Domin Bangaskiyarta Wata Uwa ta Yi Nasara Bisa Bala’i
“Idan kuna karanta wannan wasiƙar, yana nufin cewa ban tsira daga aikin da aka yi mini ba kuma na riga na mutu.”
DA WAƊANNAN kalaman ne wata uwa Mashaidiya mai suna Carmen ta soma wasiƙar da ta yi wa ’ya’yanta mata uku, masu shekaru 25, 19, 16. Sakamakon shi ne, ba a yi nasara ba sa’ad da aka yi mata fiɗar kuma Carmen ta rasu.
Barin yara mata uku a irin wannan mugun yanayi abin baƙin ciki ne sosai. Duk da haka, wannan uwar tana da bangaskiya mai ƙarfi ga Jehobah da alkawuransa kuma hakan ya sa ta yi nasara bisa bala’i, kuma wannan bangaskiyar ta ba ta kwanciyar hankali kamar yadda wasiƙarta mai ban tausayi ta nuna. Ga abin da ta gaya wa ’ya’yanta.
“Da farko, ina son in gaya muku cewa ina ƙaunarku da dukan zuciyata. . . . Ku ’ya’ya ne mafi kyau da uwa za ta so ta samu, ina alfahari da ku.
“Da zan so na ci gaba da zama tare da ku har sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta . . . , amma da yake ba zai kasance hakan ba, na roƙe shi ya taimake ku ku kasance masu aminci kamar yadda kuke. Mun jimre wa gwaji da yawa tare, kuma Jehobah bai taɓa yasar da mu ba. . . . Saboda haka, ku ci gaba da dogara ga ja-gorar da yake tanadinsa ta wurin ƙungiyarsa kuma ku ci gaba da ba da haɗin kai ga ikilisiya da dattawa. Ku yi wa’azi sau da yawa iyakar ƙoƙarinku, kuma ku ƙaunaci dukan ’yan’uwa.
“Rabuwarmu na ɗan lokaci ne. . . . Ku gafarta mini dukan kuskure da na yi da dukan lokaci da ban fahimce ku ba ko kuwa da ban gaya muku ba cewa ina ƙaunarku sosai. . . . Na san cewa kowannenku na da nasa bukatu. Jehobah ya san haka fiye da ku, kuma zai yi tanadin dukan abubuwan da kuke bukata kuma zai saka muku don dukan abubuwan da kuka jimre.
“Kada ku manta da makasudinku, wato, sabuwar duniya. Ku ci gaba da ƙoƙari don ku shige ta. Bari Jehobah ya albarkace ku kuma ya ƙarfafa ku don ku kasance da aminci har ƙarshe. . . . Kada ku yi baƙin ciki, ’ya’yana masu tamani. Ina ƙaunarku!”
Bala’i na iya faɗa wa kowa a kowane lokaci. Sarki Sulemanu na dā ya rubuta, “sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.” (Mai Hadishi 9:11; LMT) Amma waɗanda suke da bangaskiya mai ƙarfi ga Allah, suna da irin tabbaci na manzo Bulus, wanda ya ce: “Na kawar da shakka, ba mutuwa, ba rai, . . . ba kuwa wani halittacen abu, da za ya iya raba mu da ƙaunar Allah, wadda ke cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.”—Romawa 8:38, 39; Ibraniyawa 6:10.