Ka Kusaci Allah
Ya San Damuwarmu
“JUYAYI shi ne ina jin zafin ciwonka.” Da waɗannan kalaman ne wani tsoho Mashaidin Jehobah da ke wa’azi a ƙasar waje ya kwatanta wannan hali mai tamani. Jehobah Allah shi ne ya fi nuna juyayi. Yana damuwa sosai domin wahalar da mutanensa suke sha. Ta yaya za mu iya sanin cewa hakan gaskiya ne? Juyayin da Jehobah yake nunawa ya bayyana sarai a kalamai da halayen Yesu sa’ad da yake duniya. (Yohanna 5:19) Alal misali, yi la’akari da abin da ya faru a Yohanna 11:33-35.
Yesu ya tafi ƙauyen su Li’azaru sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu. Yayyen Li’azaru mata, Maryamu da Martha suna cike da baƙin ciki. Yesu yana ƙaunar wannan iyalin sosai. (Yohanna 11:5) To, me zai yi? Labarin ya ce: “Da Yesu ya ga [Maryamu] tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya. Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.” Sai Yesu ya yi hawaye.” (Yohanna 11:33-35, Littafi Mai Tsarki) Me ya sa Yesu ya yi kuka? Hakika, abokinsa Li’azaru da yake ƙauna ya mutu, amma Yesu yana gab da daidaita al’amuran ta wajen ta da shi daga matattu. (Yohanna 11:41-44) Da wani abin kuma da ya taɓa zuciyar Yesu?
Ka sake duba waɗannan kalaman da aka yi ƙaulinsu a baya. Za ka ga cewa sa’ad da Yesu ya ga Maryamu da waɗanda suke tare da ita suna kuka, “ya nisa a ransa” kuma “ya yi juyayi gaya.” Kalamai na ainihi da aka yi amfani da su a nan suna nufin motsin rai sosai.a Abin da Yesu ya gani ya shafe shi sosai. Hawayen da suka cika idonsa sun nuna yadda abin ya shafe shi sosai. Babu shakka, wahalar wasu ta taɓa zuciyar Yesu. Ka taɓa zubar da hawaye domin wani da kake ƙauna yana kuka?—Romawa 12:15.
Juyayin da Yesu ya nuna ya bayyana mana halaye da hanyoyin Ubansa, Jehobah. Ka tuna cewa Yesu ya nuna ainihin halayen Ubansa wanda hakan ya sa ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Saboda haka, sa’ad da muka karanta cewa “Yesu ya yi hawaye,” mu tabbata cewa Jehobah ya damu da wahalar da masu bauta masa suke sha. Hakika, wasu marubutan Littafi Mai Tsarki sun tabbatar da wannan gaskiyar. (Ishaya 63:9; Zechariah 2:8) Jehobah Allah ne mai kula!
Juyayi yana jawo mu kusa da mutane. Sa’ad da muka yi sanyin gwiwa ko kuwa muna baƙin ciki, muna kusantar mutanen da za su iya fahimtar yanayinmu kuma su nuna juyayi. Mun fi kusantar Jehobah, Allah mai nuna juyayi, wanda wahalarmu take shafansa kuma wanda ya san dalilin da ya sa muke zubar da hawaye!—Zabura 56:8.
[Hasiya]
a Kalmar Helenanci da aka fassara “yi hawaye” a yawancin lokaci tana nufin “yin kuka ciki-ciki,” ita kuwa kalmar da aka yi amfani da ita wajen kwatanta kukan da Maryamu da wasu suka yi wataƙila tana nufin “yin kuka sosai.”