Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Obadiah, Yunana, da Mikah
“RU’YAR Obadiah.” (Obadiah 1) Waɗannan su ne kalaman farko a cikin littafin Obadiah. Annabin bai faɗi kome ba game da kansa ba, ya ambata sunansa ne kawai a cikin littafin da ya rubuta a shekara ta 607 K.Z. A cikin littafin da aka kammala fiye da ƙarnuka biyu kafin Obadiah ya rubuta nasa, annabi Yunana ya rubuta abin da ya fuskanta a hidimarsa. Shekaru 60 da Mikah ya yi yana annabci sun faru ne a lokacin annabcin Obadiah da Yunana, daga shekara ta 777 K.Z. zuwa 717 K.Z. Abin da Mikah ya ambata game da kansa kawai shi ne, shi ɗan “[ƙauyen] Bamorashti” ne kuma ya sami kalmar Jehobah a “kwanakin Jotham, da Ahaz, da Hezekiah, sarakunan Yahuda.” (Mikah 1:1) Irin kwatancen da annabin ya yi amfani da su don ya nanata saƙonsa sun nuna cewa ya saba da zaman ƙauye.
‘ZA A DATSE EDOM HAR ABADA’
(Obadiah 1-12)
Obadiah ya ce game da Edom: “Saboda wulakanci da aka yi ma ɗan’uwanki Yaƙub, kunya za ta rufe ki, za a datse ki har abada.” Annabin ya tuna muguntar da Edomawa suka yi wa ’ya’yan Yakubu, wato, Isra’ilawa. A lokacin da Babiloniyawa suka halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z., Edomawa sun “tsaya a raɓe waje ɗaya” suka haɗa kai da ‘baƙin’ da suka kai wa Urushalima hari.—Obadiah 10, 11.
Akasarin haka, an shirya cewa ’yan gidan Yaƙub za su komo. Obadiah ya annabta: “Cikin dutsen Sihiyona za a iske waɗanda su ke tsira, za ya zama mai-tsarki.”—Obadiah 17.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
5-8—Mecece ma’anar kwatancin halakar Edom da zuwan masu sata da dare da kuma masu tsinan anab? Idan ɓarayi ne suka zo cikin Edom, za su ɗauki abin da suke so ne kawai. Idan masu tsinan anab ne suka zo, za su bar wasu amfanin gona don a sami na kala. A lokacin da aka halaka Edom, “waɗanda ke zaman lafiya da [ita],” wato, abokanta Babiloniyawa za su nemi duka dukiyoyinta kuma su sace su.—Irmiya 49:9, 10.
10—Ta Yaya ne aka ‘datse Edom har abada’? Kamar yadda aka annabta, ƙasar Edom wadda take da gwamnati da mutane da suke zaune a wani sashe na duniya sun halaka gaba ɗaya. Nabonidus Sarkin Babila ne ya ci ƙasar Edom a tsakiyar ƙarni na shida K.Z. A ƙarni na huɗu K.Z., ’ya’yan Nebaioth ne suka zauna a yankin Edom, hakan ya sa Edomawa suka koma da zama a kudancin Yahudiya, a Negeb wadda daga baya ake kira Idumiya. Bayan da Romawa suka halaka Urushalima a shekara ta 70 A.Z., Edomawa ba su sake wanzuwa ba.
Darussa Dominmu:
3, 4. Domin sun zauna a wurin da ke da manyan duwatsu da kuma kwazazzabo, wanda ya sa maƙiyansu ba za su iya zuwa su yaƙe su ba, hakan ya sa Edomawa tunanin cewa sun sami kāriya. Amma ba za a iya guje wa hukuncin Jehobah ba.
8, 9, 15. Hikima da ikon ’yan adam ba za su kāre mu a “ranar Ubangiji” ba.—Irmiya 49:7, 22.
12-14. Edomawa sun zama darassi ga waɗanda suke farin ciki saboda wahalar da bayin Allah suke sha. Jehobah ba ya ɗaukan wahalar da mutanensa da ake yi da wasa ba. Jehobah yana ɗaukan wahalar da mutanensa suke sha da muhimmanci or batu ne mai tsanani?
17-20. Annabcin komowar ’ya’yan Yaƙub ya soma cika a lokacin da waɗanda suka rage a Babila suka koma Urushalima a shekara ta 537 K.Z. Maganar Jehobah tana cika a kowane lokaci. Muna da tabbaci mai ƙarfi game da alkawuransa.
ZA A “KAƁANTADDA NINEVEH”
(Yunana 1:1–4:11)
Maimakon ya yi biyayya ga umurnin Allah ya je ‘Nineveh, babban birnin nan, ya tada murya’ ya sanar da saƙon hukunci, Yunana ya gudu zuwa wani wuri dabam. Jehobah ya gyara tunanin Yunana kuma ya sake aikansa zuwa babban birnin Assuriya sa’ad da ya aika “babban iska cikin teku” kuma ya yi amfani da “babban kifi.”—Yunana 1:2, 4,17; 3:1, 2.
Yunana ya shiga Nineveh kuma ya soma ba da saƙo na kai tsaye: “Sauran kwana arba’in tukuna, kāna a kaɓantadda Nineveh.” (Yunana 3:4) Sakamakon wa’azin da ya yi ya sa Yunana ya yi “fushi” sosai. Jehobah ya yi amfani da ‘zurma’ ya koya wa Yunana darasi game da jin ƙai.—Yunana 4:1, 6.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
3:3—Da gaske ne faɗin Nineveh ya kai “tafiyar yini uku”? E. A zamanin dā, an yarda cewa Nineveh ta haɗa da wasu unguwanni tun daga Khorsabad a arewa zuwa Nimrud a kudu. Dukan waɗannan unguwanni da ke ƙarƙashin Nineveh sun kasance birni ɗaya mai faɗin mil 60 ta ko wane gefe.
3:4—Yunana ya koyi yaren Assuriya don ya yi wa ’ya’yan Nineveh wa’azi ne? Wataƙila Yunana ya iya yaren Assuriyawa a dā ko kuma ya sami hikimar yin yaren ta wurin mu’ujiza. Wataƙila ya gabatar da saƙonsa ne a Ibrananci, kuma wani yana fassarawa. Idan haka ne, kalamansa za su jawo hankalin mutane ga saƙonsa sosai.
Darussa Dominmu:
1:1-3. Idan da sane mutum ya shirya wasu ayyuka da zai yi don kada ya yi wa’azin Mulki da almajirantarwa yadda ya kamata, hakan yana nuna irin mugun ra’ayin mutumin. Duk wanda ya yi hakan yana guje wa aikin Allah ne kamar yadda Yunana ya yi.
1:1, 2; 3:10. Alherin Jehobah ba ga al’umma ɗaya ko yare ko kuma mutane masu muhimmanci kawai ba ne. “Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane; Jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.”—Zabura 145:9.
1:17; 2:10. Kwana ukun da Yunana ya yi a cikin babban kifi, a annabce yana nuni ne ga mutuwar Yesu da tashinsa daga matattu.—Matta 12:39, 40; 16:21.
1:17; 2:10; 4:6. Jehobah ya ceci Yunana daga teku. Allah kuma ya “shirya masa zurman, ya sa kuma ya tsiro har ya rufe Yunana, domin ya zama masa inuwa bisa kansa, da za ya cece shi daga cikin wahalarsa.” Masu bauta wa Jehobah a yau za su iya dogara ga Allahnsu, da kuma jin ƙansa, don ya kāre su kuma ya cece su.—Zabura 13:5; 40:11.
2:1, 2, 9, 10. Jehobah yana jin addu’ar bayinsa kuma yana saurarar roƙonsu.—Zabura 120:1; 130:1, 2.
3:8, 10; LMT. Allah na gaskiya ya “dakatar da nufinsa,” ya canja ra’ayinsa game da masifar da ya ce zai faru da su, kuma “bai hallaka su ba.” Me ya sa? Saboda ’ya’yan Nineveh sun “bar mugayen ayyukansu.” Hakazalika, a yau Jehobah zai iya canja hukuncinsa idan mai zunubi ya nuna cewa ya tuba da gaske.
4:1-4. Babu mutumin da zai iya sa Allah ya sauƙaƙa jin ƙansa. Mu mai da hankali kada mu ji haushin yadda Jehobah yake nuna jin ƙai.
4:11. Jehobah ya sa a ci gaba da yin wa’azin Mulki a dukan duniya ne don haƙurin da yake da shi, saboda kamar yadda ya yi wa mutane 120,000 a ƙasar Nineveh yana jin tausayin “waɗanda ba su iya rarrabe hannun damansu da hagu ba.” Ya kamata mu ma mu ji tausayin mutanen da suke zama a yankinmu mu yi himma a wa’azin Mulki, da kuma almajirantarwa.—2 Bitrus 3:9.
‘ZA A YAWAITA SANƘONSU’
(Mikah 1:1–7:20)
Mikah ya fallasa zunubin Isra’ila da Yahuda, ya annabta halakar biranen, kuma ya yi alkawari game da komowa. Samariya za ta zama “tulin gona.” Isra’ila da Yahuda sun dace su sami ‘sanƙo,’ ko kuma su ji kunya saboda bautar gunki da suke yi. Domin an kai su bauta, sanƙonsu zai yalwata “kamar ungulu.” Jehobah ya yi alkawari: ‘Hakika zan tattara Yakubu.’ (Mikah 1:6, 16; 2:12; LMT) Urushalima “za ta zama tuddai” saboda shugabanni masu rashawa da kuma annabawa masu laifi. Amma Jehobah zai “tattara [mutanensa].” Wanda zai “zama mai-mulki cikin Isra’ila,” zai fito daga “Bai’talahmi Ephrathah.”—Mikah 3:12; 4:12; 5:2.
Jehobah bai nuna wa Isra’ila adalci ba ne? Bukatunsa suna da wuya ne? A’a. Abin da Jehobah yake bukata daga masu bauta masa shi ne su yi ‘aikin gaskiya, da son jin ƙai, su yi tafiya da tawali’u’ tare da Allahnsu. (Mikah 6:8) Waɗanda suke zama a zamanin Mikah sun lalace kuma “mafi kyau a cikinsu kamar ƙaya ya ke,” ‘mafi adalci a cikinsu ya fi shimgen ƙaya mugunta,’ suna azabtar da duk wanda ya yi kusa da su. Amma annabin ya yi tambaya: “Wanene Allah makwatancinka?” Allah zai gafarta wa mutanensa kuma ‘zai zubar da zunubansu duka cikin zurfin teku.’—Mikah 7:14, 18, 19.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:12—Yaushe ne annabci na “tattara ringin Isra’ila” ya cika? Na farko ya cika a shekara ta 537 K.Z., sa’ad da Yahudawa da suka rage a Babila suka koma ƙasarsu. A zamanin nan, annabcin ya cika a kan “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) Tun a shekara ta 1919, an tattara shafaffun Kiristoci “kamar garke cikin tsakiyar makiyayansu.” Sun cika da “yawan taro” saboda “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” sun haɗa kai da su, musamman tun a shekara ta 1935. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Suna himma tare wajen faɗaɗa bauta ta gaskiya.
4:1-4—A “kwanaki na ƙarshe” ta yaya Jehobah yake ‘raba shari’a tsakanin ƙabilai dayawa, kuma ya raba tsakanin manyan al’ummai’? Furcin nan “ƙabilai dayawa” da kuma “manyan al’ummai” ba ya nufin al’ummai ko kuma masu mulki. Amma, yana nufin mutane da suka fito daga dukan al’ummai kuma suka zama Shaidun Jehobah. Jehobah yana yin shari’a kuma yana daidaita al’amura game da dangantakarsu da shi.
Darussa Dominmu:
1:6, 9; 3:12; 5:2. A zamanin Mikah, Assuriyawa sun halaka Samariya a shekara ta 740 K.Z. (2 Sarakuna 17:5, 6) Assuriyawa sun zo Urushalima a lokacin sarautar Hezekiya. (2 Sarakuna 18:13) Babiloniyawa sun ƙone Urushalima a shekara ta 607 K.Z. (2 Labarbaru 36:19) Kamar yadda aka annabta, an haifi Almasihu a “Bai’talahmi Ephrathah.” (Matta 2:3-6) Annabcin Jehobah yana cika a kowane lokaci.
2:1, 2. Za mu fuskanci haɗari idan muka nuna muna bauta wa Allah amma mun sa neman arziki a gaba maimakon “mulkinsa, da adalcinsa.”—Matta 6:33; 1 Timothawus 6:9, 10.
3:1-3, 5. Jehobah yana son waɗanda suke shugabanci a tsakanin mutanensa su nuna adalci.
3:4. Idan muna son Jehobah ya amsa addu’o’inmu, dole ne mu guje wa yin zunubi.
3:8. Za mu iya cika aikin da aka ba mu na shelar bishara, wanda ya ƙunshi saƙon hukunci ne kawai idan muka sami ƙarfafa daga ruhu mai tsarki na Jehobah.
5:5. Annabcin Almasihu ya ba mu tabbaci cewa sa’ad da mutanen Allah suka fuskanci hari daga wurin maƙiyansu, zai zaɓi “maƙiyaya bakwai” [wanda ke wakiltan cikakke] da kuma “shugabannai takwas,” wato, ƙwararrun maza su yi shugabanci a tsakanin mutanen Jehobah.
5:7, 8. Ga yawancin mutane, shafaffun Kiristoci a yau suna kama da “rāɓa daga wajen Ubangiji” wato, albarka daga wajen Allah. Haka yake saboda yana amfani da shafaffu a wurin shelar saƙon Mulki. “Waɗansu tumaki” suna taimaka wa mutane su sami wartsakewa ta ruhaniya ta wurin haɗa kai da shafaffu a yin wa’azi. (Yohanna 10:16) Gata ne a saka hannu a wannan aikin da zai wartsakar da mutane!
6:3, 4. Muna bukatar mu yi koyi da Jehobah Allah kuma mu nuna alheri da tausayi ga waɗanda yake da wuya a yi sha’ani da su ko kuma waɗanda suka yi sanyin gwiwa a ruhaniya.
7:7. Kada mu yi kasala sa’ad da muke magance matsaloli a ƙarshen wannan mugun zamani. Maimakon haka, ya kamata mu “jira Allah” kamar yadda Mikah ya yi.
7:18, 19. Mu gafarta wa waɗanda suka yi mana laifi kamar yadda Jehobah yake yafe mana laifofin mu.
Ka Ci Gaba da Yin ‘Biyayya da Sunan Jehobah’
Waɗanda suke yaƙi da Allah da mutanensa, ‘za a datse su har abada.’ (Obadiah 10) Duk da haka, idan muka yi biyayya ga umurnin Allah kuma muka “juya ga barin mugun tafarki,” Jehobah ba zai halaka mu ba. (Yunana 3:10) “A cikin kwanaki na ƙarshe,” ana ɗaukaka bauta ta gaskiya fiye da addinin ƙarya kuma masu biyayya suna ta jerin gwano zuwa bauta ta gaskiya. (Mikah 4:1; 2 Timothawus 3:1) Bari mu ƙudurta cewa za mu ci gaba da yin “biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”—Mikah 4:5.
Littafin Obadiah da Yunana da kuma Mikah sun koya mana darussa masu muhimmanci! Ko da yake an rubuta su fiye da shekaru 2,500 da suka wuce, saƙonsu “mai-rai ce, mai-aikatawa,” a yau.—Ibraniyawa 4:12.
[Hoto a shafi na 8]
Obadiah ya annabta: “Za a datse [Edom] har abada”
[Hoto a shafi na 10]
Ya kamata mu “jira Allah” kamar yadda Mikah ya yi
[Hoto a shafi na 11]
Aikin wa’azi gata ne da ya kamata mu daraja