Maganar Jehobah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Sama’ila na Ɗaya
ASHEKARA ta 1117 K.Z. Shekaru ɗari uku bayan Joshuwa ya gama cin Ƙasar Alkawari da yaƙi. Dattawa na Isra’ila suka roƙi annabin Jehobah wani abu mai ban mamaki. Annabin ya yi addu’a game da batun, kuma Jehobah ya ji roƙonsu. Wannan shi ne ya kawo ƙarshen zamanin Mahukunta kuma ya soma na sarakuna. Littafin Sama’ila na Ɗaya ya bayyana aukuwa masu ban mamaki a lokaci na musamman a tarihin al’ummar Isra’ila.
Littafin Sama’ila na Ɗaya ya ɗauki tsawon shekara 102—daga shekara ta 1180 zuwa 1078 K.Z., kuma Sama’ila, Natan, da Gad ne suka rubuta shi. (1 Tarihi 29:29) Labari ne na shugabannin Isra’ila huɗu. Biyu mahukunta ne, biyu kuma sarakuna ne. Biyu sun yi wa Jehobah biyayya, sauran kuma ba su yi ba. Akwai kuma labarin mata biyu da abin koyi ne da kuma wani mayaƙi mai gaba gaɗi. Irin waɗannan misalan za su koya mana darussa game da halayen da za mu yi koyi da su da kuma waɗanda za mu ƙi. Da haka, abin da ke cikin littafin Sama’ila na Ɗaya zai sami ƙarfin aiki a kan tunaninmu da kuma halayenmu.—Ibraniyawa 4:12.
SAMA’ILA YA GAJI ELI A MATSAYIN MAHUKUNCI
(1 Sama’ila 1:1–7:17)
A lokacin Idin Tattara Amfanin Gonaki, Hannatu wadda take da zama a Rama tana ta farin ciki.a Jehobah ya riga ya ji addu’arta, kuma ta haifi ɗa na miji. Domin ta cika wa’adin da ta yi, Hannatu ta ba da ɗanta Sama’ila domin ya yi hidima a “ɗakin Ubangiji.” A wajen, yaron “yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.” (1 Sama’ila 1:24; 2:11) Sa’ad da Sama’ila yake ɗan yaro, Jehobah ya yi magana da shi, kuma ya zartar da hukuncinsa a kan gidan Eli. Yayin da Sama’ila yake girma, dukan mutanen Isra’ila suka fahimci cewa shi annabin Jehobah ne.
Da shigewar lokaci, Filistiyawa suka zo su yaƙi Isra’ilawa. Suka ƙwace Akwatin alkawari kuma suka kashe ’ya’yan Eli su biyu. Da jin labarin, sai Eli tsoho ya mutu, “ya shekara arba’in yana shugabancin Isra’ila.” (1 Sama’ila 4:18) Riƙe Akwatin alkawarin ya zame wa Filistiyawa bala’i, saboda haka, sai suka mai da Akwatin ga Isra’ilawa. Sama’ila kuma ya zama shugaban Isra’ila, aka kuma sami salama a ƙasar.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:10—Me ya sa Hannatu ta yi addu’a ga Jehobah cewa ya “ba sarkinsa iko” sa’ad da babu mutumin da ke sarauta bisa Isra’ila? An riga an annabta a Dokar Musa cewa Isra’ilawa za su naɗa wa kansu sarki. (Maimaitawar Shari’a 17:14-18) A annabcin da ya yi a kan gadon mutuwarsa, Yakubu ya ce: “[Yahuza] yana riƙe da sandan mulkinsa [alamar iko na sarauta].” (Farawa 49:8-10) Bugu da ƙari, Jehobah ya ce game da Saratu, wadda ita ce kakar Isra’ilawa: “Sarakunan jama’a za su fito daga gare ta.” (Farawa 17:16) Saboda haka, Hannatu tana addu’a ne game da sarki na nan gaba.
3:3—Shin Sama’ila ya yi barci ne a wuri Mafi Tsarki? A’a. Sama’ila Balawi ne na iyalin Kohatawa waɗanda ba firist ba. (1 Tarihi 6:33-38) Domin haka, ba a amince masa ya shiga ya ga “tsarkakakkun abubuwa” ba. (Littafin Ƙidaya 4:17-20) Wuri mai tsarki da Sama’ila ke da ikon zuwa kawai shi ne farfajiyar mazauni. Ƙila wurin ne ya yi barci. Eli ma ya yi barci a wani wuri a cikin farfajiyar. Furcin nan “inda akwatin alkawarin Allah yake” babu shakka na nufin wuraren mazauni.
7:7-9, 17—Me ya sa Sama’ila ya yi hadaya ta ƙonawa a Mizfa kuma ya gina bagade a Rama, tun da yake kuma ana yin hadaya ne a kai a kai a inda Jehobah ya zaɓa kawai? (Maimaitawar Shari’a 12:4-7, 13, 14; Joshuwa 22:19) Bayan an cire Akwatin daga mazaunin da ke Shilo, sai bayanuwar Jehobah ya bar wajen. Saboda matsayinsa na wakilin Allah, Sama’ila ya yi hadaya ta ƙonawa a Mizfa kuma ya gina bagade a Rama. Babu shakka, Jehobah ya yarda da hakan.
Darussa Dominmu:
1:11, 12, 21-23; 2:19. Halin da Hannatu ta nuna na yin addu’a, da tawali’u, da godiyar da ta nuna wa alherin Jehobah, da kuma ƙauna ta uwa, duk abin koyi ne ga mata masu tsoron Allah.
1:8. Elkana ya kafa misali mai kyau ta ƙarfafa mutane da kalamai! (Ayuba 16:5) Da farko, ya tambayi Hannatu da take baƙin ciki wannan tambayar ba da zargi ba: “Me ya sa zuciyarki ta ɓaci?” Hakan ya ƙarfafa ta ta furta yadda take ji. Bayan haka, Elkana ya tabbatar mata da ƙaunar da yake yi mata, yana cewa: “Ni ban fi ’ya’ya maza goma a gare ki ba?”
2:26; 3:5-8, 15, 19. Idan muka manne wa aikin da Allah ya ba mu, kuma muka yi amfani da koyarwa na ruhaniya, kuma idan muka kasance da sauƙin kai da kuma ladabi, za mu dinga “samun tagomashi” a gaban Allah da kuma a gun mutane.
4:3, 4, 10. Ko da yake akwatin alkawari abu ne mai tsarki, ba maganin kāriya ba ne. Saboda haka, dole ne mu “yi nesa da gumaka.”—1 Yahaya 5:21.
SARKIN ISRA’ILA NA FARKO —NASARA NE KO KASAWA?
(1 Sama’ila 8:1–15:35)
Sama’ila ya kasance da aminci ga Jehobah a duk rayuwarsa, amma ’ya’yansa ba su bi hanyar ibada ba. Sa’ad da shugabannin Isra’ila suka ce suna so a naɗa musu sarki, Jehobah kuwa ya yarda da abin da suka ce. Sama’ila ya bi umurnin Jehobah, kuma ya naɗa Saul wanda kyakkyawa ne ɗan ƙabilar Biliyaminu a matsayin sarki. Saul ya ƙarfafa matsayinsa na sarki sa’ad da ya ci Ammonawa da yaƙi.
Ɗan Saul, Jonatan, ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa. Sai Filistiyawa suka taru da sojoji masu yawa don su yaƙi Isra’ila. Saul ya fara rawar jiki kuma cikin rashin biyayya, ya yi hadayar ƙonawa. Tare da mai ɗaukan masa makamai, Jonatan mai gaba gaɗi ya kai hari a sansanin Filistiyawa. Rantsuwar da Saul ya yi, ta rage yawan nasarar da suka yi. Saul ya yaƙi dukan abokan gābansa “da ke kewaye da shi.” (1 Sama’ila 14:47) Sa’ad da ya ci Amalekawa, ya yi rashin biyayya ga Jehobah domin ya ƙyale abin da ya kamata ya “kashe.” (Littafin Firistoci 27:28, 29) Saboda haka, sai Jehobah ya ƙi Saul a matsayin sarki.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
9:9—Menene ke da muhimmanci game da furcin nan “wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani”? Wataƙila wannan furcin na nuna cewa sa’ad da annabawa suka zama sanannu a lokacin Sama’ila da kuma zamanin sarakunan Isra’ila, an sauya furcin nan “maigani” da “annabi.” Sama’ila shi ne annabi na farko.—Ayyukan Manzanni 3:24.
14:24-32, 44, 45—Jonatan ya yi hasarar tagomashin Allah ne domin ya sha zuma wadda hakan ya haramta rantsuwar da Saul ya yi? Hakan bai sa Jonatan ya yi rashin tagomashin Allah ba. Na farko, Jonatan bai san cewa ubansa ya yi rantsuwa ba. Bugu da ƙari, kuzarin ƙarya ko kuwa mummunar ra’ayi na ikon sarauta ne ya Saul ya yi wannan rantsuwar, kuma hakan ya jawo wa mutanensa matsala. Yaya Allah zai yarda da irin wannan rantsuwar? Ko da yake Jonatan ya yarda ya karɓi sakamakon haramta rantsuwar da ubansa ya yi, amma an ceci ransa.
15:6—Me ya sa Saul ya yi wa Keniyawa alheri na musamman? Keniyawa ’ya’yan surukin Musa ne. Sun taimaka wa Isra’ilawa bayan sun bar Dutsen Sinai. (Littafin Ƙidaya 10:29-32) Kuma a ƙasar Ka’anan, Keniyawa sun zauna da ’ya’yan Yahuza na ɗan lokaci. (Littafin Mahukunta 1:16) Ko da yake sun ci gaba da zama tare da Amalekawa da kuma mutane dabam dabam, Keniyawa sun ci gaba da yin abuta da Isra’ila. Da kyakkyawan dalili Saul ya ceci Keniyawa.
Darussa Dominmu:
9:21; 10:22, 27. Filako da tawali’un da Saul ke da shi sa’ad da ya zama sarki, ya taimaka masa daga aikata abin da bai dace ba sa’ad da wasu “shashashan mutane” suka ƙi sarautarsa. Irin wannan hali na kasance kāriya daga aikata abu a hanyar da bai dace ba!
12:20, 21. Kada ka yarda abubuwa “marasa amfani,” irinsu amincewa da mutane, dogara ga ƙarfin sojojin ƙasa, ko bautar gumaka, su janye ka daga bauta wa Jehobah.
12:24. Abu mai muhimmanci da zai taimaka mana mu kasance da tsoron Jehobah da kuma bauta masa da zuciya ɗaya shi ne, “tuna da manyan al’amuran da ya yi” wa mutanensa a dā da kuma a zamani.
13:10-14; 15:22-25, 30. Ka kauce wa girman kai—ko ta wurin ayyuka na rashin biyayya ko kuwa fahariya.—Karin Magana 11:2.
AN ZAƁI YARO MAKIYAYI YA ZAMA SARKI
(1 Sama’ila 16:1–31:13)
Sama’ila ya shafa Dawuda ɗan ƙabilar Yahuza ya zama sarki na gaba. Ba da daɗewa ba, Dawuda ya kashe gwarzon Bafilisten nan Goliyat da ɗan ƙaramin dutse. Dawuda da Jonatan suka zama abokai na kud da kud. Saul ya mai da Dawuda ya zama shugaban sojojinsa. Domin nasarorin da Dawuda ya samu, sai matan Isra’ila suka fara raira waƙa: “Saul ya kashe dubbai, amma Dawuda ya kashe dubun dubbai.” (1 Sama’ila 18:7) Domin kishi, Saul ya nemi ya kashe Dawuda. Bayan Saul ya kai masa hari sau uku, sai Dawuda ya zama maguji yana ɓoye-ɓoye.
Sa’ad da yake gudu don ransa, Dawuda ya ceci ran Saul sau biyu. Ya haɗu da Abigail kyakkyawar mace, kuma daga baya ya aure ta. Sa’ad da Filistiyawa suka zo su yaƙi Isra’ila, Saul kuwa ya yi wa Jehobah tambaya. Amma Jehobah ya riga ya rabu da shi. Sama’ila kuma ya riga ya mutu. Domin ya matsu, sai Saul ya tafi wurin wata mai duba, kuma ta gaya masa cewa za a kashe shi a yaƙin da zai yi da Filistiyawa. A wajen yaƙin, Saul ya ji mummunan rauni, kuma aka kashe ’ya’yansa. Labarin ya ƙare da mutuwar Saul a matsayin wanda ya kasa. Kuma har yanzu Dawuda yana ɓoye.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
16:14—Wane mugun ruhu ne ya azabtar da Saul? Mugun ruhun da ke hana Saul samun kwanciyar hankali shi ne tunanin da ke zuciyarsa, na yin mugunta. Sa’ad da Jehobah ya cire ruhunsa mai tsarki daga Saul, ya yi hasarar kāriyar ruhu mai tsarki sai kuma mugun ruhu ya hau shi. Tun da Allah ne ya sauya wannan ruhun da ruhunsa mai tsarki, shi ya sa ake kiran wannan ruhun, “mugun ruhu” daga Jehobah.
17:55-58—Domin abin da ke 1 Sama’ila 16:17-23, me ya sa Saul ya yi tambaya cewa ɗan wanene Dawuda? Ba wai Saul ya yi wannan tambayar ba ne kawai domin ya san sunan baban Dawuda. Wataƙila yana son ya san kowanene mahaifin yaron da ya yi wannan abin mamaki na kashe wannan garzon.
Darussa Dominmu:
16:6, 7. Maimakon mu yarda kyaun siffa na wasu ya burge mu ko kuwa mu zartar da hukunci cikin sauri, bari mu ga mutane yadda Jehobah ke ganinsu.
17:47-50. Muna iya fuskantar hamayya ko tsanani daga maƙiya masu kama da Goliyat da gaba gaɗi, domin ‘yaƙin na Ubangiji ne.’
18:1, 3; 20:41, 42. Za a iya samun abokai na gaskiya a cikin waɗanda suke ƙaunar Jehobah.
21:12, 13. Jehobah yana so mu yi amfani da tunaninmu da kuma iyawarmu mu magance yanayi masu wuya a rayuwa. Ya ba mu hurarriyar Kalmarsa, wadda ke ba mu hikima, sani, da kuma basira. (Karin Magana 1:4) Muna kuma da taimako na dattawa Kiristoci da aka naɗa.
24:6; 26:11. Dawuda ya kafa misali mai kyau na girmama keɓaɓɓen Jehobah!
25:23-33. Basirar Abigail abin koyi ne.
28:8-19. Domin ƙoƙarin da suke yi su ɓad da mutane ko su cuce su, mugayen ruhu suna iya yin shigar wasu mutune da suka mutu. Dole ne mu guje wa kowane irin sihiri.—Maimaitawar Shari’a 18:10-12.
30:23, 24. Wannan shawarar da ke cikin Littafin Ƙidaya 31:27, ta nuna cewa Jehobah yana daraja waɗanda suke taimakawa a cikin ikilisiya. Ko menene muke yi, mu yi shi “da himma [muna] bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba.”—Kolosiyawa 3:23.
Menene Ya fi ‘Hadaya’?
Muhimmin gaskiyar da aka nanata a labarin Eli, Sama’ila, Saul, da Dawuda, shi ne: “Ya fi kyau a yi masa biyayya, da a miƙa masa hadayar tumaki mafi kyau. Gama tayarwa kamar zunubin bokanci yake. Taurinkai kuma kamar bautar gumaka yake.”—1 Sama’ila 15:22, 23.
Muna da gata mai girma na saka hannu a aikin wa’azi na Mulki a dukan duniya da kuma aikin almajirtarwa! Yayin da muke yabon Jehobah “da bakinmu,” dole ne mu yi ƙoƙarin mu bi umurnin da yake ba mu ta wurin rubutacciyar Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa da yake amfani da ita a duniya.—Yusha’u 14:2; Ibraniyawa 13:15.
[Hasiya]
a Domin gano wuraren da aka ambata a cikin littafin Sama’ila na Ɗaya, dubi shafuffuka na 18, 19 na mujallar nan “See the Good Land,” wadda Shaidun Jehobah ne suka wallafa.