Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 7/1 p. 3
  • Ƙauna Tana da Muhimmanci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙauna Tana da Muhimmanci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • A Ina Ƙaunarka Ta Tsaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 7/1 p. 3

Ƙauna Tana da Muhimmanci

KO DA shekarunsu nawa ne, al’adarsu, yarensu, ko kuma ƙabilarsu, dukan bil adama suna bukatar ƙauna. Idan ba a gamsar da bukatar nan ba, ba sa farin ciki. Wani mabinciki na magani ya rubuta: “Ƙauna da abuta abubuwa ne da rashinsu ke sa mu ciwo kuma samunsu ke sa mu yi lafiya, abubuwa da rashinsu ke kawo baƙin ciki kuma samunsu ke kawo farin ciki, abubuwan da rashinsu ke sa mu wahala kuma ke kai ga warkarwa. Idan wani sabon magani yana iya wannan aikin, kusan kowanne likita a ƙasar zai so ya ba majiyyatarsa. Zai zama rashin bin doka ne idan ba a ba da wannan maganin ba.”

Amma, jam’iyya ta zamani, musamman ma hanyar watsa labarai da waɗanda ake ɗaukansu majagaba, sau da yawa suna nanata wadata, iko, suna, da kuma lalata maimakon bukatar ’yan Adam na dangantaka mai daɗaɗawa, ta ƙauna. Masu ilimantarwa da yawa suna nanata maƙasudi na duniya da aiki, suna da ra’ayin cewa samun nasara ita ce samun waɗannan abubuwa. To dai, ilimi da amfani da iyawar mutum na da muhimmanci, amma ya kamata ne a biɗe su har da ba za a samu lokaci domin iyali da kuma abokai ba? Wani marubuci mai ilimi na dā da ke kula da halin mutane sosai ya kwatanta mutum da yake da wasu iyawa, amma marar ƙauna da “jan ƙarfe mai-ƙara ko kuwa kūge mai-ƙaraurawa.” (1 Korinthiyawa 13:1) Irin mutanen nan sukan zama mawadata, har ma yi suna, amma ba sa farin ciki da gaske.

Yesu Kristi wanda yake da fahimta mai girma kuma daularsa wurin mutane ne, ya sa ƙauna ga Allah da kuma maƙwabci abu mafi muhimmanci a koyarwarsa. Ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. . . . Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:37-39) Waɗanda suka bi waɗannan kalmomin ne kawai za su zama mabiyan Yesu da gaske. Shi ya sa ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yohanna 13:35.

Amma yaya mutum zai koyi ƙauna a duniya ta yau? Kuma ta yaya iyaye za su koya wa yaransu ƙauna? Talifi na gaba zai bincika waɗannan tambayoyin.

[Hotuna a shafi na 3]

Ƙalubale ne mutum ya koyi ƙauna a duniya da haɗama ce ke mallakarta

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba