Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 pp. 26-27
  • Wasiƙa Daga Bolivia Farin Ciki da Kuma Samun Bege Duk da Talauci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wasiƙa Daga Bolivia Farin Ciki da Kuma Samun Bege Duk da Talauci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Yaushe Ne Zan Sake Yin Hidimar Majagaba Na Dan Lokaci?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • “Ba a Taɓa Nuna Mini Irin Wannan Ƙaunar Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ki Gaya Masu Cewa Kina Kaunar Su
    Labarai
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 pp. 26-27

Wasiƙa Daga Bolivia Farin Ciki da Kuma Samun Bege Duk da Talauci

YIN hidima a matsayin mai yin wa’azi a ƙasashen waje a ƙasar da ke tasowa, ban taɓa sabawa da ganin talauci da rashin bege ba. Ina so na ga ƙarshen wahala ga kowa. Amma na san cewa Mulkin Allah ne kawai zai iya magance waɗannan matsalolin. Amma, sau da yawa na ga cewa mutanen da suke bin Kalmar Allah suna samun farin ciki duk da yanayi mai wuya. Sabina tana ɗaya daga cikin su.

Shekaru da yawa da suka shige, Sabina, riƙe da ’ya’yanta biyu, tana kallo mijinta ya shiga wata tsohuwar mota don neman aikin da zai ba shi kuɗi sosai a wata ƙasa. Ta yi jiran dawowarsa gida, amma bai sake dawowa ba. Tun lokacin da ya tafi, Sabina tana aiki tuƙuru a kullum don ta yi wa kanta tanadi da kuma ’ya’yanta, Milena da Ghelian.

Na fara haɗuwa da Sabina ne da rana a shagon ’yar’uwarta tana ta sayar da kaya ga waɗanda suke son su saya. Fuskar Sabina ta nuna cewa ta gaje sosai da aiki. Na ce zan yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita da ’ya’yanta. Sai ta ce, “zan so hakan, amma aiki ya yi mini yawa. Amma dai, zan so ’ya’yana su yi nazarin.” Na amince da hakan. Sa’ad da muka ci gaba da nazarin, na fahimci Sabina sosai, kuma na fahimci matsalolinta.

Sabina takan tashi daga barci da ƙarfe huɗu na asuba. Yayin da ’ya’yanta suke barci a cikin daki ɗaya da suke, Sabina za ta ɗaura tukunyar da ta saba yin amfani da ita a kan wuta. Takan dafa naman da za ta saka cikin fanken da take sayarwa don ta samu kuɗin ciyar da iyalinta. Sabina takan shirya kwaɓaɓɓiyar fulawa da za a zuba naman a ciki daddare kafin ta dafa naman.

A hankali, Sabina za ta ɗaura dukan abubuwan da take bukata a ranar a cikin baron haya, wato, rumfa, rasho, murhun gas, teburi, ƙananan kujeru, tukwane, māi, nama da kwaɓaɓɓiyar fulawa da kuma galan-galan na lemun sha da take yi da kanta.

Da ƙarfe shida na safe, Sabina da yaranta biyu sun riga sun yi shirin soma tafiya. Suna rufe ƙofarsu kuma su sa kwaɗo. Babu annashuwa a fuskarsu; babu mai magana ko dariya a cikinsu. Sun mai da hankalinsu ne kawai ga aikin da ke gabansu. A yawancin safiya, daga tagar gidanmu na masu wa’azi a ƙasashen waje, na ga irin waɗannan abubuwan suna faruwa. Hakika, tana ɗaya daga cikin mata masu yawa da suke tashi tun da duku-duku don su sai da abinci da abin sha a kan hanyoyin Bolivia.

Da ƙarfe shida da rabi na safe, yayin da rana ya soma haskaka kan babban dutsen, Sabina da yaranta za su isa inda suke tsayawa. Ba tare da sun ce komi ba, za su sauke kayan da ke cikin baron kuma su kafa wurin dahuwa. Sai ta soma jefa fanken a cikin māi mai zafi. Ƙamshi mai daɗi zai cika iskar safiyar, kuma ya jawo hankalin masu jin yunwa.

