Matasa—Jehovah Ba Zai Manta Da Aikinku Ba!
“Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa, yayinda kuka hidimta ma tsarkaka, kuna kuwa yi har wa yau.”—IBRANIYAWA 6:10.
1. Yaya littattafai na Ibrananci da kuma Malachi cikin Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa Jehovah yana godiya ga hidimarka?
KA TAƁA yi wa wani abokinka kirki amma bai yi godiya ba? Abin ɓacin rai ne idan aka nuna rashin godiya ga wani abin kirki da aka yi, mafi muni ma, idan aka mance. Amma dubi yadda ya bambanta idan muna bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa, yayinda kuka hidimta ma tsarkaka, kuna kuwa yi har wa yau.” (Ibraniyawa 6:10) Ka yi tunanin wannan. Zai zama rashin adalci ne wajen Jehovah—zunubi kuwa—idan ya manta da abin da ka yi da kuma wanda kake yi cikin hidimarsa. Hakika Allah ne mai godiya!—Malachi 3:10.
2. Me ya sa bauta wa Jehovah take da muhimmanci da gaske?
2 Kana da zarafi na musamman ka bauta kuma ka yi hidima ga wannan Allah mai godiya. Tun da yake masu bi, miliyan shida ne kawai idan aka gwada da mutane biliyan shida da suke dukan duniya, gatarka tana da girma ƙwarai. Ban da haka ma, domin kana sauraro kuma kana bin saƙon bisharar, tabbaci ne cewa Jehovah yana lura da kai. Balle ma Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Hakika, Jehovah yana taimakon kowannenmu ya yi amfani da fa’idar hadayar Kristi.
Nuna Godiya ga Gatarka ta Musamman
3. Ta yaya ’ya’yan Kora suka furta godiya domin gatar bauta wa Jehovah?
3 Kamar yadda aka tattauna cikin talifi da ya gabata kana matsayi na musamman don ka faranta wa Jehovah zuciya. (Misalai 27:11) Wannan wani abu ne da ba za ka yi banza da shi ba. A cikin wata zabura, ’ya’yan Kora sun furta godiyarsu domin gatar bauta wa Jehovah. Mu karanta: “Yini ɗaya cikin gidajenka ya fi dubu: na fi so ina mai-tsaron ƙofa cikin gidan Allahna, da in zauna cikin [tanti] na mugunta.”—Zabura 84:10.
4. (a) Me zai iya sa wasu su yi tunanin cewa bauta wa Jehovah tana da hani? (b) A wace hanya ce Jehovah yake ɗokin lura da kuma sāka wa bayinsa?
4 Yadda kake ji ke nan game da gatarka ta bauta wa Ubanka na samaniya? Hakika, a wasu lokatai kamar bauta wa Jehovah tana da hani ga ’yancinka. Gaskiya ne cewa rayuwa daidai da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki na bukatar sadaukarwa. Amma mafi amfani shi ne duk abin da Jehovah ke bukata daga gare ka domin amfaninka ne. (Zabura 1:1-3) Ban da haka, Jehovah yana ganin ƙoƙarce-ƙoƙarcenka kuma yana godiya ga amincinka. Hakika, Bulus ya rubuta cewa Jehovah “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Jehovah yana neman hanyoyin yin haka nan. Wani annabi mai aminci a Isra’ila ta dā ya ce: “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.”—2 Labarbaru 16:9.
5. (a) A wace hanya ɗaya ce mafi kyau za ka nuna cewa zuciyarka ta kamalta wajen Jehovah? (b) Me ya sa yi wa wasu magana game da bangaskiyarka kamar yana da wuya?
5 Hanya ɗaya mafi kyau da za ka nuna cewa zuciyarka ta kamalta wajen Jehovah ita ce ta gaya wa wasu game da shi. Ka taɓa samun zarafin yi wa wasu abokan makarantarka wa’azi game da imaninka? Yin haka, da farko, zai yi wuya, kuma tunanin hakan zai iya ɗan tsoratar da kai. To, kana iya cewa: ‘Idan suka yi mini dariya fa?’ ‘Idan suna tunanin cewa addinina sabo ne fa?’ Yesu ya sani cewa ba kowa ne zai saurari saƙon Mulkin ba. (Yohanna 15:20) Amma wannan ba ya nufin cewa an ƙaddara maka ba’a da ƙiyayya ba. Akasin haka, matasa Shaidu da yawa sun sami masu sauraro har sun sami daraja daga tsararsu domin manne wa abin da suka gaskata.
‘Jehovah Zai Taimake Ka’
6, 7. (a) Yaya wata yarinya ’yar shekara 17 ta yi wa abokan ajinta wa’azi? (b) Me ka koya daga labarin Jennifer?
6 Ta yaya za ka yi gaba gaɗi ka yi magana game da bangaskiyarka? Me ya sa ba za ka yanke shawarar ka faɗi gaskiya kai tsaye, idan aka tambaye ka game da addininka ba? Ka yi la’akari da labarin Jennifer ’yar shekara 17. “Sa’ad da nake cin abincin rana a makaranta. ’Yammata da suke teburinmu suka soma taɗi game da addini kuma ɗaya cikinsu ta tambaya ko wane addini nake bi.” Jennifer ta yi rawan jiki ne da take ba da amsar? “E, domin ban san abin da za su ce ba,” in ji ta. To, me Jennifer ta yi? Ta ci gaba: “Na gaya wa ’yammatan cewa ni Mashaidiyar Jehovah ce. Da farko suka yi mamaki. Hakika, suna da ra’ayin cewa Shaidun Jehovah wasu irin mutane ne. Wannan ya sa suka yi mini tambayoyi, kuma na yi musu bayani game da irin ra’ayin nan. Daga baya ma, wasu ’yammatan sukan dumfare ni wani lokaci su yi tambaya.”
7 Jennifer ta yi nadama ne game da zarafin da ta samu na magana game da imaninta? Ko kaɗan! “Na yi murna sosai lokacin da muka gama shan iska,” in ji ta. Yanzu ’yammatan nan sun fahimci Shaidun Jehovah sosai. Ga shawarar Jennifer mai sauƙi : “Idan ya yi maka wuya ka yi wa abokan ajinka ko kuma malamai wa’azi, ka yi addu’a nan da nan. Jehovah zai taimake ka. Za ka yi farin cikin ka yi amfani da zarafi na yin wa’azi da kyau.”—1 Bitrus 3:15.
8. (a) Ta yaya addu’a ta taimaki Nehemiya lokacin da ya fuskanci yanayi ba zato ba tsammani? (b) Ina wasu yanayi da ake iskewa a makaranta da za ka bukaci yin addu’a a zuci ga Jehovah?
8 Ka lura cewa Jennifer ta ce a ‘yi addu’a nan da nan’ ga Jehovah idan zarafin ya samu na yin wa’azi game da imaninka. Abin da Nehemiya, mai shayarwa na Sarki Artaxerxes ya yi ke nan lokacin da ya fuskanci yanayi ba zato ba tsammani. Nehemiya ya damu ana gani domin an gaya masa matsalar Yahudawa kuma ya san cewa garu da kuma ƙofofin Urushalima sun halaka. Sarkin ya lura da cewa Nehemiya ya damu, saboda haka, ya tambaye shi abin da ya faru. Kafin Nehemiya ya amsa, ya yi addu’a domin ja-gora. Da gaba gaɗi kuwa ya nemi izini ya koma Urushalima kuma ya taimaka a sake ginin birnin. Artaxerxes ya ba Nehemiya izini. (Nehemiah 2:1-8) Wane darasi ka koya? Idan kana rawan jiki yayin da zarafin yin wa’azi game da imaninka ya samu, kada ka ƙyale zarafin sai ka yi addu’a a zuci. “Kuna zuba dukan alhininku a bisan [Jehovah],” in ji Bitrus, “domin yana kula da ku.”—1 Bitrus 5:7; Zabura 55:22.
“A Shirye Ku Ke Ku Amsa”
9. Ta yaya ne Leah ’yar shekara 13 ta iya ba da littattafai na Young People Ask guda 23?
9 Ga wani labari kuma. Leah ’yar shekara 13 tana karatun littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Worka a lokacin shaƙatawa a makaranta. “Wasu suna kallona,” in ji ta, “bai daɗe ba sai ga jama’a sun taru mata. Suka soma tambaya game da abin da ke cikin littafin.” A ƙarshen wannan ranar, ’yammata huɗu suka ce Leah ta ba su nasu kofin littafin nan Young People Ask. Bai daɗe ba waɗannan ’yammatan suna gaya wa wasu abin da ke cikin littafin kuma waɗannan suka ce a ba su nasu. Har zuwa mako na gaba, Leah ta ba da littattafai guda 23 na Young People Ask wa abokan makarantarta. Ya kasance wa Leah da sauƙi ne ta yi magana lokacin da wasu suka yi tambaya game da littafin? Da ƙyar! Ta ce: “Da farko na yi rawan jiki, amma na yi addu’a kuma na san Jehovah yana tare da ni.”
10, 11. Ta yaya ƙaramar yarinya Ba’isra’iliya ta iya taimakon shugaban sojojin Suriya ya koyi game da Jehovah, kuma waɗanne canje-canje ya yi daga baya?
10 Wataƙila labarin Leah zai tunasar da kai yanayi iri ɗaya da wata Ba’isra’iliya ta fuskanta da aka kai ta bauta a Suriya. Shugaban sojojin Suriya, Na’aman, kuturu ne. Wataƙila matarsa ce ta soma taɗi da ƙila ya sa wannan ƙaramar yarinya ta yi magana game da imaninta. Ta ce: “Da ma ubangijina yana tare da annabin da ke a Samariya! Da ya warkadda kuturtarsa.”—2 Sarakuna 5:1-3.
11 Ta wurin gaba gaɗi na ƙaramar yarinyar nan ne, Na’aman ya san cewa “babu wani Allah cikin dukan duniya, sai cikin Isra’ila.” Har ma ya tsai da cewa ba zai “sake yin hadaya ta ƙonawa, ko kowace hadaya haka ga waɗansu allohi sai ga Ubangiji.” (2 Sarakuna 5:15, 17) Hakika Jehovah ya albarkaci gaba gaɗin ƙaramar yarinyar nan. Zai iya yi, kuma zai yi haka nan ga matasa a yau ma. Leah ta shaida wannan. A kwana a tashi, wasu abokan makarantarta suka kusace ta kuma suka ce littafin Young People Ask ya taimake su a halayensu. “Na yi farin ciki,” in ji Leah, “domin na san cewa ina taimakon wasu su koyi game da Jehovah kuma in taimake su su canja rayuwarsu.”
12. Ta yaya za ka sami ƙarfafa ka kasance da amsa domin imaninka?
12 Kana iya shaida abin da ya faru wa Jennifer da Leah. Ka bi gargaɗin da Bitrus ya bayar, wanda ya rubuta cewa ya kamata Kirista kullum ya kasance a “shirye [domin ya] amsa ma kowane mai-tambayan[sa] dalilin begen da ke cikin[sa], amma dai da ladabi da tsoro.” (1 Bitrus 3:15) Ta yaya za ka iya yin wannan? Ka bi tafarkin Kiristoci na ƙarni na farko da suka roƙi Jehovah ya taimake su su yi wa’azi “da ƙarfinzuciya.” (Ayukan Manzanni 4:29) To, sai ka kasance da gaba gaɗi a yi wa wasu magana game da imaninka. Kana iya mamakin sakamakon hakan. Ban da haka ma, za ka faranta wa Jehovah zuciya.
Su Bidiyo da Kuma Rubuce-Rubuce
13. Waɗanne irin zarafi ne wasu matasa suka yi amfani da shi su yi wa’azi? (Dubi akwatuna a shafofi na 11 da 12.)
13 Matasa da yawa sun bayyana imaninsu wa abokan makaranta ko kuma malamai ta yin amfani da bidiyo. A wasu lokatai kuma aikin makaranta na ba da zarafin yabo ga Jehovah. Ga misali, yara biyu maza, Shaidun Jehovah ne, aka ba su aiki a ajinsu a kan tarihin duniya su rubuta game da wani addini a duniya. Waɗannan yara biyun suka haɗa kai su rubuta labari game da Shaidun Jehovah, sun yi amfani da littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom.b An kuma ce su karanta a fili labari na minti biyar. Bayan haka, malamin tare da ɗaliban suka yi tambayoyi da yawa har da ya sa yara biyun suka ci minti 20 a gaban ajin. Bayan makonni, abokan ajinsu suka ci gaba da yi musu tambayoyi game da Shaidun Jehovah!
14, 15. (a) Me ya sa tsoron mutum tarko ne? (b) Me ya sa ya kamata ka kasance da gaba gaɗi ka gaya wa wasu game da imaninka?
14 Kamar yadda yake cikin labarai na baya, da akwai albarka ƙwarai a yi wa wasu magana game da imaninka da tabbaci cewa kai Mashaidin Jehovah ne. Kada ka yarda tsoron mutum ya hana ka gata da kuma farin cikin taimaka wa wasu su san Jehovah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsoron mutum ya kan kawo tarko, amma wanda ya sa danganarsa ga Ubangiji za ya zauna lafiya.”—Misalai 29:25.
15 Ka tuna, kai matashi Kirista kana da wani abin da tsararka suke bukata—hanyar rayuwa mafi kyau a yanzu da kuma alkawarin rai na har abada a nan gaba. (1 Timothawus 4:8) Abin farin ciki, a Amirka—inda za ka iya tsammanin cewa mutane ba sa tunanin kome sai neman kuɗi—wani bincike da aka yi ya nuna cewa rabin matasa suna son addini, wani kashi kuma suka ce “abu mafi rinjaya” ne a rayuwarsu. Yanayin wataƙila duk ɗaya ne a wasu ɓangarorin duniya. Saboda haka, zai zamana cewa tsararka a makaranta za su so su saurari abin da za ka gaya musu daga Littafi Mai Tsarki.
Kai Matashi, Ka Kusaci Jehovah
16. Me ke cikin faranta wa Jehovah zuciya ban da yi wa wasu magana kawai game da shi?
16 Hakika, faranta wa Jehovah zuciya ba yin magana game da shi kawai ba ne. Kana kuma bukatar ka sa halayenka su yi daidai da mizanansa. Manzo Yohanna ya rubuta: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yohanna 5:3) Za ka shaida gaskiyar wannan idan ka kusaci Jehovah. Ta yaya za ka iya yin haka nan?
17. Ta yaya za ka kusaci Jehovah?
17 Ka ɗauki lokaci don karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafansa. Idan ka koyi game da Jehovah, zai kasance da sauƙi ka yi masa biyayya kuma yi wa wasu magana game da shi. “Mutum nagari daga cikin ajiya mai-kyau ta zuciyatasa ya kan fito da abin da ke mai-kyau,” in ji Yesu, “gama daga cikin yalwar zuciya bakinsa ya ke zance.” (Luka 6:45) Saboda haka, ka cika zuciyarka da nagargarun abubuwa. Me ya sa ba za ka kafa makasudi ba? Wataƙila za ka so ka yi gyara a yadda kake shirya taronka na ikilisiya a makon nan na gaba. Ƙila makasudinka na gaba zai zama ka yi ƙoƙarin yin gajeren kalami mai ma’ana daga zuci. Hakika, yana da muhimmanci ka kuma yi amfani da abubuwan da ka koya.—Filibbiyawa 4:9.
18. Ko idan ka sha wahalar wata hamayya, me za ka tabbata da shi?
18 Albarka da ke fitowa daga bauta wa Jehovah tana daɗewa—hakika na har abada. Haka ma, a wasu lokatai za ka iya shaida ɗan hamayya ko kuma ba’a domin kai Mashaidin Jehovah ne. Amma sai ka tuna da Musa. Littafi Mai Tsarki ya ce “yana sauraron sakamakon.” (Ibraniyawa 11:24-26) Kai ma za ka tabbata cewa Jehovah zai sāka maka domin ƙoƙarin da kake yi na koyo game da shi kuma ka gaya wa wasu game da shi. Babu shakka, ba zai taɓa “manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa” ba.—Ibraniyawa 6:10.
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga.
b Shaidun Jehovah ne suka buga.
Ka Tuna?
• Me ya sa za ka tabbata cewa Jehovah yana daraja hidimarka?
• Waɗanne hanyoyin yin wa’azi ne wasu suka iske yana nasara a makaranta?
• Ta yaya za ka ƙarfafa ka yi wa abokan ajinka wa’azi?
• Ta yaya za ka kusaci Jehovah?
[Box/Hotuna a shafi na 11]
Har Yara Ƙanana ma Suna Yabon Jehovah!
Har waɗanda ba su kai shekaru daga goma sha-uku ba suna wa’azi da kyau a makaranta. Ka yi la’akari da waɗannan labarai.
Amber ’yar shekara 10 a ajinta na biyar tana karatun wani littafi game da farmakin da Nazi suka yi wa Yahudawa a lokacin Yaƙin Duniya na II. Sai Amber ta kawo bidiyo nan Purple Triangles ta ba wa malamarta. Malamar ta yi mamaki da ta ga cewa Shaidun Jehovah ma suna cikin waɗanda aka tsananta musu a ƙarƙashin hukuncin Nazi. Malamar ta nuna wa dukan ajin bidiyon.
Alexa ’yar shekara takwas ta rubuta wa ajinta wasiƙa ta ba da bayanin abin da ya sa ba za ta yi bikin Kirsimati da su ba. Wasiƙar ta burge malamarta ƙwarai da har ta sa ta ta karanta wasiƙar wa ajin da kuma wasu azuzuwa biyu! “An koya mini na daraja imanin wasu da ya bambanta da nawa,” in ji ta da take kammala wasiƙar, “kuma ina mai godiya a gare ku da kuka daraja shawarata ta ƙin bikin Kirsimati.”
Ba da daɗewa ba bayan ya shiga aji ɗaya, Eric ya kai littafin nan Littafi Na na Labarun Bible makaranta kuma ya nemi izini ya nuna wa abokan ajinsa. “Ina ganin abin da ya fi,” in ji malamarsa. “Ka karanta labari ga ajin?” Eric ya karanta musu. Bayan haka, ya gayyaci duk waɗanda suke so su sami nasu littafin su ɗaga hannunsu. Mutane 18—har da malamarsu—suka ɗaga hannu! Yanzu Eric ya ga yana da nasa yanki na musamman na wa’azi.
Whitney ’yar shekara tara ta yi godiya domin mujallar nan Jehovah’s Witnesses and Education.c “Dama mamata ce take ba wa malamai na mujallar kowacce shekara,” in ji ta, “amma wannan shekarar ni na ba su da kaina. Na gode wa wannan mujallar, malamata ta zaɓe ni ‘ɗalibar da za a yi wa kyauta domin tarbiyya mai kyau.’ ”
[Hasiya]
c Dukan littattafai da aka ambata Shaidun Jehovah ne suka buga.
[Box/Hotuna a shafi na 12]
Wasu Yanayi da Wasu Sun Yin Amfani da Su Su Yi Magana Game da Imaninsu
Yayin da aka ce su ba da rahoto ko kuma su yi wani aiki na makaranta, wasun sun zaɓi wani jigo da zai ba su zarafin yin wa’azi
Wasu matasa sun ba wa malamansu bidiyo ko kuma wani littafi da ke magana game da abin da ake tattaunawa a aji
Wasu matasa sa’ad da suke karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma littattafan Littafi Mai Tsarki a lokacin hutu wasu matasa sun zo wurinsu domin su yi tambaya
[Hoto a shafi na 9]
Waɗanda suka ƙware su taimaka wa matasa su bauta wa Jehovah