Lamiri Mai Kyau
CHARLES da yake aiki a wata jami’a a Kenya, ya ɓatar da tarhonsa na selula da yake koma gida bayan aiki wata rana. A Kenya, har ila wannan alatu ne mai tsada.
“Ban yi tsammani wani zai mai da selula ba,” in ji Charles. Amma, bayan ’yan kwanaki, ya yi mamaki da ya amsa waya daga ofishin reshe na Shaidun Jehovah a Kenya. Ya yi mamaki sosai sa’ad da aka ce ya je ya karɓa tarhonsa na selula! An gaya masa cewa wani Mashaidin Jehovah mai hidima na cikakken lokaci da ya shiga mota ɗaya da Charles ne ya tsinto. Da mashaidin yake ƙoƙari ya nemi mai tarho ɗin, mai hidimar ya kai tarhon zuwa ofishin reshe, kuma masu aiki a wajen daga baya suka sami Charles ta kiran lambar da ke tarhon.
A wasiƙar da ya rubuta zuwa ofishin reshe, Charles ya ce: “Na yi godiya sosai da ƙoƙari da aka yi a neme ni. Na gode wa ɗan ƙungiyarku da ya tsinto tarho ɗin, ya gano cewa nawa ne, ya kuma mayar mini. Ba shi da sauƙi a yau a sami mai yin gaskiya, amma yana da kyau cewa muna da kalilan da su Shaidun Jehovah Allah ne na gaskiya.”
An san Shaidun Jehovah a ko’ina da yin gaskiya. Suna koyi da manzo Bulus, wanda ya ce: “Mun kawarda shakka muna da kyakkyawan lamiri, muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibraniyawa 13:18; 1 Korinthiyawa 11:1) Sun fahimta cewa irin wannan hali yana ɗaukaka Jehovah Allah, yadda Yesu ya ce: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.”—Matta 5:16.