Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 7/1 pp. 3-8
  • Ka Daraja Kyautar Rai Yadda Ya Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Daraja Kyautar Rai Yadda Ya Dace
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Daraja Rai
  • Ta Yaya Za a Yi Amfani da Jini Yadda Ya Dace?
  • Mai Ba da Rai Ya Warware Wani Batu
  • Ra’ayin Allah Game da Rai
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Mu Daraja Rai da Allah Ya Ba Mu Kyauta
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 7/1 pp. 3-8

Ka Daraja Kyautar Rai Yadda Ya Dace

“Jinin Almasihu . . . zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.”—IBRANIYAWA 9:14.

1. Wane tabbaci ne muke da shi cewa muna daraja rai?

IDAN aka tambaye ka cewa nawa ne kake ganin ranka za ta kai, wace amsa za ka ba da? Muna daraja ranmu sosai—namu da kuma na wasu. Tabbacin wannan shi ne za mu iya zuwan wajen likita ya bincika mu sa’ad da muke rashin lafiya ko kuwa a kowane lokaci mu je wurin likita yana bincika mu. Muna son mu kasance da rai da kuma koshin lafiya. Har yawancin waɗanda suka tsufa ko kuwa suka naƙasa ma ba sa son su mutu; suna son su kasance da rai.

2, 3. (a) Wane hakki ne Karin Magana 23:22 ta taƙaita? (b) Ta yaya ne hakkin da aka faɗa a Karin Magana 23:22 ya shafi Allah?

2 Yadda kake daraja ranka yana shafan dangantakarka da wasu. Alal misali, Kalmar Allah ta ce: “Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa’ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.” (Karin Magana 23:22) “Kasa kunne” tana nufin fiye da jin magana kawai; wannan karin magana tana nufin jin magana kuma a yi biyayya da ita. (Fitowa 15:26; Maimaitawar Shari’a 7:12; 13:18; 15:5; Joshuwa 22:2; Zabura 81:13) Wane dalili ne Kalmar Allah ta ba da na kasa kunne? Ba wai dan mahaifinka da mahaifiyarka sun girme ka ko kuwa domin sun fi ka sani ba. Dalilin da aka ba da, shi ne “da ba dominsa ba, da ba ka.” Wasu fassarar Littafi Mai Tsarki sun ce: “Ka kasa kunne ga mahaifinka wanda ya ba ka rai.” Babu shakka, idan ka daraja ranka, za ka cika hakkinka ga wanda ya ba ka rai.

3 Hakika, idan kai Kirista ne na gaskiya, za ka gane cewa Jehovah shi ne ainihin Tushen ranka. Domin a gare shi ne kake “rayuwa”; kake iya “motsi,” na mai rai; kuma ka “kasance” har ma kana iya yin tunani ko shiri don nan gaba, har ma na rai madawwami. (Ayyukan Manzanni 17:28; Zabura 36:9; Mai Hadishi 3:11) Daidai da Karin Magana 23:22, yana da kyau mu yi biyayya mu “kasa kunne” ga Allah, mu fahimta kuma mu bi ra’ayinsa game da yadda yake ɗaukan rai maimakon mu bi wani ra’ayi dabam.

Ka Daraja Rai

4. A farko cikin tarihin ’yan Adam, ta yaya ne daraja rai ya zama abu mai muhimmanci?

4 A farkon tarihin mutum, Jehovah ya bayyana cewa bai ƙyale mutane su yi amfani (ko kuwa su ci mutuncin) rai ba ko da wane dalili ne. Domin ya cika da fushi na kishi, Kayinu ya kashe marar laifi, ran ɗan’uwansa Habila. Kana ganin cewa Kayinu yana da ikon yanke irin wannan shawarar game da rai? Allah bai yi tunanin haka ba. Ya kama Kayinu da alhaki: “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan’uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.” (Farawa 4:10) Ka lura cewa jinin Habila da aka zubar a ƙasa yana wakiltan ransa, wanda aka gama da shi kafin lokacinsa, kuma ya yi ƙara wa Allah domin fansa.—Ibraniyawa 12:24.

5. (a) Menene Allah ya hana a zamanin Nuhu, kuma wa wannan ya shafa? (b) A wane azanci ne wannan doka take ɗauke da mataki mai muhimmanci?

5 Bayan Rigyawa, ’yan Adam suka fara sabuwar rayuwa da mutane takwas kawai. A cikin magana da ta shafi dukan mutane, Allah ya nuna yadda yake daraja rai da jini sosai. Ya ce mutane suna iya cin naman dabbobi, amma akwai abin da ya haramta: “Kowane abu mai motsi wanda ke da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome. Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa ke cikinsa, wato mushe.” (Farawa 9:3, 4) Wasu Yahudawa sun ce wannan yana nufin cewa Allah bai yarda mutane su ci nama da jini na dabba wadda ke raye ba. Amma daga baya an nuna sarai cewa Allah a nan ya hana yin amfani da jini ne domin kiyaye rai. Ban da haka, dokar da Allah ya ba da ta wurin Nuhu mataki ne na musamman domin ya cika babban manufarsa da ta shafi jini—manufa da za ta sa mutane su sami rai madawwami.

6. Ta yaya ne Allah ya nanata yadda ya ɗauki rai da daraja ta wurin Nuhu?

6 Allah ya ci gaba: “Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan’uwansa. Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.” (Farawa 9:5, 6) A nan, kana iya ganin bayani ga dukan iyalin ’yan Adam cewa Allah yana ɗaukan jinin mutum a matsayin ransa. Mahalicci ya ba mutum rai, kuma kada wani ya ɗauke ran, wanda yake wakilta jini. Idan wani ya kashe mutum, yadda Kayinu ya yi, Mahalicci yana da ikon ya “hukunta” mai kisan.

7. Me ya sa ya kamata mu so abin da Allah ya gaya wa Nuhu game da jini?

7 Ta wurin abin da Allah ya faɗa yana gaya wa mutane kada su yi wasa da jini ne. Ka taɓa mamakin dalilin haka? Menene dalilin da ya sa Allah yake ɗaukan jini haka? Hakika, amsar ta shafi wata muhimmiyar koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan koyarwa ita ce muhimmiyar saƙon Kirista, ko da yake yawancin ƙungiyoyin addinai sun ƙi saƙon. Mecece wannan koyarwa, kuma yaya wannan ta shafi ranka, shawararka, da kuma ayyukanka?

Ta Yaya Za a Yi Amfani da Jini Yadda Ya Dace?

8. A cikin doka, wace iyaka Jehovah ya bayar game da yin amfani da jini?

8 Jehovah ya ba da ƙarin bayani game da rai da jini sa’ad da ya ba Isra’ila Dokar Musa. Sa’ad da yake cikin yin haka, ya ɗauki matakai domin cika manufarsa. Ƙila ka san cewa dokar ta bukaci yi wa Allah hadayu, kamar su hatsi, mai, da kuma giya. (Littafi Firistoci 2:1–4; 23:13; Littafin Ƙidaya 15:1–5) Akwai kuma hadayun dabbobi. Allah ya ce game da wannan: “Ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa. Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra’ila, cewa kada wani daga cikinsu . . . ya ci jini.” Jehovah ya ƙara cewa, idan wani, kamar maharbi ko kuwa manomi, ya kashe dabba domin ya ci, dole ne ya zubar da jinin ya kuma rufe shi da ƙasa. Duniya ce ƙarƙashin matashin sawun Allah, ta wurin zubar da jinin a ƙasa, mutumin ya nuna cewa ran ya koma wurin Mai ba da Rai.—Littafin Firistoci 17:11–13; Ishaya 66:1.

9. Menene ainihin amfanin jini yadda aka nuna a cikin Doka, kuma mecece manufar wannan?

9 Wannan dokar ba abar da za ka yi kawai ta addini wanda ba shi da ma’ana a gare mu ba. Ka lura da dalilin da ya sa aka ce kada Isra’ilawa su ci jini? Allah ya ce: “Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra’ila, cewa kada wani daga cikinsu . . . ya ci jini.” Saboda me? “Domin Ubangiji kuwa ya ba su [jini] a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara.” Ka ga cewa wannan ya ba da bayani game da dalilin da ya sa Allah ya gaya wa Nuhu cewa kada mutane su ci jini? Mahaliccin ya ɗauki jini da muhimmanci, domin amfani na musamman da zai cetar da rayukan mutane. Jini yana da muhimminci don yafe zunubanmu (wato, yin kafara). Saboda haka, a ƙarƙashin Doka, inda Allah ya yarda a yi amfani da jini shi ne a kan bagade kaɗai domin a yi kafarar rayukan Isra’ilawa, waɗanda suke son Jehovah ya gafarta musu.

10. Me ya sa jinin dabba ba ya iya kawo cikakkiyar gafara, amma wace tunasarwa hadayu ke yi a ƙarƙashin Dokar?

10 Babu bambanci tsakanin wannan ra’ayin da Kiristanci. Sa’ad da yake nuni ga wannan hurarren tsari na Doka, Kirista manzo Bulus ya rubuta: “Kusan dukan abu da jini ake tsarkaka shi, in ba game da zubar da jini ba kuwa, ba gafara.” (Ibraniyawa 9:22) Bulus ya bayyana cewa bukatun hadayu bai mai da Isra’ilawa kamiltattun mutane, marasa zunubi ba. Ya rubuta: “Game da irin waɗannan hadayu, a kan tuna da zunubai a kowace shekara, domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bajimai da na awaki ya ɗauke zunubi.” (Ibraniyawa 10:1–4) Duk da haka, irin waɗannan hadayu suna da amfani. Sun tuna wa Isra’ilawa cewa su masu zunubi ne da ke bukatar wani abu domin a yafe musu zunubinsu gabaki ɗaya. Amma idan jinin da ke wakiltar rayukan dabbobi bai iya kawar da zunuban mutane gabaki ɗaya ba, akwai wani jinin da zai iya yin haka?

Mai Ba da Rai Ya Warware Wani Batu

11. Ta yaya muka sani cewa hadayu na dabbobi suna nuni ga wani abu?

11 Dokar tana nuni ga wani abu mai girma mai inganci don cika nufin Allah. Bulus ya yi tambaya: “To, mecece manufar shari’a?” Ya amsa: “Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala’iku ne, ta hannun matsakanci [Musa].” (Galatiyawa 3:19) Haka nan, Bulus ya rubuta: “Shari’a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da ke gaba, ba ainihin siffarsu ba.”—Ibraniyawa 10:1.

12. Game da jini, ta yaya ne za mu iya ganin aukuwa da za ta nuna manufar Allah?

12 A taƙaice, ka tuna cewa a zamanin Nuhu Allah ya ba da doka cewa mutane suna iya cin naman dabbobi don rayuwa, amma kada su ci jini. Bayan haka, Allah ya faɗi cewa “ran nama yana cikin jinin.” Hakika, yana ɗaukan jini a matsayin rai shi ya sa ya ce: “Ubangiji kuwa ya ba su [jini] a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara.” Ko da yake, akwai aukuwa ta ban mamaki da za ta nuna manufar Allah. Dokar ta alamta wani abu mai kyau da zai zo. Menene?

13. Me ya sa mutuwar Yesu take da muhimmanci?

13 Gaskiya ce game da mutuwar Yesu Kristi. Ka san cewa an gana wa Yesu azaba kuma an kafa shi. Ya yi mutuwar mai laifi. Bulus ya rubuta: “Tun muna raunana tukuna, Almasihu ya mutu a daidaitaccen lokaci domin marasa bin Allah. . . . Allah na tabbatar mana da ƙaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.” (Romawa 5:6, 8) Ta wurin mutuwarsa dominmu, Kristi ya ba da fansa domin a yafe zunubanmu. Wannan fansa ita ce muhimmiyar saƙon Kirista. (Matiyu 20:28; Yahaya 3:16; 1 Korantiyawa 15:3; 1 Timoti 2:6) Wace nasaba ce ke tsakanin jini da rai, kuma yaya ta shafi ranka?

14, 15. (a) Ta yaya ne wasu fassara na Afisawa 1:7 suka sa nanaci a kan mutuwar Yesu? (b) Wace gaskiya ce game da Afisawa 1:7 ƙila ba za mu lura da ita ba?

14 Wasu coci suna nanata mutuwar Yesu, mabiyansu suna faɗin wasu abubuwa kamar “Yesu ya mutu domina.” Ka yi la’akari da yadda wasu juyin Littafi Mai Tsarki suka fassara Afisawa 1:7: “Ta wurinsa kuma ta mutuwarsa muka sami ceto, wato, yafewar laifuffukanmu.” (The American Bible, by Frank Scheil Ballentine, 1902) “Ta wurin mutuwar Kristi an ’yantar da mu, kuma an yafe mana zunubanmu.” (Today’s English Version, 1966) “Ta wurin Kristi da kuma hadayar ransa ne muka sami ’yanci, ’yanci da yake nufin gafarar zunubai.” (The New Testament, na William Barclay, 1969) “Ta wurin mutuwar Kristi ne aka yafe mana zunubanmu kuma muka sami ’yanci.” (The Translator’s New Testament, 1973) Ka ga yadda waɗannan fassarar suka nanata mutuwar Yesu. ‘Amma,’ wasu suna iya cewa, ai mutuwar ‘Yesu’ tana da muhimmanci sosai. Menene aka yi rashinsa a cikin waɗannan fassarar?’

15 Hakika, idan ka dogara da waɗannan fassarar, wataƙila ba za ka lura da wani batu mai muhimmanci ba, kuma wannan yana iya rage fahiminka na saƙon Littafi Mai Tsarki. Irin waɗannan fassarar sun ɓoye gaskiyar cewa furci na asali na Afisawa 1:7 da ya ƙunshi kalmar Helenanci, da take nufin “jini.” Shi ya sa, wasu fassara ta Littafi Mai Tsarki sun yi kusa da na asali, kamar su Littafi Mai Tsarki na Hausa: ‘Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah.’

16. Mecece fassarar nan “jininsa” take tunasar mana?

16 Fassarar nan “jininsa” tana da muhimmiyar manufa kuma wannan tana sa mu yi tunanin fasalolin da suka shafi jini. Mutuwar wani kawai bai isa ba, har ma mutuwar kamiltaccen mutum Yesu. Ya cika abin da Doka take hotanta, musamman a Ranar Kafara. A wannan babbar rana, ana ba da hadayu na dabbobin da doka ta faɗa. Bayan haka, babban firist zai ɗauka daga cikin jinin ya kai cikin wuri Mafi Tsarki na mazauni ko kuwa na haikali, a wurin zai miƙa shi a gaban Allah, kamar yana ganinsa a zahiri.—Fitowa 25:22; Littafin Firistoci 16:2–19.

17. Ta yaya ne Yesu ya cika abin da Ranar Kafara take hotonta?

17 Yesu ya cika abin da Ranar Kafara take alamtawa, yadda Bulus ya bayyana. Da farko, ya bayyana cewa babban firist a Isra’ila yana shiga wuri Mafi Tsarki da jini sau ɗaya a shekara, wanda yakan miƙa “saboda kansa, da kuma kurakuran jama’a.” (Ibraniyawa 9:6, 7) Daidai da wannan tsarin, Yesu ya wuce sama bayan ya tashi a matsayin ruhu. A matsayin ruhu domin ba shi da jikin nama da jini, ya iya bayyana “a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.” Menene ya miƙa wa Allah? Ba wani abu na zahiri ba ne amma abu mai ma’ana ne. Bulus ya ci gaba: “Almasihu ya riga ya zo yana babban firist . . . , Almasihu ya shiga wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ba ƙari, ba kuwa ta jinin awaki ko na ’yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa. To jinin awaki ne fa da na bajimai . . . suke tsarkake su da tsabtacewar jiki, balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta Madawwamin Ruhu, lallai zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.” Hakika, Yesu ya miƙa wa Allah tamanin jinin ransa.—Ibraniyawa 9:11–14, 24, 28; 10:11–14; 1 Bitrus 3:18.

18. Me ya sa furci na Littafi Mai Tsarki game da jini yake da muhimmanci ga Kiristoci a yau?

18 Wannan gaskiya daga Allah ya sa mu fahimta dukan abin mamaki da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da jini—abin da ya sa Allah yake ɗaukansa da muhimmanci haka, yadda ya kamata mu ɗauke shi, da kuma dalilin da ya sa za mu daraja hani da Allah ya yi game da yin amfani da jini. Sa’ad da kake karatun Nassosin Kirista na Helenanci, za ka ga hasiyoyi masu yawa game da jinin Kristi. (Ka duba akwati.) Wannan ya nuna sosai cewa dole ne kowane Kirista ya ba da gaskiya ga ‘jinin [Yesu].’ (Romawa 3:25) Samun gafara da kuma salama da Allah za ta yiwu ne kaɗai ta ‘jinin [Yesu].’ (Kolosiyawa 1:20) Wannan gaskiya ne game da waɗanda Yesu ya yi alkawari na musamman da su da za su yi mulki tare da shi a sama. (Luka 22:20, 28–30; 1 Korantiyawa 11:25; Ibraniyawa 13:20) Wannan gaskiya ne game da “ƙasaitaccen taro” a yau, waɗanda za su tsira daga “matsananciyar wahala” da ke tafe nan gaba kuma su ji daɗin rai madawwami a cikin aljanna a duniya. A alamance, sun ‘wanke rigunansu da jini na Ɗan Rago.’—Wahayin Yahaya 7:9, 14.

19, 20. (a) Me ya sa Allah ya hana yin amfani da jini, kuma yaya ya kamata mu ji game da wannan? (b) Saboda haka, menene ya kamata mu so mu sani?

19 A bayyane, jini yana da ma’ana a gaban Allah. Haka nan mu ma. Mahalicci, wanda yake kula da rai, yana da iko ya hana mutane yin amfani da jini. Cikin kulawar shi har ma game da ranmu, ya ƙudura ya ajiye jini domin yin amfani da shi a muhimmiyar hanya, hanya kaɗai da za a sami rai madawwami. Wannan hanyar ta ƙunshi jinin Yesu mai tamani. Muna godiya cewa Jehovah Allah ya aikata domin amfaninmu ta yin amfani da jini—jinin Yesu—a wannan hanya ta ceton rai! Kuma muna godiya ga Yesu domin hadayar da ya yi ta zubar da jininsa dominmu! Hakika, za mu iya fahimtar abin da manzo Yahaya ya furta: “Ga wanda ke ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta jininsa—ya maida mu firistoci mallakar Allah Ubansa. Amin.”—Wahayin Yahaya 1:5, 6.

20 Allahnmu mafi hikima Mai Ba da Rai da daɗewa yana da wannan aiki na ceton rai a zuciyarsa. Muna iya tambaya cewa, ‘Yaya wannan zai shafi shawararmu da halinmu?’ Talifi na gaba zai tattauna wannan tambayar.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene za mu koya game da yadda Allah ya ɗauki jini a batun da ya shafi Habila da Nuhu?

• A cikin Doka, wace iyaka Allah ya sa game da yin amfani da jini, kuma me ya sa?

• Ta yaya Yesu ya cika abin da aka alamta da Ranar Kafara?

• Ta yaya ne jinin Yesu zai iya ceton ranmu?

[Akwati a shafi na 7]

JININ WANENE YAKE CETON RAYUKA?

“Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon ikilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jinin [ɗansa].”—Ayyukan Manzanni 20:28.

“To, tun da ya ke yanzu an kuɓutar da mu ta jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan.”—Romawa 5:9.

“Marasa sa zuciya, marasa Allah kuma a duniya. Amma yanzu, cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.”—Afisawa 2:12, 13.

“Dukkan cikar Allah ta tabbata, domin Allah na farin ciki da haka, da nufin ta wurinsa Allah ya sulhunta dukkan abubuwa da shi kansa . . . yana ƙulla zumunci ta jininsa na [gungumen azaba].”—Kolosiyawa 1:19, 20.

“Saboda haka ya ’yan’uwa, . . . muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu.”—Ibraniyawa 10:19.

“An fanshe ku ne daga al’adunku na banza da wofi da kuka gadā, ba da abubuwa masu lalacewa ba . . . sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo.”—1 Bitrus 1:18, 19.

“In kuwa muna zaune a haske kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.”—1 Yahaya 1:7.

“Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa, domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama’a, da kowace al’umma.”—Wahayin Yahaya 5:9.

“An jefa mai ƙarar ’yan’uwanmu ƙasa . . . Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida.”—Wahayin Yahaya 12:10, 11.

[Hoto a shafi na 5]

Ta wurin Doka, Allah ya nuna cewa jini yana da muhimmanci a wajen yafe zunubai

[Hoto a shafi na 6]

Ta wurin jinin Yesu, rayuka da yawa za su iya samun ceto

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba