Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 6/1 p. 28-p. 31 par. 8
  • Taƙaici Daga Littafin Farawa—na II

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taƙaici Daga Littafin Farawa—na II
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • IBRAHIM YA ZAMA ABOKIN ALLAH
  • (Farawa 11:10–23:20)
  • YAKUBU YANA DA ’YA’YA MAZA 12
  • (Farawa 24:1–36:43)
  • JEHOVAH YA ALBARKACI YUSUFU A MASAR
  • (Farawa 37:1–50:26)
  • Suna da Bangaskiya Mai Jimrewa
  • Allah Ya Albarkaci Ibrahim da Iyalinsa
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Jehobah Ne “Allah Mai Ba Da Salama”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Daga Tufana Zuwa Ceto Daga Ƙasar Masar
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 6/1 p. 28-p. 31 par. 8

Maganar Jehovah Rayayyiya Ce

Taƙaici Daga Littafin Farawa—na II

DAGA halittar mutum na farko Adamu zuwa mutuwar Yusufu ɗan Yakubu, littafin Farawa ya yi maganar tarihin ’yan Adam na shekaru 2,369. An tattauna surori 10 na farko da kuma ayoyi 9 na sura 11, ya haɗa da labarin halitta zuwa hasumiya ta Babel a fitowar Afrilu na wannan jarida. Wannan talifin ya bayyana taƙaici na sauran littafin Farawa, game da yadda Allah ya yi sha’ani da Ibrahim, Ishaƙu, Yakubu, da Yusufu.

IBRAHIM YA ZAMA ABOKIN ALLAH

(Farawa 11:10–23:20)

Shekaru 350 bayan Rigyawar, an haifi mutum da Allah yake so sosai a zuriyar ɗan Nuhu, Shem. Sunansa Abram ne, daga baya aka canja zuwa Ibrahim. Da Allah ya umurce shi, Abram ya bar birnin Chaldiya na Ur kuma ya zama mai zama a tanti a ƙasar da Jehovah ya yi alkawari zai ba shi da zuriyarsa. Domin bangaskiyarsa da kuma biyayya, aka soma kiran Ibrahim “abokin Allah.”—Yaƙub 2:23.

Jehovah ya halaka miyagun mazaunan Saduma da birane kusa da ita, amma ba abin da ya sami Lutu da ’ya’yansa mata. Wani alkawarin Allah ya cika sa’ad da aka haifi Ishaƙu ɗan Ibrahim. Shekaru da yawa bayan haka, Jehovah ya gwada bangaskiyar Ibrahim sa’ad da ya gaya masa ya ba da wannan ɗan don hadaya. Ibrahim yana shirye ya yi biyayya amma mala’ika ya hana shi. Babu shakka cewa Ibrahim mutum ne mai bangaskiya, kuma an tabbatar masa cewa ta wurin zuriyarsa dukan al’ummai za su yi albarka. Mutuwar matarsa ƙaunatacciya, Saratu, ta sa Ibrahim baƙin ciki sosai.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

12:1-3—Yaushe alkawarin da aka yi da Ibrahim ya soma, kuma har yaushe? A bayyane yake cewa an soma amfani da alkawari da Jehovah ya yi da Abram cewa “a cikin [Abram] dukan ƙabilan duniya za su yi albarka” sa’ad da Abram ya ketare Yufiretis a hanyarsa zuwa Kan’ana. Wannan ya faru a 14 ga Nisan, shekara ta 1943 K.Z.—shekaru 430 kafin a ‘yantar da Isra’ila daga Masar. (Fitowa 12:2, 6, 7, 40, 41) Alkawari da aka yi da Ibrahim “alkawari madawwami” ne. Yana ci gaba har sai iyalai na duniya sun sami albarka a halaka dukan magabtan Allah kuma.—Farawa 17:7; 1 Korinthiyawa 15:23-26.

15:13—Yaushe ne wahala na shekara 400 da aka annabta zuriyar Abram za su sha ta cika? Wannan lokacin wahala ya soma a shekara ta 1913 K.Z., sa’ad da aka yaye ɗan Ibrahim Ishaƙu a shekararsa ta 5 kuma ɗan ubansa Ishmael mai shekara 19 ‘yana masa ba’a.’ (Farawa 21:8-14; Galatiyawa 4:29) Ya kai ƙarshensa sa’ad da aka ’yantar da Isra’ilawa ne daga bauta a Masar a shekara ta 1513 K.Z.

16:2—Ya dace ne da Saraya ta ba Abram baranyarta Hajaratu, ta zama matarsa? Abin da Saraya ta yi ya yi daidai da al’ada na lokacin—cewa ya kamata bakararriya ta ba mai gidanta ƙwarƙwara domin a haifi magaji. Ana auren mace fiye da ɗaya a zuriyar Kayinu. Bayan haka, ya zama al’ada kuma wasu masu bauta wa Jehovah suka soma yin haka. (Farawa 4:17-19; 16:1-3; 29:21-28) Amma, Jehovah bai yasar da mizani na asali ba na auren mace guda. (Farawa 2:21, 22) Nuhu da ’ya’yansa maza da aka maimaita wa umurni su ‘yalwata da ’ya’ya su kuma mamaye duniya’ babu shakka sun auri mata ɗaɗɗaya. (Farawa 7:7; 9:1; 2 Bitrus 2:5) Yesu Kristi ya sake furta wannan mizani na auren mace guda.—Matta 19:4-8; 1 Timothawus 3:2, 12.

19:8—Lutu ya yi laifi ne da ya ba ’yan Saduma ’ya’yansa mata? Bisa ƙa’ida na ƙasashen Gabas, hakkin mai gidan ne ya kāre baƙi da ke gidansa, ya goyi bayansu har mutuwa idan ta kama haka. Lutu a shirye yake ya yi hakan. Da gaba gaɗi ya fita waje ya tari taron ‘yan banza, ya rufe kofa don shi kaɗai ya fuskance su. Lokacin da ya ba da ’ya’yansa mata, Lutu wataƙila ya fahimci cewa baƙinsa manzanni ne daga Allah, kuma mai yiwuwa ya yi tunani cewa Allah zai iya tsare ’ya’yansa mata yadda Ya tsare gwaggonsa Saratu a Masar. (Farawa 12:17-20) Hakika, yadda batun ya juya, an tsare Lutu da ’ya’yansa mata.

19:30-38—Jehovah ya yi na’am da yadda Lutu ya yi maye kuma ya samu ‘ya’ya maza ta wurin ‘ya’yansa mata biyu? Jehovah ba ya na’am da jima’i tsakanin dangi ko kuwa yin maye. (Leviticus 18:6, 7, 29; 1 Korinthiyawa 6:9, 10) Lutu ya ƙi da “ayyuka . . . marasa-shari’a” na mazaunan Saduma. (2 Bitrus 2:6-8) Da yake ’ya’yan Lutu mata sun sa ya yi maye yana nuna cewa sun sani ba zai yarda ya yi jima’i da su da saninsa ba. Amma, tun da yake su baƙi ne a ƙasar, ’ya’yansa mata suna jin cewa wannan ce kaɗai hanya da za a tuna da iyalin Lutu. An rubuta labarin cikin Littafi Mai Tsarki don a bayyana dangantakar Mowabawa (ta zuriyar Mowab) da Ammoniyawa (ta zuriyar Benammi) da zuriyar Ibrahim, Isra’ilawa.

Darussa da Za Mu Koya:

13:8, 9. Ibrahim ya ba da misali mai kyau na bi da jayayya! Kada mu daina dangantaka na salama domin muna son riba ta kuɗi, abubuwa da muka fi so, ko kuma fahariya.

15:5, 6. Sa’ad da Ibrahim yake tsufa kuma ba shi da ɗa, ya yi wa Allah magana game da batun. Jehovah kuma ya ba shi tabbaci. Menene sakamakon? Ibrahim ya “bada gaskiya ga Ubangiji.” Idan muka gaya wa Jehovah zuciyarmu cikin addu’a, muka amince da tabbacinsa cikin Littafi Mai Tsarki, muka yi masa biyayya, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi.

15:16. Jehovah bai zartar da hukuncinsa ba a kan Amoriyawa (ko, Kan’aniyawa) har tsara huɗu. Me ya sa? Domin shi Allah ne mai haƙuri. Ya jira har sai babu begen za su yi gyara. Kamar Jehovah, muna bukatar mu riƙa haƙuri.

18:23-33. Jehovah ba ya halaka mutane ba ji ba gani ba. Yana kāre adalai.

19:16. Lutu ya yi ta “nauwa” kuma mala’ikun suka jawo shi da iyalinsa daga cikin birnin Saduma. Zai yi kyau kada mu yi rashin azancin gaggawa yayin da muke jiran ƙarshen muguwar duniya.

19:26. Wauta ce abin da muka bari a duniya su janye hankalinmu ko mu yi sha’awarsu!

YAKUBU YANA DA ’YA’YA MAZA 12

(Farawa 24:1–36:43)

Ibrahim ya shirya Ishaƙu ya auri Rifkatu, mace da take da bangaskiya ga Jehovah. Ta haifi tagwaye Isuwa da Yakubu. Isuwa ya rena matsayinsa na ɗan fari kuma ya sayar wa Yakubu, wanda daga baya ya samu albarkar babansa. Yakubu ya gudu zuwa Fadan-aram, inda ya auri Lai’atu da Rahila kuma ya yi kiwon garken babansu na shekara 20 kafin ya bar wajen da iyalinsa. Ta wajen Lai’atu, Rahila, da barorinsu biyu, Yakubu yana da ‘ya’ya maza 12 da kuma ‘ya’ya mata. Yakubu ya yi kokawa da mala’ika kuma aka albarkace shi, aka canja sunansa zuwa Isra’ila.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

28:12, 13—Menene ma’anar mafarkin Yakubu game da “tsani”? Wannan “tsani,” da ƙila ya yi kama da matakala na dutse ya nuna cewa akwai sadawa tsakanin duniya da sama. Cewa mala’ikun Allah suna hawa da sauƙowa a kansa yana nuna cewa mala’iku suna hidima a wasu muhimman hanyoyi tsakanin Jehovah da ‘yan Adam da suke da amincewarsa.—Yohanna 1:51.

30:14, 15—Me ya sa Rahila ta ba da zarafin mijinta ya shigo wurinta don ta samu manta’uwa? A lokacin dā, ana amfani da ’ya’yan itacen manta’uwa don maganin barci ko sauƙaƙa tsotsuwar zuciya. An ce ’ya’yan itacen yana iya ta da sha’awar jima’i da kuma ƙara iya haihuwa ko taimaka a ɗaukan ciki. (Waƙar Waƙoƙi 7:13) Ko da Littafi Mai Tsarki bai faɗa abin da ya sa Rahila ta yi wannan musanyar ba, wataƙila ta yi tunanin cewa manta’uwa za ta taimake ta ta yi ciki kuma ya kawo ƙarshen zargin zama bakararriya. Amma, an yi wasu shekaru kafin Jehovah “ya buɗe cikinta.”—Farawa 30:22-24.

Darussa da Za Mu Koya:

25:23. Jehovah yana iya sanin halin jariri da ba a haifa ba, ya nuna sanin gaba kuma ya zaɓa tun da wuri wanda zai cika ƙudurinsa. Duk da haka ba ya ƙaddara ƙarshen mutane ba.—Hosea 12:3; Romawa 9:10-12.

25:32, 33; 32:24-29. Damuwar Yakubu game da samun matsayin ɗan fari da kuma kokawa dukan dare da mala’ika don ya sami albarka ya nuna da gaske yana daraja abubuwa na ruhaniya. Jehovah ya danƙa mana abubuwa na ruhaniya da yawa, kamar dangantakarmu da shi da ƙungiyarsa, fansa, Littafi Mai Tsarki, da kuma begenmu na Mulki. Bari mu zama kamar Yakubu a nuna godiya game da su.

34:1, 30. ‘Wahala’ da Yakubu ya sha ya soma domin Dinatu ta yi abokantaka da mutane da ba sa ƙaunar Jehovah. Dole mu zaɓi abokai masu kyau.

JEHOVAH YA ALBARKACI YUSUFU A MASAR

(Farawa 37:1–50:26)

Kishi ya sa ’ya’yan Yakubu maza suka sayar da ɗan’uwansu Yusufu zuwa bauta. A Masar an sa Yusufu a kurkuku domin ya manne wa mizanan ɗabi’a na Allah cikin aminci da gaba gaɗi. Da shigewar lokaci, aka cire shi daga kurkuku don ya faɗi ma’anar mafarkin Fir’auna, da ya annabta shekaru bakwai na yawan abinci kuma bayan haka za a yi shekara bakwai na yunwa. Aka sa Yusufu ya zama shugaban masu ba da abinci a Masar. ’Yan’uwansa suka zo neman abinci a Masar domin yunwa. Iyalin ta sake haɗuwa kuma suka zauna a ƙasar Goshen mai ni’ima. Da yake bakin mutuwa, Yakubu ya albarkaci ’ya’yansa maza kuma ya furta annabci da ya ba da tabbataccen begen albarka mai yawa a ƙarnuka nan gaba. An binne jikin Yakubu a Kan’ana. Sa’ad da Yusufu ya mutu a shekararsa ta 110, aka sa kada jikinsa ya ruɓa, bayan haka aka kai Ƙasar Alkawari.—Fitowa 13:19.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

43:32—Me ya sa cin abinci tare da Ibraniyawa abin ƙyama ne ga Masarawa? Wannan mai yiwuwa domin wariya na addini ne ko fahariya na ƙabila. Masarawa ba sa son maƙiyaya. (Farawa 46:34) Me ya sa? Ƙila maƙiyaya a Masar matsiyata ne. Ko kuma tun da yake ƙasar noma da suke da ita kaɗan ne, Masarawa ba sa son waɗanda suke neman wurin kiwon garke.

44:5—Yusufu da gaske ya yi amfani da kōfi domin ya yi ishara? Kōfi na azurfa da abin da aka faɗa game da shi mai yiwuwa ruɗu ne. Yusufu mai bauta wa Jehovah da aminci ne. Bai yi amfani da kōfin don ya yi ishara ba, yadda Banyamin bai sace shi ba da gaske.

49:10—Menene ma’anar “Kandirin” da “sandar mai-mulki”? Kandiri ƙaramin sanda ne da sarki yake riƙewa da ke nuna alamar ikon sarauta. Sandar mai mulki doguwa ce da ke nuna ikonsa na ba da umurni. Yakubu ya ambata wannan don ya nuna cewa iko na musamman zai kasance da ƙabilar Yahuda har zuwan Shiloh. Yesu Kristi ne wannan zuriyar Yahuda, wanda Jehovah ya ba wa sarautar samaniya. Kristi yana da ikon sarauta da ikon ba da umurni.—Zabura 2:8, 9; Ishaya 55:4; Daniel 7:13, 14.

Darussa da Za Mu Koya:

38:26. Yahuda bai aikata da kyau ba a sha’aninsa da surukuwarsa gwauruwa, Tamar. Amma, da aka gaya masa shi ya ba ta ciki, Yahuda cikin tawali’u ya yarda da kuskurensa. Mu ma ya kamata mu yi saurin yarda da kuskurenmu.

39:9. Amsar da Yusufu ya ba matar Fotifa ta nuna cewa tunaninsa ya yi daidai da na Allah a batun ɗabi’a kuma cewa ƙa’idodi na ibada ne suke ja-gorar lamirinsa. Bai kamata mu ma mu yi ƙoƙari mu yi hakan yayin da muka ƙara samun cikakken sani na gaskiya ba?

41:14-16, 39, 40. Jehovah yana iya canja yanayin waɗanda suke tsoronsa. Sa’ad da masifa ta same mu, zai yi kyau mu dogara ga Jehovah kuma mu kasance da aminci gare shi.

Suna da Bangaskiya Mai Jimrewa

Hakika, Ibrahim, Ishaƙu, Yakubu, da Yusufu mutane masu tsoron Allah ne da suke da bangaskiya. Labari game da rayuwarsu, da ke cikin littafin Farawa, yana ƙarfafa bangaskiya kuma ya koya mana darussa da yawa masu amfani.

Za ka amfana daga wannan labarin yayin da kake da aiki na karatun Littafi Mai Tsarki a Makarantar Hidima ta Allah. Yin la’akari da labarin zai sa ya zama hakika.

[Hoto a shafi na 28]

Jehovah ya albarkaci Yusufu

[Hoto a shafi na 28]

Ibrahim mutumi ne mai bangaskiya

[Hoto a shafi na 28]

An ceci Lutu adali da ’ya’yansa mata

[Hoto a shafi na 31]

Yakubu ya daraja abubuwa na ruhaniya. Kana yin haka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba