Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 8/1 pp. 13-17
  • Ka Yi Sauraron Ranar Jehobah Da Jimiri

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Sauraron Ranar Jehobah Da Jimiri
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Rashin Lafiya Bai Hana Su Ba
  • Jure Baƙin Ciki
  • Bi da Gwaji Iri-Iri
  • Za Ka Iya Jimrewa!
  • ‘Bari Hakuri Ya Cika Aikinsa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Jimre Kamar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Kana Bukatar Jimiri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 8/1 pp. 13-17

Ka Yi Sauraron Ranar Jehobah Da Jimiri

“Sai ku ƙara bada ƙoƙari, cikin bangaskiyarku kuma ku kawo . . . [jimiri].”—2 BITRUS 1:5, 6.

1, 2. Menene jimiri, kuma me ya sa Kiristoci suke bukatarsa?

BABBAR ranar Jehobah ta kusa sosai. (Joel 1:15; Zephaniah 1:14) Mu Kiristoci da muka ƙudurta riƙe amincinmu ga Allah, cikin ɗoki muna jiran wannan lokaci sa’ad da za a ɗaukaka ikon mallakar Jehobah. Amma a yanzu, muna fuskantar ƙiyayya, taƙaici, tsanani, da kuma mutuwa domin imaninmu. (Matta 5:10-12; 10:22; Ru’ya ta Yohanna 2:10) Hakan na bukatar jimiri, wato, iya jimre wahala. Manzo Bitrus ya aririce mu: “Sai ku ƙara bada ƙoƙari, cikin bangaskiyarku kuma ku kawo . . . [jimiri].” (2 Bitrus 1:5, 6) Muna bukatar jimiri, domin Yesu ya ce: “Wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.”—Matta 24:13.

2 Muna yin rashin lafiya, makoki, kuma muna fuskantar gwaji iri-iri. Shaiɗan zai yi farin ciki sosai idan muka yi rashin bangaskiyarmu! (Luka 22:31, 32) Da taimakon Jehobah, muna iya jimre gwaji iri-iri. (1 Bitrus 5:6-11) Yi la’akari da wasu labaran gaskiya da suka tabbatar da cewa muna iya jiran ranar Jehobah da jimiri da kuma cikakkiyar bangaskiya.

Rashin Lafiya Bai Hana Su Ba

3, 4. Ka ba da misalin da ya nuna cewa muna iya bauta wa Jehobah cikin aminci duk da rashin lafiya?

3 Allah ba ya warkar da mu ta hanyar mu’ujiza, amma yana ba mu ƙarfin jimre rashin lafiya. (Zabura 41:1-3) “Tun lokacin da na yi wayo,” in ji Sharon, “ba na rabuwa da keken guragu. Tun lokacin da aka haife ni, wata irin cuta da ke shafan ƙwaƙwalwa kuma ta gurguntar da mutum ta hana ni sanin farin cikin yaranta.” Koyan game da Jehobah da kuma alkawuransa na koshin lafiya ya sa Sharon ta kasance da bege. Ko da yake tana yin magana da kuma tafiya da kyar, tana jin daɗin yin hidimar Kirista. A shekaru 15 da suka shige, ta ce: “Ko da yake lafiyar jikina na iya ci gaba da raunana, amma aminci na da kuma dangantaka ta da Allah sune rayuwata. Ina farin cikin kasancewa cikin mutanen Jehobah da kuma samun taimako marar ƙarewa!”

4 Manzo Bulus ya aririci Kiristoci a Tassalunika su “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1 Tassalunikawa 5:14) Abubuwa kamar su fid da rai na iya jawo baƙin ciki. A shekara ta 1993, Sharon ta rubuta: “Tun da yake ina jin kamar wadda ta gaza, . . . na yi mugun baƙin ciki na shekaru uku da rabi. . . . Amma na sami ƙarfafa da shawara daga dattawa. . . . Ta hanyar Hasumiyar Tsaro, Jehobah ya ƙara ba da haske game da mugun baƙin ciki. Hakika, yana kula da mutanensa kuma ya san yadda muke ji.” (1 Bitrus 5:6, 7) Har yanzu Sharon tana bauta wa Allah cikin aminci yayin da take jiran babbar ranar Jehobah.

5. Wane tabbaci ne ya nuna cewa Kiristoci za su iya jimre mugun damuwa?

5 Wasu Kiristoci suna mugun damuwa domin abubuwan da suka gani a dā. Harley ya ga yadda aka yi Yaƙin Duniya na biyu kuma yana yin mafarki game da yaƙin. A lokacin da yake barci, sai ya fashe da ihu yana cewa: “Ka mai da hankali! Ka lura!” Da ya farka, sai ya ga jikinsa cike da jiɓin razana. Amma, da shigewar lokaci ya biɗi rayuwa ta ibada kuma yawan yin irin wannan mugun mafarkin ya ragu.

6. Ta yaya ne wani Kirista ya fuskanci matsalar da ta shafi motsin rai?

6 Yin aikin wa’azin daga kofa zuwa kofa ya yi wa wani Kirista mai taɓin hankali wuya. Ya nace wa wannan aikin, domin ya fahimci cewa hidimar za ta sa ya samu rai da kuma waɗanda suka saurare shi. (1 Timothawus 4:16) A wasu lokatai ba zai iya danna ƙararrawar gidan ba, amma ya ce: “Bayan wani ɗan lokaci na kan kwantar da hankalina, in je kofa ta gaba, kuma in sake gwadawa. Ta wajen ci gaba a hidima, na kasance da lafiya ta ruhaniya.” Halartar taro ya zame masa ƙalubale, amma wannan ɗan’uwan ya ɗauki tarayya ta ruhaniya da tamani. Saboda haka, yana iya ƙoƙarinsa ya kasance a taron.—Ibraniyawa 10:24, 25.

7. Ko da yake wasu suna jin tsoron yin magana a gaban mutane ko su halarci taro, ta yaya suke nuna jimiri?

7 Wasu Kiristoci suna mugun jin tsoron wasu yanayi ko abubuwa. Alal misali, suna iya jin tsoron yin magana a gaban mutane ko halartar taro. Ka yi tunanin yadda zai yi masu wuya su yi kalami a taron Kirista ko kuwa su ba da jawabi a Makarantar Hidima ta Allah! Duk da haka, suna jimrewa, kuma kasancewarsu a taro da kalaminsu yana ƙarfafa mu.

8. Menene ya fi muhimmanci sa’ad da ake jimre da matsalolin da suka shafi motsin rai?

8 Ƙarin hutu da barci na iya taimaka wa mutum ya jimre da matsalar motsin rai. Ana kuma iya neman taimakon likita. Mafi muhimmanci shi ne, dogara ga Allah ta hanyar addu’a. “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka,” in ji Zabura 55:22. “Ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.” Saboda haka, ko ta yaya, “ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka.”—Misalai 3:5, 6.

Jure Baƙin Ciki

9-11. (a) Menene zai iya taimaka mana mu jimre baƙin ciki sa’ad da wani ƙaunatacce ya mutu? (b) Ta yaya ne misalin Hannatu zai iya taimaka mana mu jimre baƙin ciki?

9 Sa’ad da wani ya mutu a cikin iyali, irin wannan rashin na iya jawo mugun baƙin ciki. Ibrahim ya yi kuka saboda mutuwar matarsa da yake ƙauna, Saratu. (Farawa 23:2) Har ma Yesu wanda kamiltacce ne “ya yi kuka” sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu. (Yohanna 11:35) Saboda haka, dole ne ka yi baƙin ciki sa’ad da mutuwa ta ɗauke wani da kake ƙauna. Amma, Kiristoci sun san cewa za a yi tashin matattu. (Ayukan Manzanni 24:15) Saboda haka, ba sa “baƙinciki, kamar sauran mutane, waɗanda ba su da bege.”—1 Tassalunikawa 4:13.

10 Ta yaya za mu iya jure irin wannan baƙin ciki? Wataƙila wannan misalin zai taimaka. Ba ma ci gaba da yin baƙin ciki sa’ad da wani abokinmu ya yi tafiya domin mun san cewa zai dawo. Idan muka kasance da irin wannan ra’ayin sa’ad da wani amintaccen Kirista ya mutu, hakan zai iya rage baƙin cikinmu domin mun san cewa za a ta da shi daga matattu.—Mai Wa’azi 7:1.

11 Cikakkiyar dogara da “Allah na dukan ta’aziyya” zai taimaka mana mu jimre baƙin ciki. (2 Korinthiyawa 1:3, 4) Wani abu kuma da zai taimaka mana shi ne tuna abin da gwauruwa ta ƙarni na farko, Hannatu ta yi. Hannatu ta zama gwauruwa bayan shekaru bakwai da yin aure. Amma har a shekararta ta 84, ta ci gaba da yin tsarkakkiyar hidima ga Jehobah a haikali. (Luka 2:36-38) Irin wannan rayuwar da ke cike da ibada ya taimaka mata ta jure baƙin ciki da kaɗaici. Saka hannu a ayyukan Kirista a kowane lokaci, har da aikin wa’azin Mulki, za su iya taimaka mana mu jure baƙin ciki.

Bi da Gwaji Iri-Iri

12. Waɗanne gwaji ne wasu Kiristoci suka jimre da ya shafi rayuwar iyali?

12 Wasu Kiristoci suna jimre gwajin da suka shafi rayuwar iyali. Alal misali, idan aboki ko abokiyar aure ya ko ta yi zina, hakan zai shafi iyalin sosai! Saboda gigita da baƙin ciki, aboki ko abokiyar auren da aka ci amanarsa yana ko tana iya kasa yin barci kuma ya ko ta ci gaba da yin kuka sosai. Yin ɗan ƙaramin aiki na iya zama abu mai wuya wanda hakan zai sa a yi kurakurai ko wani haɗari ya faru. Abokin auren da aka ci amanarsa zai ko za ta kasa cin abinci, zai ko za ta rama, kuma yana ko tana iya ci gaba da damuwa. Zai iya yi masa ko mata wuya ya ko ta yi ayyukan Kirista. Kuma hakan zai shafi yaransu sosai!

13, 14. (a) Wane ƙarfafa ne ka samu daga addu’ar Sulemanu a keɓewar haikali? (b) Me ya sa muke yin addu’a don samun ruhu mai tsarki?

13 Sa’ad da muka fuskanci irin waɗannan gwaje-gwajen, Jehobah yana yin tanadin taimakon da muke bukata. (Zabura 94:19) Mun san cewa Allah yana jin addu’ar mutanensa ta wajen addu’ar da Sarki Sulemanu ya yi a keɓewar haikalin Jehobah. Sulemanu ya yi addu’a: “Ko wace addu’a da roƙo da aka yi, a bakin kowane mutum, ko a bakin dukan jama’arka Isra’ila, kowa yana sane da ciwutar zuciyar kansa, ya miƙa hannunwansa zuwa gidan nan: sai ka ji a cikin sama mazauninka, ka yi gafara, ka aika, ka sāka ma kowane mutum gwalgwadon dukan aikinsa, kai wanda ka san zuciyatasa; (gama kai kaɗai ka san zuciyar dukan yan adam:) domin su ji tsoronka dukan kwanakin da su ke zaune a cikin ƙasa wadda ka ba ubanninmu.”—1 Sarakuna 8:38-40.

14 Za mu sami taimako sosai idan muka ci gaba da yin addu’a don samun ruhu mai tsarki. (Matta 7:7-11) Ɗiyar ruhu ta ƙunshi halaye kamar su farin ciki da salama. (Galatiyawa 5:22, 23) Muna samun sauƙi sosai sa’ad da Ubanmu na sama ya amsa addu’o’inmu, wato, sa’ad da aka yi farin ciki maimakon baƙin ciki, kuma sa’ad da aka sami kwanciyar hankali maimakon azaba!

15. Waɗanne nassosi ne za su taimaka mana mu kawar da damuwarmu?

15 Muna iya yin alhini sa’ad da muke jimre yawan damuwa. Amma muna iya kawar da wasu daga cikin waɗannan damuwar idan muka tuna waɗannan kalamai na Yesu: “Kada ku yi alhini saboda ranku, abin da za ku ci, ko kuwa abin da za ku sha; ko saboda jikinku, abin da za ku yafa. . . . Amma ku fara biɗan mulkinsa, da [adalcin Allah]; waɗannan abu duka fa za a ƙara muku su.” (Matta 6:25, 33, 34) Manzo Bitrus ya aririce mu mu ‘zuba dukan alhininmu a bisa Allah, domin yana kula da mu.’ (1 Bitrus 5:6, 7) Ya dace mu yi iya ƙoƙarinmu don magance matsala. Yawan damuwa game da matsalar ba zai taimaka mana ba, amma addu’a za ta taimaka mana. Mai zabura ya raira: “Ka danƙa ma Ubangiji tafarkinka; ka dogara gareshi, shi kuma za ya tabbatadda shi.”—Zabura 37:5.

16, 17. (a) Me ya sa ba za mu iya daina damuwa gaba ɗaya ba? (b) Menene za mu shaida idan muka bi Filibbiyawa 4:6, 7?

16 Bulus ya rubuta: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filibbiyawa 4:6, 7) ’Yan adam ajizai ba za su daina yin alhini gaba ɗaya ba. (Romawa 5:12) Bahittiyawa matan Isuwa sun “zama abin ɓāta rai ga” Ishaƙu da Rifkatu iyayen Isuwa masu tsoron Allah. (Farawa 26:34, 35) Ƙila rashin lafiya ya jawo damuwa ga Kiristoci kamar Timothawus da Tarofimas. (1 Timothawus 5:23; 2 Timothawus 4:20) Bulus ya damu domin ’yan’uwa masu bi. (2 Korinthiyawa 11:28) Amma “Mai-jin addu’a” a kowane lokaci yana taimakon waɗanda suke ƙaunarsa.—Zabura 65:2.

17 Yayin da muke jiran ranar Jehobah, muna samun taimako da ƙarfafa daga “Allah kuwa na salama.” (Filibbiyawa 4:9) Jehobah yana ‘cike da juyayi, da alheri’ shi ‘nagari ne, mai hanzarin gafartawa,’ kuma “ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Fitowa 34:6; Zabura 86:5; 103:13, 14) Saboda haka, bari mu ‘bar roƙe roƙenmu su sanu ga Allah,’ domin hakan zai sa mu sami “salama kuwa ta Allah,” wato, kwanciyar hankali da ta fi ƙarfin fahimtar mutane.

18. Kamar yadda yake a Ayuba 42:5, ta yaya za a iya ‘ganin’ Allah?

18 Sa’ad da aka amsa addu’o’inmu, mun san cewa Allah yana tare da mu. Bayan Ayuba ya jimre gwajinsa, ya ce: “Na ji labarinka [Jehobah] ta wurin ji na kunne; amma yanzu idona ya gan ka.” (Ayuba 42:5) Da idon fahimi, bangaskiya, da kuma godiya, muna iya yin tunani a kan yadda Allah yake bi da mu kuma muna iya ‘ganinsa’ fiye da dā. Irin wannan dangantakar za ta sa mu sami kwanciyar hankali!

19. Menene zai faru idan muka ‘zuba duka alhininmu bisa Jehobah’?

19 Idan muka ‘zuba duka alhininmu bisa Jehobah,’ za mu iya jimre gwaji cikin kwanciyar hankali da zai kāre zuciyarmu da tunaninmu. A can cikin zuciyarmu ta alama, za mu sami ’yanci daga alhini da jin tsoro. Kuma hankalinmu zai kwanta.

20, 21. (a) Labarin Istifanus ya bayyana wane irin kwanciyar hankali ne sa’ad da ake fuskantar gwaji? (b) Ka ba da misali na zamani na kwanciyar hankali sa’ad da ake jimre gwaji.

20 Almajiri Istifanus ya nuna kwanciyar hankali sa’ad da yake jimre gwajin bangaskiyarsa. Kafin ya ba da shaidarsa ta ƙarshe, duka waɗanda suke zaune a cikin Majalisa sun ‘ga fuskarsa, sai ka ce fuskar mala’ika.’ (Ayukan Manzanni 6:15) Akwai alamar kwanciyar hankali a fuskarsa, kamar ta mala’ika, mai ɗauke da saƙon Allah. Bayan Istifanus ya fallasa laifinsu game da mutuwar Yesu, zuciyar alkalan “suka soku, suka ciji haƙoransu a kansa.” “Cike da Ruhu Mai-tsarki,” Istifanus “ya zuba ido zuwa sama, ya ga darajar Allah, da Yesu a tsaye ga hannun daman na Allah.” Da yake ya samu ƙarfafa daga wannan wahayin, Istifanus ya kasance da aminci har mutuwa. (Ayukan Manzanni 7:52-60) Ko da yake ba ma ganin wahayi, muna iya samun kwanciyar hankali daga Allah sa’ad da aka tsananta mana.

21 Ka yi la’akari da kalaman wasu Kiristoci da ’yan Nazi suka kashe a lokacin Yaƙin Duniya na biyu. Sa’ad da yake faɗin abin da aka yi masa a kotu kafin a kashe shi, ɗaya daga cikinsu ya ce: “Na saurara sa’ad da ake karanta hukuncin mutuwar da aka yanke mini, kuma bayan haka na faɗi kalaman nan, ‘Ka kasance da aminci har mutuwa,’ da kuma wasu ’yan kalamai na Ubangijinmu, shi ke nan. Amma kada ku damu. Domin ina da kwanciyar hankali irin wadda ba ku zato!” Wani Kirista matashi da za a fille wa kai ya yi wa iyayensa wasiƙa: “Yanzu sha biyun dare ya riga ya wuce. Har yanzu ina da lokacin canja zuciyata. Amma! Zan taɓa yin farin ciki a wannan duniyar idan na musanta Ubangijinmu? Ko kaɗan! Amma yanzu, kuna da tabbacin cewa na bar wannan duniyar a cikin farin ciki da kwanciyar hankali.” Babu shakka, Jehobah yana taimaka wa bayinsa masu aminci.

Za Ka Iya Jimrewa!

22, 23. Wane tabbaci ne za ka iya kasancewa da shi yayin da kake jiran ranar Jehobah da jimiri?

22 Wataƙila ba za ka fuskanci wasu cikin ƙalubalen da muka tattauna ba. Duk da haka, Ayuba mai tsoron Allah ya faɗi gaskiya sa’ad da ya ce: “Mutum, haihuwar mace kwanakinsa kaɗanna ne, cike da wahala kuma.” (Ayuba 14:1) Wataƙila ku iyaye ne da ke aiki tuƙuru don ku yi wa yaranku ja-gora ta ruhaniya. Suna bukatar su jimre gwaji a makaranta, kuma za ku kasance da farin ciki sa’ad da suka manne wa Jehobah da mizanansa na adalci! Wataƙila kana fuskantar wahala da gwaji a wurin aikinka. Za ka iya jimre waɗannan da kuma wasu, domin ‘Jehobah yana ɗauke da nawayarka kowace rana.’—Zabura 68:19.

23 Kana iya tunanin cewa ba ka da amfani sosai, amma ka tuna cewa Jehobah ba zai taɓa mance aikinka da kuma ƙaunar da ka nuna wa sunansa mai tsarki ba. (Ibraniyawa 6:10) Da taimakonsa, kana iya jimre gwajin bangaskiya. Saboda haka, ka ci gaba da sa yin nufin Allah a addu’arka da kuma tsare-tsarenka. Da haka, za ka iya kasancewa da tabbacin samun albarka daga Allah da kuma taimakonsa yayin da kake jiran ranar Jehobah da jimiri.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa Kiristoci suke bukatar jimiri?

• Menene zai iya taimaka mana mu jimre da rashin lafiya da kuma baƙin ciki?

• Ta yaya ne addu’a ke taimaka mana mu jimre gwaji?

• Me ya sa ya yiwu mu jira ranar Jehobah da jimiri?

[Hoto a shafi na 15]

Dogara da Jehobah na sa mu jimre mutuwar waɗanda muke ƙauna

[Hoto a shafi na 17]

Addu’a na taimaka mana mu jimre gwajin bangaskiyarmu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba