Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 9/1 pp. 4-8
  • Za Ka Nuna Ɗaukakar Allah Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Nuna Ɗaukakar Allah Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Kiristoci Suke Nuna Ɗaukakar Allah
  • Ba Za a sa Mutanen Allah Su Yi Shuru Ba
  • Muna Jimrewa da Taimakon Jehobah
  • Aikin da Za a Riƙa Tunawa
  • Kana Nuna Ɗaukakar Jehobah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Kiristoci Ku Nuna Ɗaukakar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Kada Ka Ƙyale Kome Ya Hana Ka Samun Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • “Ka Cika Hidimarka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 9/1 pp. 4-8

Za Ka Nuna Ɗaukakar Allah Kuwa?

“Muke nuna ɗaukakar Ubangiji kamar madubi.”—2 KORANTIYAWA 3:18.

1. Menene Musa ya gani, kuma menene ya faru bayan haka?

WANNAN shi ne wahayi mafi ban tsoro da mutum ya taɓa gani. Musa ya kaɗaita a kan Dutsen Sinai, kuma an amsa roƙo mai wuya da ya yi. An ƙyale shi ya ga abin da mutum bai taɓa gani ba, wato ɗaukakar Jehobah. Amma fa, Musa bai ga Jehobah ba kai tsaye. Bayyanuwar Allah tana da girma da babu mutumin da zai ganta ya rayu. Maimakon haka, Jehobah ya kāre Musa da ‘hannunsa,’ babu shakka, ya yi amfani da mala’ika domin kada wani abu ya same shi har sai Jehobah ya wuce. Bayan haka, Jehobah ya ƙyale Musa ya ga wasu ’yan ƙyalli na wannan tsarkakkiyar ɗaukaka. Kuma Jehobah ya yi wa Musa magana ta bakin mala’ika. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta abin da ya faru bayan haka: “Sa’ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sinai . . . fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.”—Fitowa 33:18–34:7, 29.

2. Menene manzo Bulus ya rubuta game da ɗaukakar da Kiristoci suke nunawa?

2 A ce kana tare da Musa a kan dutsen. Zai zama abin ban sha’awa ka ga haske mai kashe ido na Maɗaukaki kuma ka saurari kalamansa! Zai kasance gata mai girma ka yi tafiya a kan Dutsen Sinai tare da Musa wanda shi ne matsakancin Doka ta alkawari! Ka san cewa a wasu hanyoyi Kiristoci na gaskiya suna nuna ɗaukakar Allah fiye da wadda Musa ya nuna? Wannan gaskiya mai sa tunani an same ta ne a wata wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta. Ya rubuta cewa Kiristoci shafaffu suna “nuna ɗaukakar Ubangiji kamar madubi.” (2 Korantiyawa 3:7, 8, 18) A wata sassa, Kiristoci da suke da bege na duniya su ma suna nuna ɗaukakar Allah.

Yadda Kiristoci Suke Nuna Ɗaukakar Allah

3. Ta yaya ne muka san Jehobah a hanyoyin da Musa bai sani ba?

3 Ta yaya ne za mu iya nuna ɗaukakar Allah? Ba mu taɓa gani ko jin muryar Jehobah kamar yadda Musa ya yi ba. Amma, mun san Jehobah a hanyoyin da Musa bai san sa ba. Yesu bai bayyana ba a matsayin Almasihu sai bayan kusan shekaru 1,500 bayan mutuwar Musa. Sakamakon haka, Musa bai san yadda Dokar za ta cika a Yesu wanda ya mutu domin ya ceci mutane daga zaluncin zunubi da mutuwa ba. (Romawa 5:20, 21; Galatiyawa 3:19) Bugu da ƙari, Musa ya ɗan fahimci ɗaukakar manufar Jehobah, wadda ke da nasaba ta kusa da Mulkin Almasihu, da kuma Aljanna a duniya da za ta kawo. Da haka, mun ga ɗaukakar Jehobah ba da idanun mu ba, amma da idanun bangaskiya da ke bisa koyarwa ta Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, mun ji muryar Jehobah, ba ta wurin mala’ika ba, amma ta wurin Littafi Mai Tsarki, musamman ma Linjila wadda ta kwatanta koyarwa da hidimar Yesu a hanya mai kyau.

4. (a) Ta yaya ne shafaffun Kiristoci suke nuna ɗaukakar Allah? (b) A waɗanne hanyoyi ne waɗanda suke da bege na duniya suke nuna ɗaukakar Allah?

4 Ko da yake Kiristoci ba sa nuna ɗaukakar Allah ta wajen annurin da ke fuskarsu, amma fuskarsu tana nuna haske yayin da suke gaya wa wasu game da mutuntakar Jehobah masu ɗaukaka da kuma manufofinsa. Game da zamaninmu, annabi Ishaya ya annabta cewa mutanen Allah za su ‘ba da labarin girman [Jehobah] ga waɗannan al’ummai.’ (Ishaya 66:19) Bugu da ƙari, a 2 Korantiyawa 4:1, 2 mun karanta: “Da ya ke muna da wannan hidima . . . , Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.” A nan, Bulus yana nuni ne musamman ga shafaffun Kiristoci waɗanda sune masu “hidima na Sabon Alkawari.” (2 Korantiyawa 3:6) Amma hidimarsu ta shafi mutane masu yawa waɗanda suke da begen samun rai madawwami a duniya. Hidimarsu duka ta ƙunshi nuna ɗaukakar Jehobah ba kawai a abin da suke koyarwa ba, amma a yadda suke rayuwarsu. Gata ce kuma hakkinmu ne mu nuna ɗaukakar Allah Maɗaukaki!

5. Mecece ni’imarmu ta ruhaniya ke nunawa?

5 A yau, ana wa’azin bisharar ɗaukakar Mulkin Allah a dukan duniya kamar yadda Yesu ya annabta. (Matiyu 24:14) Mutane daga al’ummai, harsuna, sun saurari bisharar kuma sun canja rayuwarsu domin su yi nufin Allah. (Romawa 12:2; Wahayin Yahaya 7:9) Kamar Kiristoci na farko, sun ƙi su daina faɗin abubuwan da suka gani kuma suka ji. (Ayyukan Manzanni 4:20) Fiye da mutane miliyan shida ne suke nuna ɗaukakar Allah a yau. Kana cikinsu kuwa? Ni’ima ta ruhaniya na mutanen Allah tana bayyana albarkar Jehobah da kuma kāriyarsa. Sanin cewa ruhun Jehobah na tare da mu na ba mu ƙarin tabbaci cewa akwai iko masu ƙarfi da suka kewaye mu. Bari mu ga dalilin da ya sa haka.

Ba Za a sa Mutanen Allah Su Yi Shuru Ba

6. Me ya sa ake bukatar bangaskiya da gaba gaɗi domin samun matsayi wurin Jehobah?

6 A ce an kira ka ka zo ka ba da shaida a kotu a kan wani mai laifi marar tausayi. Kuma ka sani cewa wannan mai laifin yana da wata ƙungiya kuma zai iya yin kome don kada ka fallasa shi. Domin ka ba da shaida game da wannan mai laifin, kana bukatan ka kasance da gaba gaɗi da kuma ƙarfafa cewa hukuma za ta kāre ka daga hannunsa. Muna cikin yanayi makamancin haka. A shaidar da muke yi game da Jehobah da kuma manufofinsa, muna ba da shaida ne game da Shaiɗan Iblis, muna fallasa shi a matsayinsa na mai kisan kai da kuma maƙaryaci wanda yake yaudaran dukan duniya. (Yahaya 8:44; Wahayin Yahaya 12:9) Domin ka sami matsayinka a wurin Jehobah kuma ka yi gāba da Iblis na bukatar bangaskiya da gaba gaɗi.

7. Ta yaya Shaiɗan yake rinjaya, kuma menene yake ƙoƙarin yi?

7 Jehobah shi ne Mafifici. Ikonsa ya fi na Shaiɗan. Kuma mun tabbata cewa Jehobah zai iya kāre mu kuma yana ɗokin yin haka idan muka ci gaba da bauta masa cikin aminci. (2 Tarihi 16:9) Duk da haka, Shaiɗan shi ne mai sarautar aljanu da kuma duniyar da ke bare daga Allah. (Matiyu 12:24, 26; Yahaya 14:30) Tun da yake an jefo shi duniya kuma yana cike da “matsanancin fushi,” Shaiɗan yana hamayya da bayin Jehobah kuma yana amfani da duniyar da take ƙarƙashin ikonsa don ya rufe bakin dukan waɗanda suke yin wa’azin bishara. (Wahayin Yahaya 12:7-9, 12, 17) Ta yaya yake yin haka? Aƙalla ta hanyoyi uku.

8, 9. Ta yaya ne Shaiɗan ke amfani da ƙauna ta ƙarya, kuma me ya sa ya kamata mu zaɓi waɗanda muke tarayya da su sosai?

8 Hanya ɗaya da Shaiɗan ke ƙoƙarin janye hankalinmu ita ce ta kula da rayuwa. A wannan zamani na ƙarshe, mutane sun zama masu son kuɗi, masu sonkai, masu son annashuwa. Amma ba sa son Allah. (2 Timoti 3:1-4) Da yake sun shagala da al’amuran rayuwa na yau da kullum, yawancin mutane “ba su farga” ba da bisharar da muke kawo musu. Ba sa son koyon gaskiyar Littafi Mai Tsarki. (Matiyu 24:37-39) Irin wannan halin na iya shafanmu, kuma ya jawo mana gyangyaɗi na ruhaniya. Idan muka gina ƙauna ga abubuwa na biyan bukata da kuma annashuwa ta rayuwa, ƙaunar da muke yi wa Allah za ta yi sanyi.—Matiyu 24:12.

9 Domin wannan dalilin, Kiristoci suna zaɓan irin mutanen da suke yin tarayya da su. Sarki Sulemanu ya rubuta cewa: “Ka koya daga wurin masu hikima, za ka zama mai hikima, yi abuta da wawaye, za ka kuwa lalace.” (Karin Magana 13:20) Bari mu yi “abuta” da waɗanda suke nuna ɗaukakar Allah. Abu ne mai kyau mu yi haka! Yayin da muke taruwa tare da ’yan’uwanmu na ruhaniya maza da mata a wajen taronmu da kuma a wasu lokatai, muna samun ƙarfafa domin ƙaunarsu, imaninsu, murnarsu, da kuma fahiminsu. Irin wannan tarayya mai kyau na ƙarfafa ƙudurinmu na ci gaba a hidimarmu.

10. A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan ya yi amfani da ba’a a kan mutanen da suke nuna ɗaukakar Allah?

10 Hanya ta biyu da duniya take amfani da ita domin ta hana Kiristoci nuna ɗaukakar Allah ita ce, ba’a. Wannan dabarar ba abin mamaki ba ce. A lokacin hidimarsa a duniya, an yi wa Yesu Kristi ba’a, an yi masa dariya, an yi masa tsaki, an wulakanta shi, har ma an tofa ma shi yau. (Markus 5:40; Luka 16:14; 18:32) Kiristoci na farko su ma sun zama abin ba’a. (Ayyukan Manzanni 2:13; 17:32) Bayin Jehobah na zamani su ma suna fuskantar irin wannan zagin. In ji manzo Bitrus, za a kira su annabawan ƙarya. Bitrus ya annabta: “Can zamanin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna biye wa muguwar sha’awa tasu, suna cewa, ‘To, ina alkawarin dawowa tāsa? Ai, . . . dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.’ ” (2 Bitrus 3:3, 4) Ana yi wa mutanen Allah ba’a cewa ba su da tabbaci. An ɗauki mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a tsohon yayi. Ga mutane da yawa, saƙon da muke wa’azinsa wawanci ne. (1 Korantiyawa 1:18, 19) Mu Kiristoci muna iya fuskantar ba’a a makaranta, a wajen aiki, a wasu lokatai ma har a cikin iyali. Ba mu yi sanyin gwiwa ba, amma mun ci gaba da nuna ɗaukakar Allah ta wurin wa’azin da muke yi, kamar Yesu mun san cewa, Kalmar Allah gaskiya ce.—Yahaya 17:17.

11. Ta yaya ne Shaiɗan ya yi amfani da tsanantawa domin ya rufe bakin Kiristoci?

11 Dabara ta uku da Iblis ke amfani da ita domin ya rufe bakinmu ita ce, hamayya ko tsanantawa. Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Sa’an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al’ummai za su ƙi ku saboda sunana.” (Matiyu 24:9) Hakika, mu Shaidun Jehobah mun fuskanci mugun tsanani a wurare da yawa a ɓangarorin duniya. Mun sani cewa tun da daɗewa Jehobah ya annabta cewa ƙiyayya, ko gāba za ta kasance tsakanin waɗanda suke bauta wa Allah da waɗanda suke bauta wa Shaiɗan Iblis. (Farawa 3:15) Mun sani cewa idan muka kasance da aminci a lokacin gwaji, hakan ya nuna cewa muna goyon bayan ikon mallakar Jehobah. Sanin haka zai sa mu kasance da ƙarfi har ma a cikin yanayi mai wuya. Babu tsanantawa da zai sa mu yi shiru idan muka ƙudurta cewa za mu nuna ɗaukakar Allah.

12. Me ya sa ya kamata mu yi murna idan muka kasance da aminci sa’ad da muka fuskanci hamayya daga Shaiɗan?

12 Kana ƙin rinjayar duniya ka kuma kasance da aminci duk da ba’a da hamayya? Idan haka ne, kana da dalilin yin murna. Yesu ya tabbatar wa waɗanda za su bi shi cewa: “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni. Ku yi murna da farin ciki matuƙa, domin sakamakonku mai yawa ne a sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.” (Matiyu 5:11, 12) Jimrewarka na ba da tabbacin cewa ruhu mai tsarki mai iko na Jehobah yana tare da kai, kuma yana ƙarfafa ka ka nuna ɗaukakarsa.—2 Korantiyawa 12:9.

Muna Jimrewa da Taimakon Jehobah

13. Menene dalili mafi muhimmanci da ya sa muke jimrewa a hidimarmu ta Kirista?

13 Dalili mafi muhimmanci da ya sa muke jimrewa a hidimarmu shi ne ƙaunar da muke yi wa Jehobah da kuma son nuna ɗaukakarsa. Mutane sukan so su bi misalan waɗanda suke ƙauna suke kuma darajawa, kuma babu wanda ya cancanci a yi koyi da shi sai Jehobah Allah. Domin ƙaunarsa mai yawa, ya aiko Ɗansa zuwa duniya domin ya shaidi gaskiya kuma ya ceci mutane masu biyayya. (Yahaya 3:16; 18:37) Kamar Allah, muna son dukan ire-iren mutane su kai ga tuba kuma su sami ceto, wannan shi ne dalilin da ya sa muke yi musu wa’azi. (2 Bitrus 3:9) Wannan muradin, tare da ƙudurinmu na yin koyi da Allah, na motsa mu mu ci gaba a nuna ɗaukakar Allah a hidimarmu.

14. Ta yaya ne Jehobah ya ƙarfafa mu domin mu jimre a hidimarmu?

14 Amma, daga wurin Jehobah ne muke samun ƙarfin jimrewa a hidimarmu ta Kirista. Yana kāre mu kuma yana ƙarfafa mu ta wurin ruhunsa, ƙungiyarsa, da kuma Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Jehobah yana “ba da haƙuri” ga waɗanda suke so su nuna ɗaukakarsa. Yana amsa addu’armu kuma yana ba mu hikima domin mu bi da gwaji. (Romawa 15:5; Yakubu 1:5) Ƙari ga haka, Jehobah ba ya ƙyale mu mu fuskanci gwajin da ba za mu iya jimrewa ba. Idan muka dogara ga Jehobah, zai yi mana mafita domin mu ci gaba da nuna ɗaukakarsa.—1 Korantiyawa 10:13.

15. Menene ke taimaka mana mu jimre?

15 Jimrewa a hidimarmu na nuna cewa ruhun Allah yana tare da mu. Alal misali: A ce wani ya umurce ka ka raba burodi kyauta daga kofa zuwa kofa. Kuma ya umurce ka ka yi amfani da kuɗinka da kuma lokacinka. Bayan haka, sai ka fahimci cewa mutane kaɗan ne kawai suke son burodinka, wasu har hamayya suke yi maka domin ƙoƙarin da kake yi na raba shi. Kana ganin cewa za ka ci gaba da wannan aikin na watanni har shekaru? Wataƙila a’a. Amma ka himmantu wajen yin shelar bishara da lokacinka da kuma kuɗinka na shekaru da yawa. Me ya sa? Ba domin ƙaunar da kake yi wa Jehobah ba ne, da kuma albarka da ya sa wa ƙoƙarinka ta wurin ruhunsa don ya taimaka maka ka jimre? Hakika!

Aikin da Za a Riƙa Tunawa

16. Jimrewa a hidimarmu na nufin menene a gare mu da kuma waɗanda suka saurare mu?

16 Hidimar sabuwar alkawari kyauta ce da ba ta misaltuwa. (2 Korantiyawa 4:7) Hakazalika, hidimar Kirista da waɗansu tumaki suke yi a dukan duniya wadata ce. Yayin da ka ci gaba da jimrewa a hidimarka, kamar yadda manzo Bulus ya rubuta wa Timoti, “za ka ceci kanka da masu sauraronka.” (1 Timoti 4:16) Ka yi tunanin abin da wannan ke nufi. Bisharar da kake wa’azinta tana ba wasu zarafin samun rai madawwami. Za ka iya gama abota na kud da kud da waɗanda ka taimaka wa a ruhaniyance. Ka yi tunanin irin murnar da za ka samu na yin rayuwa madawwami a Aljanna da waɗanda ka taimaka wa su koyi game da Allah! Hakika, ba za su taɓa mance ƙoƙarin da ka yi na taimaka musu ba. Wannan abu ne mai gamsarwa!

17. Me ya sa lokacinmu shi ne lokaci mafi muhimmanci a tarihin ’yan adam?

17 Kana raye a lokaci na musamman a tarihin ’yan adam. Ba za a ƙara wa’azin bishara ba a duniyar da take bare daga Allah. Nuhu ya rayu a irin wannan duniyar, kuma ya ga sa’ad da ta shuɗe. Ya yi murna domin ya aikata nufin Allah na gina jirgi cikin aminci, wanda hakan ya kāre shi da iyalansa! (Ibraniyawa 11:7) Kai ma kana iya samun irin wannan farin cikin. Ka yi tunanin yadda za ka ji a sabuwar duniya sa’ad da ka tuna aikin da ka yi a wannan zamani na ƙarshe, sanin cewa ka yi iya ƙoƙarinka wajen ɗaukaka abubuwan Mulki.

18. Wane tabbaci da ƙarfafa ne Jehobah ya ba bayinsa?

18 Bari mu ci gaba da nuna ɗaukakar Allah. Idan muka yi haka, za mu riƙa tunawa da shi har abada. Jehobah yana tuna aikinmu. Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan ƙarfafar: “Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. Muna dai kukata ƙwarai kowannenku ya nuna irin wannan himma ga yin cikakkiyar sa zuciya, tabbatacciya, har ya zuwa ƙarshe, don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da waɗanda suka karɓi cikar alkawaran nan, ta bangaskiya tasu da haƙurinsu.”—Ibraniyawa 6:10-12.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Ta yaya ne Kiristoci suke nuna ɗaukakar Allah?

• Waɗanne dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su a ƙoƙarinsa na rufe bakin mutanen Allah?

• Wane tabbaci ne ke nuna cewa ruhun Allah yana tare da mu?

[Hoto a shafi na 5]

Fuskar Musa ta nuna annuri

[Hotuna a shafuffuka na 6, 7]

Muna nuna ɗaukakar Allah a hidimarmu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba