Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 5/1 pp. 3-8
  • Matasa Da Suke Faranta Wa Jehovah Zuciya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa Da Suke Faranta Wa Jehovah Zuciya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kāriya Domin “Mugun”
  • “Ka Faranta Zuciyata”
  • Jehovah Yana Kula da Kai!
  • Lada Mai Yawa a Yanzu
  • Bauta wa ‘Allah Mai Farin Ciki’
  • Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Yadda Za A Faranta Wa Allah Rai
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Yi Hattara, Shaidan Yana So Ka Bijire!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 5/1 pp. 3-8

Matasa Da Suke Faranta Wa Jehovah Zuciya

An shirya waɗannan talifofin nazari musamman domin matasa tsakanin Shaidun Jehovah ne. Saboda haka, muna ƙarfafa matasa su yi nazarin wannan da kyau kuma su yi kalami a sake lokacin da ake nazarinsu a taron Nazari na Hasumiyar Tsaro.

“Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.”—Misalai 27:11.

1, 2. (a) Ka ba da bayani game da ko sha’awar abubuwan duniya kawai yana nufi cewa ba a yi ka ka zama Kirista ba. (Romawa 7:21) (b) Me ka koya daga misalin Asaph? (Dubi akwati, shafi na 4.)

A CE ka je sayan riguna. Da kake dubawa sai ka ga wata taguwa da kake so sosai. Kana son kalar da kuma salon sosai, kuma ba ta da tsada sosai. Amma sai ka sake bincika ta sosai. Ka lura cewa bakin yadin ya tsufa, kuma ɗinkin ba shi da kyaun gani. Ko da yake taguwar tana da kyau, ba a yi ta da inganci ba. Za ka so ka ɓāta kuɗinka a kan irin wannan mummunar ɗinkin?

2 Ka gwada wannan da yanayin da za ka iya fuskanta na matashi Kirista. Kamar taguwar—waɗannan abubuwan duniya idan ka yi musu kallo ɗaya, za su kasance kyawawa sosai. Alal misali, abokan makarantarka suna iya zuwan wata liyafa, su sha miyagun ƙwayoyi, su sha giya, su fita zance, kuma su shagala cikin lalata. A wasu lokatai, kana sha’awar irin wannan salon rayuwar ne? Kana sha’awar ka ɗanɗana abin da suke kira ’yanci? Idan haka ne, kada ka yi hanzarin kammala cewa kana da muguwar zuciya, ba a yi ka ka zama Kirista ba. Balle ma, Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa duniya tana da ban sha’awa ƙwarai—har ma ga wanda yake son ya faranta wa Allah zuciya.—2 Timothawus 4:10.

3. (a) Me ya sa bai da amfani a biɗi abubuwan duniya? (b) Ta yaya wata Kirista ta kwatanta wofincin biɗan abubuwan duniya?

3 Yanzu ka duba abubuwan wannan duniya da kyau, yadda za ka binciki wata taguwa da kake son ka saya. Ka tambayi kanka, ‘Menene ingancin yadi da kuma ɗinki na wannan zamani?’ Littafi Mai Tsarki ya ce “duniya ma tana wucewa.” (1 Yohanna 2:17) Duk wata annashuwa da za a samu daga cikinta, na ɗan lokaci ne kawai. Ban da haka ma, halaye na rashin ibada suna jawo mummunar sakamako. Hakika, ba su da sauƙi. Wata Kirista da ta jimre wa abin da ta kira “azaba domin mummunar rayuwar ƙuruciya,” ta ce: “Duniya tana da ban sha’awa ƙwarai, da rinjaya. Kuma tana so ka gaskata cewa za ka iya more kowanne fanninta ba tare da wani mummunar sakamako ba. Amma wannan ba zai yiwu ba. Duniya za ta yi amfani da kai, bayan ta gama amfani da kai, sai ta jefar da kai.”a Me ya sa za ka ɓata ƙuruciyarka a irin wannan hanyar rayuwa marar inganci?

Kāriya Domin “Mugun”

4, 5. (a) Ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa, menene Yesu ya roƙa cikin addu’a ga Jehovah? (b) Me ya sa wannan roƙon ya dace?

4 Da sanin cewa babu wani abu mai inganci da wannan zamani yake da shi ya bayar, matasa tsakanin Shaidun Jehovah suna faman su guje wa yin abokantaka da wannan duniya. (Yaƙub 4:4) Kana ɗaya daga cikin waɗannan matasa masu aminci? Idan haka ne, muna yaba maka. A gaskiya, ba shi da sauƙi a tsayayya wa matsi na tsara kuma a kasance dabam, amma kuna da masu taimako.

5 Ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa, Yesu ya yi addu’a ga Jehovah ya “tsare” almajiransa domin “mugun.” (Yohanna 17:15) Da kyakkyawan dalili Yesu ya yi wannan roƙon. Ya sani cewa bin tafarkin aminci ba zai kasance da sauƙi ba ga mabiyansa, ko yaya girmansu. Me ya sa? Kamar yadda Yesu ya fahimta, domin almajiransa za su fuskanci magabci, mai ƙarfi marar ganuwa—“mugun,” Shaiɗan Iblis. Littafi Mai Tsarki ya ce wannan mugun halittar ruhu “yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.”—1 Bitrus 5:8.

6. Ta yaya muka sani cewa Shaiɗan ba ya tausayin matasa?

6 Duk cikin tarihi, Shaiɗan yana farin ciki ya jawo laifi mafi muni a kan mutane. Ka yi la’akari da masifu da Shaiɗan ya jawo wa Ayuba da iyalinsa. (Ayuba 1:13-19; 2:7) Wataƙila kana iya tuna labaran rayuwarka da yake ɗauke da mugun hali na Shaiɗan. Iblis yana kan yawon neman wanda zai cinye, ba ya tausayin matasa. Alal misali, a farkon ƙarni na farko A.Z., Hirudus ya fito da dabara ya kashe dukan ’ya’ya maza a Baitalahmi daga masu shekara biyu zuwa ƙasa. (Matta 2:16) Yana yiwuwa cewa Shaiɗan ne ya motsa Hirudus—wannan domin ya halakar da yaron da wata rana zai zama Almasihu da Allah ya yi alkawarinsa zai kawo hukuncin Allah a kan Shaiɗan! (Farawa 3:15) A bayyane yake cewa Shaiɗan ba ya ƙaunar matasa. Ainihin manufarsa ita ce ya halaka mutane da yawa yadda zai iya. Wannan gaskiya ne a yanzu musamman ma domin an jefo da Shaiɗan daga sama zuwa duniya, “hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.”—Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.

7. (a) Ta yaya Jehovah ya bambanta da Shaiɗan? (b) Yaya Jehovah yake ji game da more rayuwarka?

7 Akasin Shaiɗan da yake da “hasala mai-girma,” Jehovah mai “jinƙai mai-taushi” ne. (Luka 1:78) Shi ne tushen ƙauna. Hakika, wannan hali mai girma ya bayyana Mahaliccinmu daidai, da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Dubi bambanci tsakanin allah na wannan zamani da Allah da kake da gatar bauta wa! Ko da yake Shaiɗan nema yake ya halakar, Jehovah “ba shi nufin kowa da halaka ba.” (2 Bitrus 3:9) Yana ɗaukan rayukan kowanne da tamani—har da ranka. Lokacin da Jehovah ya yi maka gargaɗi kada ka zama na duniya, ba ƙoƙarin ya hana ka more rayuwarka ba ne yake yi ko kuma ya hana ka ’yancinka. (Yohanna 15:19) Akasarin haka, yana lura da kai ne domin mugun. Ubanka na samaniya yana son ka sami abin da ya fi annashuwa ta ɗan lokaci na wannan duniyar kyau. Burinsa shi ne ka sami “hakikanin rai”—rai na har abada a duniya ta aljanna. (1 Timothawus 6:17-19) Jehovah yana son ka yi nasara, kuma yana ƙarfafa ka ka cim ma makasudin. (1 Timothawus 2:4) Ban da haka, Jehovah yana gayyatarka musamman. Don menene?

“Ka Faranta Zuciyata”

8, 9. (a) Wace irin kyauta ce za ka iya ba wa Jehovah? (b) Ta yaya Shaiɗan yake zargin Jehovah, yadda aka misalta a labarin Ayuba?

8 Ka taɓa saya wa wani abokinka na kud da kud wata kyauta sai ka ga yadda ya cika da godiya, farin ciki da mamaki sa’ad da ya karɓi kyautar? Wataƙila ka yi tunani mai zurfi da kuma la’akari sosai game da irin kyautar da za ta dace da mutumin. Yanzu ka yi la’akari da wannan tambayar: Wace irin kyauta za ka iya ba wa Mahaliccinka, Jehovah Allah? A farko, tunanin wannan ma sai ya kasance wauta. Menene Mai Iko Duka yake bukata daga bil adama? Menene za ka ba shi da ƙila ba shi da shi? Littafi Mai Tsarki ya amsa a Misalai 27:11: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.”

9 Kamar yadda ka sani ta wurin nazarinka na Littafi Mai Tsarki, Shaiɗan Iblis ne yake zargin Jehovah. Ya ce duk wanda yake bauta wa Allah, yana yin haka ne ba domin yana ƙaunarsa ba, amma don son kai. Idan suka wahala, in ji Shaiɗan, babu ɓata lokaci za su yi watsi da bauta ta gaskiya. Alal misali, ka yi la’akari da abin da Shaiɗan ya gaya wa Jehovah game da Ayuba mutum mai adalci: “Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowane sassa? Ka albarkaci aikin hannuwansa, dabbobinsa sun ƙaru a ƙasa. Miƙa hannunka kaɗai yanzu, ka taɓa dukan abin da yake da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”—Ayuba 1:10, 11.

10. (a) Ta yaya muka sani cewa Shaiɗan yana tuhumar ba amincin Ayuba ba ne kawai? (b) Ta yaya batun ikon mallaka ya shafe ka?

10 Yadda yake a bayyane cikin labarin Littafi Mai Tsarki, Shaiɗan ya tuhumi ba kawai amincin Ayuba ba amma kuma na dukan wasu da suke bauta wa Allah—har da kai. Hakika, da yake magana game da galibin mutane, Shaiɗan ya ce wa Jehovah: “Dukan abin da mutum [ko waye, ba Ayuba kawai ba] ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayuba 2:4) Ka ga matsayinka a wannan batu mai muhimmanci? Yadda aka nuna a Misalai 27:11, Jehovah yana cewa ne da akwai abin da za ka ba shi—dalili da zai sa ya sami amsa wa mai zargi, Shaiɗan. Ka duba—Mamallakin Dukan Halitta yana kiranka ka sa hannu a ba da amsa ga wannan batu mafi girma gabaki ɗaya. Dubi yadda wannan yake hakki mai girma kuma gatar taka ce! Za ka iya cika abin da Jehovah yake biɗa a gare ka? Ayuba ya yi hakan. (Ayuba 2:9, 10) Haka ma Yesu da wasu da yawa cikin tarihi suka yi, har da matasa da yawa. (Filibbiyawa 2:8; Ru’ya ta Yohanna 6:9) Za ka iya yin haka nan. Kada ka yi kuskure, babu tsaka-tsaki cikin wannan batun. Ta wurin halayenka, za ka nuna ko kana goyon bayan zargin Shaiɗan ko kuma amsar Jehovah. Wanene za ka zaɓa ka bi?

Jehovah Yana Kula da Kai!

11, 12. Jehovah yana damuwa ne idan ka zaɓi ka bauta masa ko kuma babu? Ka ba da bayani.

11 Jehovah yana damuwa ne game da zaɓen da kake yi? Mutane da yawa ba sun riga sun riƙe amincinsu gare shi domin ya iya ba da amsa ga Shaiɗan ba ne? Hakika, Iblis ya yi da’awar cewa babu wanda yake bauta wa Jehovah domin ƙauna amma an ƙaryata wannan zargin. Duk da haka, Jehovah yana son ka kasance a gefensa na batun ikon mallaka domin yana kula da kai ainihinka. Yesu ya ce: “Ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.”—Matta 18:14.

12 A bayyane yake cewa Jehovah yana damuwa da tafarkin da ka zaɓa. Fiye da haka ma, yana shafansa. Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa Jehovah yana da juyayi ƙwarai a kan halayen kirki ko kuma na mugunta da mutane suke yi. Alal misali, da Isra’ilawa suka riƙa tawaye, sun ‘ɓata’ wa Jehovah rai. (Zabura 78:40, 41) Kafin Rigyawan zamanin Nuhu, yayin da “muguntar mutum ta yi yawa,” ya ‘ɓata’ wa Jehovah rai. (Farawa 6:5, 6) Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi. Idan ka bi mummunar tafarki, kana iya ɓata wa Mahaliccinka rai. Wannan ba ya nufin cewa Allah kumami ne ko kuma wanda motsin rai ke rinjayarsa. Maimakon haka, yana ƙaunarka ne kuma ya damu da lafiyarka. A wata sassa kuma, idan ka yi abin da ke daidai, Jehovah yana farin ciki. Yana farin ciki ba domin ya sake samun wata amsa ga Shaiɗan ba amma kuma domin zai iya zama Mai Saka maka. Abin da yake son ya yi ke nan. (Ibraniyawa 11:6) Hakika Uba mai ƙauna kake da shi, Jehovah Allah!

Lada Mai Yawa a Yanzu

13. Ta yaya bauta wa Jehovah take kawo albarka a yanzu ma?

13 Ladar bauta wa Jehovah ba a nan gaba kawai za a samu ba. Matasa da yawa tsakanin Shaidun Jehovah a yanzu, suna samun albarkar farin ciki, gamsuwa, da kyakkyawan dalili kuwa. “Dokokin Ubangiji madaidaita ne, masu-faranta zuciya,” in ji mai Zabura. (Zabura 19:8) Fiye da wani mutum, Jehovah ya san abin da yake da kyau dominmu. Ta wurin annabi Ishaya, Jehovah ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi. Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.”—Ishaya 48:17, 18.

14. Ta yaya ƙa’idar Littafi Mai Tsarki za ta taimake ka ka guje wa azabar cin bashi?

14 Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimake ka ka guje wa azaba mai yawa da ɓacin rai. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce waɗanda suke son kuɗi “sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa.” (1 Timothawus 6:9, 10) Wani cikin tsararka ya fuskanci gaskiyar wannan nassin? Wasu matasa maza da mata sun nitse cikin bashi mai yawa domin suna son su sayi riguna masu sabon salo da kuma kayayyakin ɗaki na zamani. Mutum ya kasance da nauyin biyan bashi mai ruwa da yawa domin abubuwan da hakika da ba zai iya saya ba, bauta ce mai tsanani!—Misalai 22:7.

15. A waɗanne hanyoyi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ke kāre ka daga azaba da lalata take jawowa?

15 Ka yi la’akari kuma da batun lalata. Kowacce shekara, a dukan duniya, yara da yawa masu shekara daga goma sha-uku suna yin cikin shege. Wasu sukan haifi ɗa da ba su da niyyar ko kuma da ba za su iya renonsa ba. Wasu kuma suna zub da ciki kuma su sha zafin azaba ta lamiri. Akwai kuma matasa maza da mata da suke ɗaukan cuta ta wurin jima’i, kamar su ƙanjamau. Ga wanda ya san Jehovah kuma, sakamako mafi muni shi ne ɓata dangantakarsa da Jehovah.b (Galatiyawa 5:19-21) Da dalili mai kyau Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku guje ma fasikanci.”—1 Korinthiyawa 6:18.

Bauta wa ‘Allah Mai Farin Ciki’

16. (a) Ta yaya muka sani cewa Jehovah yana son ka more ƙuruciyarka? (b) Me ya sa Jehovah ya kafa maka tafarkin da za ka bi?

16 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehovah ‘Allah mai farin ciki.’ (1 Timothawus 1:11) Yana so kai ma ka yi farin ciki. Hakika, Kalmarsa ta ce: “Ka more ƙuruciyarka. Ka yi farin ciki yayin da kake matashi.” (Mai-Wa’azi 11:9, Today’s English Version) Amma Jehovah yana duba can gaba da wannan lokacin kuma ya san sakamako mai daɗewa na nagari da kuma mummunar hali. Abin da ya sa ya yi maka gargaɗi ke nan: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma [a] kwanakin ƙuruciyarka, kafin miyagun kwanaki su zo, shekaru suna gusowa kuma, inda za ka ce, Ba ni jin daɗinsu.”—Mai-Wa’azi 12:1.

17, 18. Ta yaya wata matashiya Kirista ta furta farin cikinta a bauta wa Jehovah, kuma ta yaya za mu samu farin ciki haka nan?

17 A yau matasa da yawa sun sami farin ciki mai yawa a bauta wa Jehovah. Alal misali, Lina ’yar shekara 15 ta ce: “Zan iya tsayawa da gaba gaɗi. Ina da lafiyar jiki domin na hanu daga shan taba da kuma miyagun ƙwayoyi. Ina da kāriya mai girma da ake ba ni ta wurin ikilisiya da ke taimakona in sha kan matsi da Shaiɗan yake kawowa. Ina farin ciki domin tarayya mai kyau da ni ke da shi a Majami’ar Mulki. Mafi daɗi ma, ina da begen rai madawwamin cikin duniya.”

18 Kamar Lina, matasa Kiristoci da yawa suna yaƙi ƙwarai domin bangaskiya, kuma wannan na kawo musu farin ciki. Sun fahimci cewa rayuwarsu—ko da a wasu lokatai na cike da ƙalubale—tana da ma’ana ta gaske da kuma ta nan gaba. Saboda haka, ka ci gaba da bauta wa Allah wanda yake ƙaunarka da gaske. Ka sa zuciyarsa ta yi murna, kuma zai sa ka yi farin ciki a yanzu da kuma har abada!—Zabura 5:11.

[Hasiya]

a Dubi talifin nan “The Truth Gave Me Back My Life,” da ke cikin Awake!, fitar 22 ga Oktoba, 1996.

b Abin ta’aziyya ne sanin cewa idan mutum ya tuba, ya daina yin laifi, kuma ya yi ikirarin zunubinsa, Jehovah zai yi masa “gafara a yalwace.”—Ishaya 55:7.

Ka Tuna?

• Wane haɗari ne kake fuskanta daga “mugun” Shaiɗan?

• Ta yaya za ka faranta zuciyar Jehovah?

• Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah yana damuwa da kai?

• Waɗanne albarkat ake samu daga bauta wa Jehovah?

[Akwati a shafi na 4]

Mutum Mai Adalci Ya Kusa Ya Yi Tuntuɓe

Asaph Balawi shahararren mawaƙi ne a haikalin Jehovah a Isra’ila ta dā. Ya rubuta waƙoƙi ma da aka yi amfani da su wajen bauta. Duk da gatar da yake da ita, da akwai lokaci da ya yi sha’awar halin rashin ibada na tsaransa, da suke karya dokokin Allah ba tare da wani sakamakon ba. Daga baya Asaph ya ce: “Ƙafafuna sun kusa su zāme; saura kaɗan takawata ta yi talalaɓiya. Gama na ji kishin zuci ga masu-girman kai, sa’anda na ga arzikin masu-mugunta.”—Zabura 73:2, 3.

Daga bayan, Asaph ya je haikalin Allah ya yi addu’a game da batun. Da sabon ra’ayi na ruhaniya, ya fahimci cewa Jehovah yana ƙyamar mugunta kuma a ƙarshe masu mugunta da masu adalci za su girbe abin da suka shuka. (Zabura 73:17-20; Galatiyawa 6:7, 8) Hakika, miyagu suna wuri mai santsi. A ƙarshe, za su fāɗi yayin da Jehovah ya halaka wannan zamani na rashin ibada.—Ru’ya ta Yohanna 21:8.

[Hotuna a shafi na 6]

Jehovah yana ƙaunarka da gaske, amma Shaiɗan yana neman ya halaka ne

[Hoto a shafi na 7]

Matasa da yawa suna samun farin ciki mai yawa a bauta wa Jehovah tare da wasu Kiristoci

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba