Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 7/1 pp. 4-7
  • Yadda Za a Koya Ƙauna ta Gaske

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Koya Ƙauna ta Gaske
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Koyar ta Wurin Misali
  • Yadda Duka Za Su Iya Koya Ƙauna
  • Hurarriyar Ja-Gora ta Uba
  • Ƙauna—’Yar Ruhun Allah
  • Ka Koyi Ƙauna Daga ’Yan’uwanci na Kirista
  • “Ƙauna Ba ta Ƙarewa Daɗai”
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kauna​—Hali ne Mai Muhimmanci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
  • A Ina Ƙaunarka Ta Tsaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 7/1 pp. 4-7

Yadda Za a Koya Ƙauna ta Gaske

“Ƙauna maganin rai ne; ƙauna rai ce.”—Living to Purpose, na Joseph Johnson, 187.

YAYA ɗan Adam ke koya ya nuna ƙauna? Ta wurin koyon halin mutum ne? Ta wurin karatun littattafan ba da taimako ne? Ta wurin kallon siliman ne na soyayya? Da ƙyar. Ta wurin misali da kuma renon iyayensu ne bil adama ke koya ƙauna a farko. Yara za su koya ma’anar ƙauna idan, a yanayin soyayya, suna ganin iyayensu suna ciyar kuma kāre su, suna magana da su, kuma suna nuna sonsu sosai. Suna kuma iya koya ƙauna sa’ad da iyayensu suka koyar musu su kiyaye wasu ƙa’idodi na nagarta da mugunta.

Ƙauna ta gaske ba da’awar soyayya ko kuma zakin baki kawai ba ce. Tana aikawa domin abin da wasu suke so, ko idan ba su so haka ba a lokacin, yadda yake ne sa’ad da aka yi wa yara horo ta ƙauna. Kamiltaccen misali na wanda yake nuna ƙauna marar son kai ne Mahalicci kansa. Manzo Bulus ya rubuta: “Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji, Kada ka suma kuma sa’anda ka sami tsautawa gareshi; Gama wanda Ubangiji ke ƙauna shi ya ke horo.”—Ibraniyawa 12:5, 6.

Iyaye, ta yaya za ku yi koyi da Jehovah a nuna wa iyalinku ƙauna? Yaya muhimmancin misalin da kuka kafa a dangantakarku ta mata da miji yake?

Ku Koyar ta Wurin Misali

Idan kai miji ne, kana ɗaukaka, ko kuma ɗauka matarka da tamani sosai, kana bi da ita cikin daraja da ladabi? Idan ke mata ce, kina ƙaunar kuma goyon bayan mijinki? Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata mata da miji su ƙaunace kuma daraja juna. (Afisawa 5:28; Titus 2:4) Idan suka yi haka nan, sai yaransu su ga ƙauna ta Kirista tana aiki. Lallai darasi ne mai tasiri kuma mai daraja!

Iyaye ma suna ɗaukaka ƙauna cikin gida sa’ad da suke kiyaye mizanai masu girma cikin iyali game da batun nishaɗi, ɗabi’a, da maƙasudai da kuma tsara abin da ya fi muhimmanci. A dukan duniya, mutane sun iske cewa Littafi Mai Tsarki yana ba da wannan taimako mai girma a cikin iyalai, yana ba da tabbacin cewa da gaske Littafi Mai Tsarki “hurare daga wurin Allah ne mai-amfani ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci.” (2 Timothawus 3:16) Hakika, ƙa’idodin ɗabi’a da ja-gorar rayuwa da ke cikin Huɗuba Bisa Dutse babu waɗanda suka kai su.—Matta, surori 5 zuwa 7.

Sa’ad da dukan iyali suke dogara ga ja-gorar Allah kuma ke bin mizanansa, kowanne zai yi zaman lafiya, kuma yara za su yi girma su san yadda ake ƙauna kuma su iya daraja iyayensu. A wata sassa kuma, a iyali da ake da mizanai iri biyu, na cike da kuskuri, na zaɓi sonka, yara suna iya gajiya, su yi fushi, kuma su yi tawaye.—Romawa 2:21; Kolossiyawa 3:21.

Game da iyaye gwauraye fa? Suna da kasawa ne a koyar da ƙauna ga yaransu? Ba haka ba. Babu abin da ya fi kyau a kasance da nagarin uwa da uba suna haɗa kai da juna, abin da ya faru ya nuna cewa dangantaka mai kyau ta iyali tana iya taimakawa idan mahaifi gwauro ne. Idan kai mahaifi gwauro ne, ka yi ƙoƙarin yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a gidanka. Hakika, wata karin magana ta gaya mana: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka”—har da hanyoyi na zama iyaye.—Misalai 3:5, 6; Yaƙub 1:5.

Nagargarun matasa da yawa, iyaye gwauraye ne suka yi renonsu kuma ana ganinsu yanzu suna bauta wa Allah da aminci cikin dubban ikilisiyoyin Shaidun Jehovah a dukan duniya. Wannan yana tabbatar da cewa iyaye gwauraye ma suna iya nasara a koya wa yaransu game da ƙauna.

Yadda Duka Za Su Iya Koya Ƙauna

Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi rashin “ƙauna irin na tabi’a,” a “kwanaki na ƙarshe” watau, rashin soyayya da ya kamata waɗanda suke cikin iyali suke wa juna. (2 Timothawus 3:1, 3) Duk da haka, waɗanda ma suka yi girma a yanayi da babu ƙauna za su iya koya ƙauna. Ta yaya? Ta wurin koyo daga Jehovah, wanda shi ne Tushen ƙauna kuma da ke nuna ƙauna da soyayya ga dukan waɗanda suka juya gare shi da zuciya ɗaya. (1 Yohanna 4:7, 8) “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni,” in ji mai Zabura.—Zabura 27:10.

Jehovah yana nuna mana ƙaunarsa a hanyoyi dabam dabam. Wannan ya haɗa da ja-gora ta uba ta wurin Littafi Mai Tsarki, ta wurin taimakon ruhu mai tsarki, da kuma ta goyon baya mai daɗaɗawa na ’yan’uwanci na Kirista. (Zabura 119:97-105; Luka 11:13; Ibraniyawa 10:24, 25) Ka yi la’akari da tanadin nan uku da za su iya taimake ka ka yi girma a ƙaunar Allah da kuma maƙwabci.

Hurarriyar Ja-Gora ta Uba

Domin mu gina gami mai daɗaɗawa da wani, dole ne mu san mutumin sosai. Ta wurin bayyana kansa cikin shafofin Littafi Mai Tsarki, Jehovah ya gayyace mu mu kusace shi. Amma, karanta Littafi Mai Tsarki kawai bai isa ba. Dole ne mu yi amfani da koyarwarsa kuma mu amfana daga ciki. (Zabura 19:7-10) “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi,” in ji Ishaya 48:17. Hakika, Jehovah wanda shi ne ƙauna, yana koyar da mu domin amfaninmu—ba domin yana son ya hana mu ’yanci kawai ta wurin dokoki da sharidu da ba su da amfani ba.

Cikakken sani na Littafi Mai Tsarki kuma na taimakonmu mu yi girma a ƙaunar mutane. Wannan haka yake domin gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta koyar da mu ra’ayin Allah game da mutane kuma ya nuna mana ƙa’idodin da ya kamata su sarrafa yadda muke bi da juna. Da irin koyarwar nan, muna da dalili mai ƙarfi don gina ƙauna ga maƙwabci. Manzo Bulus ya ce: “Abin da ni ke addu’a ke nan, ƙaunarku ta yalwata har gaba gaba cikin sani da ganewa duka.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Filibbiyawa 1:9.

Domin a misalta yadda ‘cikakken sani’ ke ja-gorar ƙauna, ka yi la’akari da muhimmiyar gaskiya da ke a Ayukan Manzanni 10:34, 35: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowacce al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” Idan Allah yana kimanta mutane domin ayyukansu na adalci da tsoronsu na ibada ba domin ƙasar da suka fito ko kuma fatar jikinsu ba, bai dace mu ma mu ɗauki ’yan’uwanmu yadda yake yi ba?—Ayukan Manzanni 17:26, 27; 1 Yohanna 4:7-11, 20, 21.

Ƙauna—’Yar Ruhun Allah

Kamar yadda ruwan sama a lokacinsa a kan itatuwa suke sa a yi girbi mai kyau, ruhun Allah na iya haifa cikin mutane masu zuciyar kirki halaye da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su da “ ’yar Ruhu.” (Galatiyawa 5:22, 23) Na farko cikin ’yar ruhun, ƙauna ce. (1 Korinthiyawa 13:13) Amma ta yaya za mu sami ruhun Allah? Muhimmiyar hanya ita ce ta addu’a. Idan muka yi addu’a don ruhun Allah, za ya ba mu. (Luka 11:9-13) Kana ‘ci gaba da’ yin addu’a domin ruhu mai tsarki? Idan ka yi haka, to, ’ya’yansa masu tamani, haɗe da ƙauna ya kamata su ƙara bayyana a rayuwarka.

Amma, akwai kuma wani irin ruhu da ke yin gāba da ruhun Allah. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan, “ruhun duniya.” (1 Korinthiyawa 2:12; Afisawa 2:2) Mugun ruhu ne, tushensa ba kowa ba Shaiɗan Iblis ne, “mai-mulkin wannan duniya” ta mutane da ke bare daga Allah. (Yohanna 12:31) Kamar iska mai guguwa, “ruhun duniya” yana da mugun sha’awa da ke lalace ƙauna kuma ke gamsar da jiki kumami.—Galatiyawa 5:19-21.

Mutane suna samun wannan mugun ruhun idan suka ƙyale kansu ga tunanin son abin duniya, halin ni-ne farko, halin nuna ƙarfi, da halin ɗimaucewa da ke ɓata ra’ayin ƙauna da ke ko’ina cikin duniya. Idan kana son ka ci gaba da ƙauna ta gaske, dole ne ka yi tsayayya ƙwarai da ruhun duniya. (Yaƙub 4:7) Amma kada ka dogara ga naka ƙarfi; ka nemi Jehovah domin taimako. Ruhunsa—iko da ya fi cikin sararin halitta—zai iya ƙarfafa ka kuma ba ka nasara.—Zabura 121:2.

Ka Koyi Ƙauna Daga ’Yan’uwanci na Kirista

Kamar yadda yara suke koya su nuna ƙauna ta yadda ake nuna musu a gida, dukanmu—manya da ƙanana—za mu iya ƙara nuna ƙauna ta wurin yin tarayya da wasu Kiristoci. (Yohanna 13:34, 35) Alhali ma, ɗaya cikin aikin ikilisiyar Kirista na musamman shi ne ta kasance wuri da mutane suke iya “motsa juna ga ƙauna da nagargarun ayyuka.—Ibraniyawa 10:24, New International Version.

Waɗanda suka “wahala, suna watse” ne musamman suke godiya ga ƙaunar nan cikin wannan duniya marar ƙauna da ta kewaye mu. (Matta 9:36) Abin da ya faru ya nuna cewa dangantaka ta ƙauna bayan an yi girma, na iya sha kan munanan tabo da aka ɗauko daga rashin ƙauna a yarantaka. Saboda haka, yana da muhimmanci cewa dukan Kiristoci da suka keɓe kansu su yi wa sababbi da suke shigowa tsakaninsu maraba da zuciya ɗaya!

“Ƙauna Ba ta Ƙarewa Daɗai”

Littafi Mai Tsarki ya ce “ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.” (1 Korinthiyawa 13:8) Yaya yake haka? Manzo Bulus ya gaya mana: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura.” (1 Korinthiyawa 13:4, 5) A bayyane yake cewa wannan ƙauna ba wata ƙage ko kuma zakin baki ba ce kawai. Akasarin haka—waɗanda suke nuna ta sun sani ko kuma fahimci baƙin ciki da azabar rayuwa, amma ba sa yarda wa waɗannan su lalace ƙaunarsu ga ’yan’uwansu. Irin ƙaunar nan da gaske “magamin kamalta” ce.—Kolossiyawa 3:12-14.

Ka yi la’akari da misalin wata Kirista ’yar shekara 17 a Koriya. Da ta soma bauta wa Jehovah Allah, iyalinta suka ƙi da haka kuma ta bar gidan. Amma, maimakon ta yi fushi, ta yi addu’a game da batun, ta yarda wa Kalmar Allah da ruhunsa su kiyaye tunaninta. Bayan haka, tana rubuta wa iyalin wasiƙa sau da sau, wasiƙunta cike suke da ƙaunar soyayya da take musu. Sakamakon haka, ’yan’uwanta maza biyu suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma yanzu Kiristoci ne da suka keɓe kansu. Uwarta da ƙanenta ma suka karɓi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. A ƙarshe, ubanta, da yake bala’in hamayya, halinsa ya canja. Yarinya Mashaidiyar ta rubuta: “Dukanmu mun auri ’yan’uwa Kiristoci, kuma iyalinmu da suke bauta tare yanzu sun kai 23.” Dubi nasarar ƙauna!

Kana son ka gina ƙauna ta gaske kuma taimake wasu su yi hakan? Sai ka juya ga Jehovah, Tushen dukan halayen kirki. Hakika, ka tuna da Kalmarsa, ka yi addu’a domin ruhu mai tsarki, ka yi tarayya kullum da ’yan’uwanci na Kirista. (Ishaya 11:9; Matta 5:5) Dubi yadda yake daɗaɗa zuciya a san cewa jim kaɗan dukan mugunta ba za su kasance kuma ba, a bar waɗanda suke kiyaye ƙauna ta gaske ta Kirista! Gaskiya, ƙauna ce mabuɗin farin ciki da kuma rai.—Zabura 37:10, 11; 1 Yohanna 3:14.

[Hotuna a shafi na 6]

Addu’a da nazarin Kalmar Allah za su taimake mu mu koya ƙauna ta gaske

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba