Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 7/1 pp. 4-7
  • Neman Ilimi na Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Neman Ilimi na Gaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Rubutu Masu Tsarki da Za Su Kai Ka ga Ceto’
  • Muhimman Gaskiya
  • Natsu Wajen Bincika Nassosi Kowace Rana
  • Ka Yi Farin Ciki Ka Sami Kuma Kana Samun Sanin Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Biɗi Allah da Zuciya Da Kuma Azancinka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 7/1 pp. 4-7

Neman Ilimi na Gaskiya

ARANAR 18 ga Disamba, shekara ta 1810. Dare ya soma yi. Jirgin Mayaƙan Ruwa na Britaniya mai suna HMS Pallas ya ɓace a cikin hadari a kudu maso gabashin Scotland. Duhun dare da kuma dusar ƙanƙarar da ke zuba sun sa ya yi wa matuƙan jirgin wuya su ga alamar wutar da za ta yi wa jirginsu ja-gora zuwa baƙin teku. Ka yi tunanin irin farin ciki da suka yi sa’ad da suka ga wuta kuma suka nufi inda take da jirginsu! Abin baƙin ciki, ba wannan wutar suke bukata ba don ja-gora. Wannan wuta ce da wasu ma’aikata suka kunna a kusa da gaɓar tekun. Jirgin Pallas ya yi karo da duwatsu kuma ya ragargaje gaba ɗaya. Matuƙan jirgi sha ɗaya suka mutu. Wannan bala’i ne!

Game da jirgin Pallas, kuskure ne ya kai ga wannan bala’in. A wasu lokatai, matuƙan jirgin ruwa sun fuskanci haɗarurruka da suka wuce wannan, wato alamar wutar ƙarya. Ana kunna irin waɗannan wutan ne domin a yaudari jiragen ruwa su yi karo da duwatsu a kwashi ganima, in ji littafin nan Wrecks, Wreckers and Rescuers.

‘Rubutu Masu Tsarki da Za Su Kai Ka ga Ceto’

Sa’ad da kake biɗan ilimi, za ka fuskanci irin haɗarin da matuƙan jirgin nan suka fuskanta. Kana iya bin bayanin ƙarya, ko kuwa ka bari a ruɗe ka. Hakan na iya kai ga haɗari. Menene za ka yi don ka kāre kanka? Ka tabbata cewa tushen iliminka tabbatacce ne kuma ingantacce. Wannan jaridar ta ɗaukaka Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, a matsayin inda za a iya samun ainihin ilimi domin tana ɗauke da “littattafai masu-tsarki, waɗanda ke da iko su hikimtadda kai zuwa ceto” na fiye da shekara 125.—2 Timothawus 3:15-17.

Babu shakka, idan kana son ka dogara ga Littafi Mai Tsarki a matsayin tabbataccen ja-gora, zai dace ka bincika gaskiyarsa. (Zabura 119:105; Misalai 14:15) Kana iya rubuta wa waɗanda suka wallafa wannan jaridar don samun bayanin da ya tabbatar wa miliyoyi cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki. Alal misali, kana iya karanta mujallar nan mai suna Littafi Don Dukan Mutane.a Ta yi bayanai masu yawa da suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki cikakke ne, tabbatacce, kuma hurarre.

Muhimman Gaskiya

Menene wasu cikin waɗannan muhimman gaskiya da “littattafai masu-tsarki” suka ƙunsa? Yi la’akari da misalan da suke gaba:

Allah Maɗaukaki ɗaya ne kuma shi ne Mahaliccin dukan abubuwa. (Farawa 1:1) Muna raye ne domin “[Allah ya] halicci dukan abu” kuma ya ba mu rai. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Shi ya sa shi kaɗai ne ya cancanci mu bauta masa. Mahalicci shi ne ainihin Tushen dukan ilimi. (Zabura 36:9; Ishaya 30:20, 21; 48:17, 18) Yana da sunan da yake son mu kira shi da shi. (Fitowa 3:15) Wannan sunan da aka rubuta da yaren Ibraniyawa kuma wanda aka juya zuwa YHWH, ya bayyana sau 7,000 a cikin Littafi Mai Tsarki. Tun shekaru masu yawa ana kiransa da Turanci ‘Jehovah.’—Zabura 83:18.

Jehobah ya halicci maza da mata su rayu har abada a cikin Aljanna a nan duniya. Ya ba ’yan adam halaye na ruhaniya irin waɗanda yake da su. Ya ba su baiwa da kuma iyawa da zai sa su mori rayuwa mai armashi na dindindin a duniya. (Farawa 1:26-28) Ba nufinsa ba ne duniya ta zama wurin gwaji ga maza da mata, wato inda za a shirya mutane domin rayuwar ruhu a sama, kamar a wurin ne kawai za su iya morar dangantaka da Allah.

Babu wani mugun abu a cikin mutanen da Allah ya halitta. An soma mugunta ne sa’ad da wasu cikin halittun Allah, wato mutane da kuma halittar ruhu suka yi amfani da ’yancin yin zaɓe kuma suka yi wa Allah tawaye. (Kubawar Shari’a 32:5) Iyayenmu na farko sun ɗauka wa kansu ikon zaɓa wa kansu abin da ke da kyau da marar kyau. (Farawa 2:17; 3:1-5) Hakan ya jawo wa iyalin mutane mutuwa. (Farawa 3:19; Romawa 5:12) Don daidaita batutuwan da tawayen ya tayar, Jehobah ya ƙyale mugunta na ɗan lokaci. Amma manufarsa ga wannan duniyar da kuma iyalin ’yan adam ba ta canja ba. (Ishaya 45:18) Maza da mata za su rayu har abada a cikin Aljanna a duniyar da aka tsabtacce.—Matta 6:10; Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.

Yesu Kristi ba shi ne Allah Maɗaukaki ba, amma Ɗan Allah ne. Yesu Kristi da kansa ya koya wa mabiyansa su yi addu’a haka: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Bai taɓa daidaita kansa da Allah ba. Maimakon haka, ya ce: “Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.

Yesu ya cika muhimmin gurbi wajen cika nufin Allah. Allah ya aiko shi ya zama “haske cikin duniya, domin dukan wanda yana ba da gaskiya [gare shi] kada shi zauna cikin duhu.” (Yohanna 12:46) In ji manzo Bitrus, “babu ceto ga waninsa.” (Ayukan Manzanni 4:12) Wannan gaskiya ne domin cetonmu ya dangana ne a kan jinin Kristi mai tamani. (1 Bitrus 1:18, 19) Yesu Kristi ya ba da ransa a matsayin hadayar fansa domin ya ceci mutane daga zunubin da iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u suka jefa iyalinsu. (Matta 20:28; 1 Timothawus 2:6) Kuma Allah ya yi amfani da Yesu ya bayyana nufinsa.—Yohanna 8:12, 32, 46, 47; 14:6; Ayukan Manzanni 26:23.

Allah ya riga ya kafa Mulki ko kuwa gwamnati a sama, wa Yesu Kristi da waɗanda aka zaɓa daga cikin mutane. Wannan jigon da ake yawan maimaitawa ya cika Littafi Mai Tsarki. Allah ya miƙa wa wannan gwamnatin hakkin tabbatar da cewa an yi nufinsa a duniya kamar yadda ake yi a sama. (Matta 6:10) A dā, ba nufin Allah ba ne mutane su je sama. Duniya ce ya kamata ta zama gidansu. Amma sa’ad da mutum ya faɗa cikin zunubi, Allah ya ƙudurta wani sabon abu. Ya shirya ya zaɓi mutane “daga cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, da iri” su yi “mulki” da Kristi a gwamnatin sama. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10) Nan ba da daɗewa ba, wannan Mulkin “za ya parpashe . . . ya cinye” duka ire-iren sarautar mutane, wadda ta jawo kaito da azaba ga iyalin mutane.—Daniel 2:44.

Kurwa tana mutuwa. Wannan muhimmiyar gaskiya ta Littafi Mai Tsarki ta yi bayani sosai game da mutum da kuma rayuwarsa. Kuma ta kawar da rashin fahimta da kuma bayanai na ƙarya da suka ruɗi mutane game da yanayin matattu.

Littafi na farko na Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: ‘Ubangiji Allah kuwa ya sifanta mutum daga turɓayar ƙasa, ya hura masa lumfashin rai cikin hancinsa; mutum kuma ya zama rayayyen mai-rai.’ (Farawa 2:7) Ka fahimci abin hakan ke nufi? Kurwa ba wani abu ne da ke raye a jikin mutum. Mutum ba shi da kurwa. Shi ne kurwa, wato abubuwan da aka harhaɗa daga “turɓayar ƙasa” da kuma rai da ya fito daga Allah. Kurwa tana mutuwa. Sa’ad da mutum ya mutu, kurwa ta mutu.—Farawa 3:19; Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Waɗanda suka mutu za a iya ta da su daga matattu. Sa’ad da wannan ɗan lokacin da Allah ya ƙyale mugunta ya wuce, “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma: waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai; waɗanda sun yi mugunta, zuwa tashi na shari a.” (Yohanna 5:28, 29; Ayukan Manzanni 24:15) Tashin matattu zai maido mutane zuwa rai a aljanna a duniya, zuwa ga ainihin irin ran da Allah ya nufa wa iyalin mutane.

Natsu Wajen Bincika Nassosi Kowace Rana

Ka ga yadda sanin wannan muhimmiyar gaskiyar zai taimake ka? A wannan lokaci na wahala, irin wannan sanin zai iya kāre ka daga “ilimin da ana ce da shi hakanan a ƙaryace” da Shaiɗan Iblis yake yayyaɗawa. Yana faɗin cewa shi “mala’ika na haske” ne, kuma wakilansa sun mayar da kansu “masu-hidiman adalci.” (1 Timothawus 6:20; 2 Korinthiyawa 11:13-15) Cikakken sani na Littafi Mai Tsarki zai iya kāre ka daga ilimin da ya fito daga ussan ilimi na wannan duniyar na “masu-hikima da masu-fahimi” waɗanda “sun ƙi maganar Ubangiji.”—Matta 11:25; Irmiya 8:9.

Domin akwai koyarwa masu yaudara da kuma ussan ilimi a zamaninsa, manzo Yohanna ya yi wa Kiristoci na ƙarni na farko gargaɗi: ‘Kada ku bada gaskiya ga kowane ruhu.’ Ya ce: “Ku gwada ruhohi, ko na Allah ne.” (1 Yohanna 4:1) Yi la’akari da wannan misalin. Idan ka sami wani bayani da zai iya shafar rayuwarka, za ka karɓa ne domin bayanin ya fito daga tushe mai kyau ba tare da ka yi tunani ba? A’a. Za ka duba tushen saƙon, kuma za ka duba abin da ya ƙunsa kafin ka ɗauki mataki a kai.

Ta wajen yin tanadin hurarren rubutu da ke ɗauke da muhimman gaskiya, Allah ya sa za ka iya yin haka, wato “auna” ko haske mai ja-gora da kake bi tabbatacce ne. (1 Tassalunikawa 5:21) An yaba wa mutane masu yardar rai a ƙarni na farko domin “suna bin cikin littattafai kowace rana” don su tabbata cewa abubuwan da suka koya gaskiya ne. (Ayukan Manzanni 17:11) Kai ma za ka iya yin haka. Ka ƙyale Littafi Mai Tsarki, “kamar da fitilla mai-haskakawa cikin wuri mai-duhu,” ya yi maka ja-gora har ka tsira. (2 Bitrus 1:19-21) Idan ka yi haka, za “ka ruski sanin Allah,” wanda ke ba da ilimi na gaskiya.—Misalai 2:5.

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 4]

Kalmar Allah kamar fitila take

[Hoto a shafi na 5]

Menene sunan Allah?

[Hoto a shafi na 5]

Menene zai sami mutane a nan gaba?

[Hoto a shafi na 6]

Yesu shi ne Allah Maɗaukaki?

[Hoto a shafi na 6]

Ina matattu suke?

[Hoto a shafi na 7]

Tashin matattu yana ɗaya daga cikin muhimman gaskiyar da aka koyar a cikin Littafi Mai Tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba