iyali.
Har wannan lokacin, matata Mercedes ba ta son ta koyi gaskiya, domin ta fi jin tsoron mutum fiye da amincewa da koyarwar Littafi Mai Tsarki. A lokacin, an hana aikin Shaidun Jehobah a ƙasar Spain, saboda haka, tana ganin cewa masu iko za su kori yaranmu biyu daga makaranta kuma dukanmu za mu zama bare. Amma sa’ad da ta ga cewa dukan iyalin suna amincewa da koyarwar Littafi Mai Tsarki, sai ita ma ta ce a yi nazari da ita.
A cikin shekara biyu, mutane arba’in cikin dangogi na suka zama Shaidu kuma aka yi musu baftisma a matsayin alamar keɓe kansu don su bauta wa Allah. Hakika, iyalina suna da irin makasudi da manufa da nake da shi a rayuwa. Ina jin cewa na cim ma abin da ya fi amfani. Allah ya albarkace mu sosai a ruhaniyance.
Na Gamsu Sa’ad da Na Soma Tsufa
A cikin shekaru ashirin, na mai da hankali ga renon ’ya’yanmu maza biyu da kuma taimaka wa ikilisiyarmu. Sa’ad da ni da Mercedes muka ƙaura zuwa Logroño, Shaidu wajen ashirin ne suke cikin wannan birni da ke da mazauna dubu ɗari. Ba da daɗewa ba, na samu hakki da yawa a cikin ikilisiya.
Sa’ad da nake ɗan shekara hamsin da shida, kamfanin da nake aiki suka rufe ma’aikatar ba zato ba tsammani, kuma na rasa aikina. Tun da daɗewa nake da muradin yin hidima na cikakken lokaci, sai na yi amfani da wannan zarafin na zama majagaba. Fanso da nake karɓa kaɗan ne, kuma biyan bukatun rayuwa da wannan ɗan kuɗin ba shi da sauƙi. Mercedes ta taimaka ta wajen yin aikin shara. Da hakan, mun tallafa wa iyalinmu kuma ba mu taɓa rasa abubuwan da muke bukata ba. Har ila ni majagaba ne, kuma a lokaci-lokaci tana hidimar majagaba na ɗan lokaci, kuma tana jin daɗin aikin wa’azi sosai.
A ’yan shekarun da suka shige, Mercedes tana ba da mujallunmu a kai a kai ga wata mata mai suna Merche da ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da take yarinya. Mercha tana jin daɗin karanta littattafanmu, kuma Mercedes ta lura cewa har ila Merche ta san muhimmanci koyarwar Littafi Mai Tsarki. Daga baya, Merche ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma ta soma samun ci gaba sosai. Amma mijinta Vicente, mashayi ne kuma ba ya iya riƙe aikinsa. Saboda haka, ba ya taimaka mata da kuɗi; kuma halinsa na yin maye ya kusan kashe auren su.
Matata ta ba Merche shawara cewa ta gaya wa Vicente ya yi magana da ni, kuma daga baya ya yi hakan. Bayan na ziyarce shi sau da yawa, sai ya yarda na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Vicente ya soma canjawa, ya ƙi shan giya kwanaki da yawa. Bayan hakan sai ya yi mako guda ko fiye da haka bai sha giya ba. Daga baya, sai ya daina shan giya gabaki ɗaya. Ya canja halinsa, kuma iyalinsa ta kasance da haɗin kai. Dukan iyalinsa, tare da matarsa da ’yarsu, suna tallafa wa ƙaramar ikilisiya da ke Tsibirin Canary, inda suke zaune a yanzu.
Tuna Rayuwa Mai Ma’ana da Na Yi
Ko da yake wasu cikin dangogina da suka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki shekaru da suka shige sun mutu yanzu, danginmu ya ci gaba da ƙaruwa, kuma Allah ya albarkace mu sosai. (Mis. 10:22) Na gamsu cewa kusan dukan waɗanda suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki shekaru arba’in da suka shige tare da yaransu da jikokinsu sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci!
A yanzu ina da dangogi masu yawa da Shaidu ne, da yawa cikinsu dattawa ne, bayi masu hidima, da kuma majagaba. Ɗana na fari da matarsa suna hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke Madrid, a ƙasar Spain. Sa’ad da na zama Mashaidi, da akwai misalin ’yan’uwa dubu uku a Spain. A yanzu kuwa akwai fiye da dubu ɗari. Ina jin daɗin hidima na cikakken lokaci, kuma ina godiya ga Allah don rayuwa mai ban al’ajabi da na samu a hidimarsa. Ko da yake ban je makaranta sosai ba, a lokaci-lokaci ina hidima a matsayin mataimakin mai kula da da’ira.
A ’yan shekarun da suka shige, na gano cewa kusan ba kowa a cikin ƙauye da na yi girma. Talauci ya tilasta wa dukan waɗanda suke wajen su bar gonarsu da gidajensu su tafi neman rayuwa mai kyau. Abin farin ciki, da yawa cikin waɗannan da suka ƙaura, har da ni, mun samu dukiyoyi na ruhaniya. Mun koyi cewa rayuwa tana da ma’ana kuma bauta wa Jehobah na kawo farin ciki mai yawa.
[Hoto a shafi na 32]
Kusan dukan iyalin Ɗan’uwa Martínez’ da suke cikin gaskiya