“Guda nawa?” Sabina ta tambayi mai sayayya na farko. Ba tare da kallon sama ba, mutumin da barci bai warware daga idonsa ba zai ɗaga yatsu biyu, kuma za ta ba shi soyayyen fanke mai zafi guda biyu. Sai ta karɓi kuɗin. Haka irin wannan cinikayyar za ta ci gaba a ranar. Sa’ad da suka sayar da fanken, sai su kwashe kayansu su tafi gida. Ko da yake ƙafafuwan Sabina suna yi mata ciwo domin aikin safiyar da ta yi, za ta wuce ne zuwa aiki na biyu da take yi a shagon ’yar’uwarta.

Sa’ad da na isa shagon don soma nazarin Littafi Mai Tsarki da yaranta, ta riga ta ajiye benci guda biyu a gefe guda. Tun daga farko, Milena da Ghelian, ’yan shekara 9 da 7, suna ɗokin yin nazarin kowane babi kuma suna yin shiri sosai. A hankali a hankali, waɗannan yaran suka soma gaya mini abin da ke zuciyarsu kuma na zama abokiyarsu. Hakan ya faranta ran Sabina sosai. Ba da daɗewa ba, ta yanke shawara cewa duk da rashin samun lokacinta, ita ma za ta soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.

Yayin da fahimin Sabina ya ƙaru, haka ma ƙaunar da take yi wa Jehobah Allah. Ta soma shaida wani abin da ba ta taɓa shaida ba, farin ciki! Wannan matar da a dā a gajiye take kuma ba ta farin ciki a yanzu ta fita dabam. A yanzu ta miƙe tsaye, tana kallon mutane, kuma fuskarta ya cika da annuri. “Sabina tana murmushi a kowane lokaci,” in ji ’yar’uwarta. “A dā ba ta yin hakan.” Wasu kuma sun ga canji mai girma a Sabina da yaranta. Ta samu biyan bukatan son sanin Allah da manufofinsa.

Sabina tana jin daɗin nazarinta, amma aiki tuƙuru da take yi ya hana ta halartan taron Kirista. Daga bisani, ta yi na’am da gayyatar da na yi mata na ziyartar Majami’ar Mulki. Bayan haka, ba ta daina zuwa ba. A cikin ikilisiya, Sabina ta samu abokan gaskiya. Ta kuma ga cewa Jehobah yana yin tanadi ga waɗanda suke ƙaunarsa kuma suka yi sadaukarwa don su bauta masa.—Luka 12:22-24; 1 Timotawus 6:8.

Sabina tana ƙaunar abin da take koya, kuma tana son ta gaya wa wasu. Amma ta ce, “Tsoro yana kama ni a duk lokacin da na yi tunanin yi wa mutane wa’azi.” Ta yi tunani, ‘Yaya ni, mace marar ilimi, matsoraciya za ta iya yi wa wani wa’azi?’ Duk da haka, alherin da aka nuna mata da kuma ci gaban da ta shaida a rayuwarta sun motsa ta ta ɗauki wannan mataki mai muhimmanci. Kuma ta fahimci cewa yaranta suna bin misalinta. Saboda haka, ta soma gaya wa mutane bishara. Su ma yaranta suka bi sawunta.

A yau, Sabina ba wata talakar mace ba ce marar farin ciki da take shan wahala a kullum. Ko da yake ba ta da kuɗi sosai. Amma yadda take ɗaukan rayuwa ya canja. A yanzu, a matsayinta na Kirista da ya yi baftisma, tana gaya wa wasu bisharar Mulkin Allah, wadda ita ce kawai za ta magance yanayin talauci da tsoro a duniya har abada.—Matta 6:10.

Ƙarfe biyar na safiya ta yi, kuma Sabina tana shirye ta fita daga ɗaki guda da take kwana. Amma wannan safiyar ba wai za ta je sayar da fanke ba ne. Za ta sadu da rukunin ’yan’uwanta Kiristoci don yin wa’azi a kan titi. Ba da wasu daga cikin lokacinta don taimaka wa wasu ya sa ta sami ƙarin farin ciki a rayuwarta. Tana rufe ƙofarta, cike da murmushi kuma, ta tafi kan titi. Maimakon ta tura baro, tana ɗaukan ƙatuwar jaka. A cikin jakar akwai Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki da za ta yi amfani da su ta yaɗa bege ga wasu. Yin murmushi da gaba gaɗi, Sabina ta ce, “Ban taɓa mafarkin cewa zan gaya wa wasu game da Littafi Mai Tsarki ba.” Ta daɗa cewa, “Ina ƙaunar hakan!”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba