Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 9/1 p. 3
  • “Da an Sake Su da Wuri”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Da an Sake Su da Wuri”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 9/1 p. 3

“Da an Sake Su da Wuri”

GENEVIÈVE DE GAULLE, ’yar ɗan’uwan Charles de Gaulle, tsohon shugaban ƙasar Faransa, ta san Shaidun Jehobah sosai a sansanin fursuna na Nazi da ke Ravensbrück, a arewacin Jamus. Ita ce ta rubuta furcin da ke sama a wata wasiƙa a watan Agusta, shekara ta 1945.

An ’yantar da sansanin fursunan da ke Auschwitz, a ƙasar Poland, a ranar 27 ga Janairu, 1945. Tun shekara ta 1996, an ci gaba da tuna wannan rana a Jamus domin waɗanda suka shiga hannu a lokacin mulkin Hitler.

A lokacin wani jawabi na tuni a ranar 27 ga Janairu, 2003, shugaban Majalisar Wakilai na Baden-Württemberg, Peter Straub, ya ce: “Dukan waɗanda suka sha tsanani domin addininsu ko kuwa domin siyasa, kuma sun gwammace su mutu da su miƙa kansu, sun cancanci mu daraja su sosai, kuma ba za mu iya furta wannan darajar da kalamai ba kawai. Shaidun Jehobah ne kawai ’yan addini da suka ƙi yin abin da mulkin Hitler ke bukata: Sun ƙi su sara wa Hitler. ‘Sun ƙi su yi masa biyayya,’ kamar yadda suka ƙi yin aikin soja. Kuma yaransu sun ƙi su shiga Ƙungiyar Matasa na Hitler.”

Yesu Kristi ya ce game da mabiyansa: “Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.” (Yahaya 17:16) Matsayin Shaidun Jehobah ya dangana ne a kan addininsu. Straub ya ci gaba: “Shaidun Jehobah waɗanda suke sanye da bajo mai ruwan albasa a rigunansu a matsayin fursunoni a sansanin fursuna, sune kawai za su iya janye kisan da za a yi musu. Saka hannu a takardar da ta musanta imaninsu kawai ake bukata.”

Yawancin Shaidu sun ƙi su saɓi imaninsu. Saboda haka, kusan 1,200 ne suka mutu a Nazi. An kashe ɗari biyu da saba’in a matsayin ’yan hamayya. Sun yi biyayya ga kalmar nan: “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”—Ayyukan Manzanni 5:29.

Shaidun Jehobah ba wai mutane ba ne na musamman, kamar yadda Ulrich Schmidt, shugaban Majalisa na arewacin Rhine-Westphalia ya faɗa. Sa’ad da take nuni ga maganarsa, mujallar nan Landtag Intern ta kira su “talakawa waɗanda suke bin lamirinsu, sun yi tsayin daka domin imaninsu na addini, sun nuna gaba gaɗi na ’yan ƙasa, kuma sun fallasa ra’ayin Nazi domin tabbacinsu na Kirista.” Muna da tabbacin cewa Jehobah Allah yana farin ciki bisa duka waɗanda suka manne masa cikin aminci a lokaci mai wuya. A Karin Magana 27:11 mun karanta: “Ɗana, ka zama mai hikima, ni kuwa zan yi farin ciki, zan iya amsa kowace irin sūkar da wani zai yi mini.”

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 3]

Courtesy of United States Holocaust Memorial Museum

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba