Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 6/1 pp. 3-4
  • Ana Banza da Kuma Wulakanta Tsofaffi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ana Banza da Kuma Wulakanta Tsofaffi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Makamantan Littattafai
  • Kula Da Tsofaffi Hakki Ne Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Allah Yana Kula da Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Suna Ware Amma Ba A Mance Da Su Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Jehobah Yana Kula Da Bayinsa Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 6/1 pp. 3-4

Ana Banza da Kuma Wulakanta Tsofaffi

MAI gadi yana kewaye kewayensa, abin da ya gani abin tsoro ne. A waje a gaban gagarumin gida, sai ga gawawwakin tsofaffi biyu mata da miji, waɗanda suka faɗo daga gidan bene mai hawa takwas. Ko da yake kashe kansu da suka yi yana da ban tsoro, dalilin haka ya fi ma ban tsoro. Rubutu da aka samu a aljihun mijin ya ce: “Mun kashe kanmu ne domin wulakanci da ƙiyayyar da ɗanmu da matarsa suke nuna mana.”

Ba kullum ake samun irin wannan labarin ba, amma abin da ya jawo wannan abin damuwa ne kuma abu ne da ya zama ruwan dare. Hakika wulakanta tsofaffi yana faruwa a kusan dukan ɓangarorin duniya. Ga misali:

• Wani bincike ya nuna cewa, kashi 4 na tsofaffi a Kanada sun ba da rahoton cewa wani cikin iyalinsu ya wulakanta su. Amma kuma, da yawa cikin waɗannan tsofaffi suna kunya ko kuma tsoron su faɗi abin da yake damunsu. Waɗanda ake wulakantawa a hakikanin gaskiya za su kai kusan kashi 10, in ji masana.

• “Al’ummar Indiya ko da yake tana ba da alamar iyali masu ƙaunar juna, adadin tsofaffi da ’ya’yansu suke ƙin su yana ƙaruwa,” in ji mujallar nan India Today.

• Wani adadi da ke akwai ya nuna cewa, “tsakanin miliyan 1 ko 2 na Amirkawa masu shekara 65 zuwa sama, wanda suka dogara ya kula da su ko ya kāre su, ya ji musu rauni ko ya wulakanta su,” in ji National Center on Elder Abuse (Cibiyar Kula da Wulakanta Tsofaffi). Wani mataimakin lauyan gunduma a San Diego ta California, ya ce “wulakanta tsofaffi ita ce babbar matsalar da take damun hukuma a yau.” Ya daɗa cewa: “Ina ganin matsalar za ta ƙaru a nan da shekaru kaɗan masu zuwa.”

• A Canterbury ta New Zealand, damuwa tana ƙaruwa game da yadda wasu cikin iyali da suke shan miyagun ƙwayoyi, giya, ko kuma suke da matsalar caca suke fakon tsofaffi. Adadin ƙara da aka kai na waɗanda aka wulakanta ya yi tashin gwauron zabi daga 65 a shekara ta 2002 zuwa 107 a shekara ta 2003. Wani shugaban hukumar da aka kafa ta hana wannan wulakanci ya ce, wannan “adadin ba wani abu ba ne idan aka kwatanta shi da adadi na ainihi.”

• Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar Japan ta ba da shawara cewa “tsofaffi da aka wulakanta ya kamata mu mai da musu hankali fiye ma da yara da aka zalunta ko kuma wasu da aka zalunta,” in ji The Japan Times. Me ya sa? In ji Times ɗin, “idan aka gwada da zaluntar yaro ko kuma abokiyar aure, wulakanta tsofaffi tana ɗaukan lokaci mai tsawo kafin ta bayyana, dalili kuma shi ne domin tsofaffi suna ɗaukan alhakin haka idan ɗansu ne ko ’yarsu ya ko ta wulakanta su, kuma domin gwamnati ba za ta sami hanyar magance wannan matsalar ba.”

Waɗannan ’yan misalan abubuwa ne da suke faruwa a duniya da suka sa mu yi tambayoyi: Me ya sa ake banza kuma ake wulakanta tsofaffi haka masu yawa? Da bege kuwa cewa abubuwa za su gyaru? Wace ƙarfafa ce tsofaffi suke da ita?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba