Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 2/1 p. 29
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Makamantan Littattafai
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Kana Cika Alkawuranka Kuwa?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Ka Yi Biyayya Don Ka Amfana Daga Alkawuran Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 2/1 p. 29

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Daidai ne bisa Nassi Kirista ya dafa Hannunsa a kan Littafi Mai Tsarki don ya yi rantsuwa a kotu domin ya faɗi gaskiya?

Kowanne zai tsai da tasa shawara a wannan batun. (Galatiyawa 6:5) Amma dai, Littafi Mai Tsarki bai ce kada a yi rantsuwa a faɗi gaskiya a kotu ba.

Rantsuwa abin da ake yi ne da daɗewa a ko’ina. Alal misali, a lokatan dā Helenawa suna ɗaga hannu sama ko kuma taɓa bagadi sa’ad da suke rantsuwa. Sa’ad da Baroma yake rantsuwa, yakan riƙe dutse a hannunsa kuma ya rantse: “Idan na yi ruɗu da ganga, sa’ad da Jupiter yake tsare birnin, bari [allah] Jupiter ya kawar da ni daga nagarta, yadda zan yi da wannan dutsen.”—Daga littafin nan Cyclopedia of Biblical, Theological, and Ecclesiastical Literature, na John McClintock da James Strong, kundi na VII, shafi na 260.

Irin ayyukan nan na nuna nufin mutane ne da suke sane da ikon Allah wanda yake iya ganin mutane kuma da suke ba da lissafi gare shi. Daga lokatan dā, masu bauta wa Jehovah na gaskiya sun sani cewa ya san abin da suke faɗa kuma suke yi. (Misalai 5:21; 15:3) Suna rantsuwa a gaban Allah, ko kuma cewa shi ne shaidarsu. Alal misali, Boaz, Dauda, Sulemanu, da kuma Zedekiya sun yi haka nan. (Ruth 3:13; 2 Samu’ila 3:35; 1 Sarakuna 2:23, 24; Irmiya 38:16) Masu bauta wa Allah na gaskiya ma sun yarda wasu su sa su su yi rantsuwa. Wannan haka ya faru da Ibrahim da Yesu Kristi.—Farawa 21:22-24; Matta 26:63, 64.

Mutumin da yake rantsuwa a gaban Jehovah a wasu lokatai yakan yi hakan da alama. Abram, (Ibrahim) ya gaya wa sarkin Saduma: “Na rigaya na tada hannuna ga Ubangiji, Allah maɗaukaki, mai-sama da ƙasa.” (Farawa 14:22) Mala’ika da yake magana da annabi Daniel “ya tada hannunsa na dama da hannunsa na hagu zuwa sama, ya yi rantsuwa kuma bisa ga wanda ya ke rayuwa har abada.” (Daniel 12:7) Har ma an nuna cewa Allah yana ɗaga hannunsa cikin alama a yin rantsuwa.—Kubawar Shari’a 32:40; Ishaya 62:8.

Nassi bai hana rantsuwa ba. Amma ba sai Kirista ya yi rantsuwa a kowacce magana don ya tabbatar cewa gaskiya ce ba. Yesu ya ce: “Bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a.” (Matta 5:33-37) Haka ma almajiri Yaƙub ya ce. Sa’ad da ya ce “kada ku yi rantsuwa,” yana gargaɗi ne game da rantsuwa na ba gaira ba dalili. (Yaƙub 5:12) Babu wani tsakanin Yesu da Yaƙub da ya ce yin rantsuwa don faɗan gaskiya a kotu ba daidai ba ne.

Idan aka ce Kirista ya yi rantsuwa a kotu domin ya tabbatar da abin da ya ce gaskiya ne fa? Zai iya shawarta ya rantse. Ko kuma a yarda masa ya sanar da cewa ba ƙarya yake yi ba.—Galatiyawa 1:20.

Idan a kotu ana ɗaga hannu ko kuma ana dafa shi ne a kan Littafi Mai Tsarki sa’ad da za a yi rantsuwa, Kirista zai iya shawarta ya bi hakan. Zai iya tuna da misalai na Nassi game da yin rantsuwa tare da alama. Kirista kam, abu mafi muhimmanci gare shi sa’ad da yake rantsuwa shi ne yana tuna cewa yana rantsuwa ne a gaban Allah, ya faɗi gaskiya. Irin rantsuwar nan batu ne mai tsanani. Idan Kirista yana jin zai iya kuma ya kamata ya amsa tambayar da aka yi masa a irin yanayin nan, to, sai ya tuna cewa dole ne ya faɗi gaskiya, abin da ya kamata Kirista ya yi ke nan kullum.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba