Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 1/1 pp. 3-6
  • Ta’aziyya Ta’aziyya Domin Waɗanda Suka Wahala

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta’aziyya Ta’aziyya Domin Waɗanda Suka Wahala
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Wahala ta Fara?
  • Warware Batun
  • Ƙarshen Wahala
  • Ta’aziyya ga Waɗanda Suke Wahala
  • Me Ya Sa Akwai Mugunta da Wahala a Ko’ina?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Za Mu Amfana Idan Muka Jimre Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 1/1 pp. 3-6

Ta’aziyya Ta’aziyya Domin Waɗanda Suka Wahala

DUK cikin ƙarnuka da suka shige tambayar nan, me ya sa Allah ya ƙyale mutane su wahala, ya dami masu ussan ilimi da kuma ’yan tauhidi. Wasu sun ce tun da yake Allah ne mai iko duka, lallai shi ne ke da alhakin wahalar mutane. Marubucin The Clementine Homilies, wani aikin bincike na ƙarni na biyu na afokirifa, ya yi da’awar cewa Allah yana sarautar duniya da hannunsa biyu. Iblis yana haddasa wahala da azaba, da “hannun hagu,” Yesu kuma yana ceto yana ba da albarka da “hannun dama.”

Wasu, ba su yarda da cewa Allah ya ƙyale wahala ba, ko idan shi yake haddasa ta, sun ƙi cewa ana wahala ma sam. Mary Baker Eddy ta rubuta: “Mugunta ruɗu ne, ba ta da tushe.” “Idan an aza cewa zunubi, ciwo, da kuma mutuwa ba kome ba ne, za su ɓace.”—Science and Health With Key to the Scriptures.

Sakamakon aukuwa masu ban tausayi na tarihi, musamman daga yaƙin duniya na farko har zuwa zamaninmu, mutane da yawa sun kammala da cewa Allah dai ba zai iya kawar da wahala ba. “A ganina, ƙunar baƙin wake, ta kawar da ra’ayin cewa Allah ne mai iko duka gaba ɗaya,” in ji Bayahude manazarci David Wolf Silverman. Ya daɗa cewa “da a ce za a fahimci Allah, to, nagartansa ta jitu da wanzuwar mugunta, wannan zai yi daidai idan ba shi ke da iko duka ba.”

Da’awar cewa Allah yana goyon bayan wahala a wata hanya, ba za ta iya kawar da ita ba, ko kuma wai wahala wata ƙage ne, ba za ta iya kawo ta’aziyya ba ga waɗanda suke wahala. Abu mafi muhimmanci, irin imanin nan sun saɓa ƙwarai da Allah wanda Littafi Mai Tsarki ya bayyana shi mai gaskiya, mai ƙarfi, kuma mai kula. (Ayuba 34:10, 12; Irmiya 32:17; 1 Yohanna 4:8) To, Littafi Mai Tsarki ya ba da wani dalili ne da ya sa aka ƙyale wahala?

Yaya Wahala ta Fara?

Allah bai halicci mutane su wahala ba. Maimako haka, ya ba ma’aurata na farko, Adamu da Hauwa’u, kamiltaccen azanci da jiki, ya shirya musu lambu mai kyau ya zama gidansu, kuma ya ba su aiki mai gamsarwa, mai kyau. (Farawa 1:27, 28, 31; 2:8) Amma, idan za su ci gaba da farin ciki wannan ya dangana ga daraja sarautar Allah da kuma ikonsa na tsai da abin da ke nagarta da mugunta. Wannan farilla ta Allah an wakilce ta da itace da aka kira “itace na sanin nagarta da mugunta.” (Farawa 2:17) Adamu da Hauwa’u za su nuna sun miƙa kansu ga Allah idan sun yi biyayya ga umurninsa na kada su ci itacen.a

Abin baƙin ciki, Adamu da Hauwa’u suka kasa yin biyayya ga Allah. Wani halittar ruhu ɗan tawaye, wanda daga baya aka san shi da Shaiɗan Iblis, ya hudubantar da Hauwa’u cewa idan ta yi biyayya ga Allah ba zai amfane ta ba. Yana mai cewa Allah yana hana ta wani muhimmin abu mai daraja: ’yancin kai, ikon zaɓan abin da ke nagarta da mugunta. Shaiɗan ya yi da’awar cewa idan ta ci daga itacen, ‘idanunta za su buɗe kuma za ta zama kamar Allah, ta san nagarta da mugunta.’ (Farawa 3:1-6; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Da yake ta jarabu da ’yancin kai, Hauwa’u ta ci itacen da aka haramta, sai kuma Adamu ya yi haka nan.

A ranar, Adamu da Hauwa’u suka soma shaida sakamakon tawayensu. Da suka ƙi sarauta ta Allah, sun yi hasarar kāriya da kuma albarka wadda yin biyayya ga Allah za ta kawo musu. Allah ya kore su daga Aljanna kuma ya gaya wa Adamu: “Sabili da kai an la’anta ƙasa; da wahala za ka ci daga cikinta duk muddar ranka; sai da jiɓi a fuskarka za ka ci abinci, har kuma ka koma ƙasa.” (Farawa 3:17, 19) Adamu da Hauwa’u suka soma ciwo, da shan azaba, da tsufa, da kuma mutuwa. Wahala ta zama ɓangaren rayuwar mutum.—Farawa 5:29.

Warware Batun

Wani zai iya tambaya, ‘Me ya sa Allah bai mance da zunubin Adamu da Hauwa’u ba kawai’? A’a, domin wannan zai daɗa rage darajar ikonsa, ƙila ma ya daɗa jawo wani tawaye da zai iya haddasa wahalar da ta fi wannan. (Mai-Wa’azi 8:11) Ban da haka, ƙyale irin wannan rashin biyayyar zai nuna cewa Allah yana da hannu cikin mugunta. Marubucin Littafi Mai Tsarki, Musa ya tunasar da mu: “Aikin [Allah] cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, marar-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:4) Ta bin ƙa’idarsa, Allah ya ƙyale Adamu da Hauwa’u su sha wahalar sakamakon rashin biyayyarsu.

Me ya sa Allah bai halaka ma’aurata na farko tare da Shaiɗan nan da nan ba, shi wanda ya hadassa tawaye? Yana da ikon yin haka. Da Adamu da Hauwa’u ba su haifi ’ya’yan da za su bar musu gadōn wahala da mutuwa ba. Amma irin wannan nuna ikon Allah ba zai jitu da daidaitar ikon Allah a kan halittunsa masu basira ba. Ƙari ga haka, da Adamu da Hauwa’u sun mutu babu ’ya’ya, wannan zai nuna kasawar ƙudurin Allah su cika duniya da ’ya’yansu kamilai. (Farawa 1:28) “Allah ba kamar mutum ba ne . . . Duk abin da ya yi alkawarin, yana yi; idan ya yi magana, tana cika.”—Litafin Lissafi 23:19, Today’s English Version.

A cikin cikakkiyar hikimarsa, Jehovah Allah ya yanke shawarar ya ƙyale tawayen ya ci gaba na ɗan lokaci. ’Yan tawayen za su samu isashen lokaci su ɗanɗana sakamakon ’yancin kai daga Allah. Aukuwa na duk rayuwar mutane ya nuna sarai bukatar da mutane suke da shi na ja-gorar Allah da kuma fifikon sarautar Allah a kan na mutane ko kuma na Shaiɗan. Ban da haka, Allah ya ɗauki mataki ya ga cewa ƙudurinsa na asali domin duniya ya cika. Ya yi alkawarin cewa “zuriya,” ko kuma ‘ɗa,’ zai zo wanda zai ‘ƙuje Shaiɗan a kai,’ ya kawar da tawayensa gabaki ɗaya da kuma mummunar sakamakonsa.—Farawa 3:15, hasiya na NW.

Yesu Kristi ne Zuriya da aka yi alkawarinsa. Mun karanta a 1 Yohanna 3:8, cewa: “Bayyanuwar Ɗan Allah ke nan, shi halaka ayyukan Shaiɗan.” Kuma ya yi wannan ta ba da ransa na mutum kamili da kuma biyan farashin fansar domin ya fanshi ’ya’yan Adamu daga zunubi da mutuwar da suka gada. (Yohanna 1:29; 1 Timothawus 2:5, 6) Waɗanda suka ba da gaskiya ga hadayar Yesu an yi musu alkawarin samun sauƙi daga wahala ta dindindin. (Yohanna 3:16; Ru’ya ta Yohanna 7:17) Yaushe wannan zai faru?

Ƙarshen Wahala

Ƙin ikon Allah ya jawo wahaloli mai yawa. Saboda haka, ya dace Allah ya yi amfani da ikonsa na musamman ya kawo ƙarshen wahalar ’yan Adam kuma ya cim ma ƙudurinsa na asali domin duniya. Yesu ya ambata wannan tanadi na Allah lokacin da ya koyar da mabiyansa su yi addu’a haka: “Ubanmu wanda ke cikin sama, . . . Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Matta 6:9, 10.

Lokacin da Allah ya ba wa mutane su gwada da gwamnatin kansu ya kusa ya ƙare. A cika annabcin Littafi Mai Tsarki, an kafa Mulkinsa a sammai a shekara ta 1914, Yesu Kristi ne Sarkinsa.b Ba da daɗewa ba, zai ragargaje kuma ya kawo ƙarshen dukan gwamnatin mutane.—Daniel 2:44.

A lokacin ɗan hidimarsa a duniya, Yesu ya yi tanadin alamar albarkar da maido da sarautar Allah zai kawo ga ’yan Adam. Lingila ta nuna tabbaci cewa Yesu ya nuna juyayi ga mutane cikin jam’iyyar da su matalauta ne kuma ake musu wariya. Ya warkar da masu rashin lafiya, ya ciyar da mayunwata, kuma ya tashi matattu. Ko ikon halittu ma sun yi biyayya gare shi. (Matta 11:5; Markus 4:37-39; Luka 9:11-16) Ka yi tsammanin abin da Yesu zai cim ma sa’ad da ya yi amfani da ikon hadayarsa ta fansa ya amfani dukan ’yan Adam masu biyayya! Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari ta wurin sarautar Kristi cewa, Allah “za ya share dukan hawaye daga idanun [mutane]: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba” ba.—Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Ta’aziyya ga Waɗanda Suke Wahala

Abin farin ciki ne mu sani cewa Allahnmu, mai ƙauna kuma mai iko duka, Jehovah, yana kula kuma ba da daɗewa ba zai kawo sauƙi ga mutane! Hakika, wanda yake rashin lafiya mai tsanani zai yarda da maganin da zai warkar da shi ko maganin yana da zafi. Haka nan ma, idan mun sani cewa yadda Allah yake bi da al’amura zai kawo madawwamin albarka, sanin wannan zai taimake mu ko da yaya yawan wahalar da za mu fuskanta take.

Ricardo, wani ne da ya koyi samun ta’aziyya daga alkawuran Littafi Mai Tsarki. “Bayan mutuwar matata, na so na kaɗaita kaina ƙwarai,” in ji shi, “amma bai daɗe ba na farfaɗo a fahimtar cewa wannan ba zai dawo da matata ba kuma zai daɗa munin yanayin motsin rai na ne kawai.” Maimakon haka, Ricardo ya bi tsarinsa na halartar taron Kirista kuma yana gaya wa wasu saƙon Littafi Mai Tsarki. “Da na ga goyon bayan Jehovah na ƙauna kuma na lura da yadda yake amsa addu’o’ina a kan ƙananan abubuwa, ya sa na matsa kusa da shi,” in ji Ricardo. “Sanin ƙaunar Allah ya sa na jimre wa abin da lallai gwadi mafi girma ne da na fuskanta.” Ya ce: “Har ila ina son ganin matata, amma na tabbata cewa duk abin da Jehovah ya ƙyale ya faru mana ba zai kawo lahani na dindindin ba.”

Kamar Ricardo da wasu miliyoyin mutane, kai ma kana fatar lokacin da wahalar mutane na yanzu za ta zama “al’amura na dā . . . ba kuwa za su shiga zuciya ba”? (Ishaya 65:17) Ka tabbata cewa albarkar Mulkin Allah abin da za ka iya samu ne idan ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki: “Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kiransa tun yana kusa.”—Ishaya 55:6.

Domin taimakon yin wannan, ka sa karatu da kuma nazarin Kalmar Allah da kyau ya zama muhimmin abu a rayuwarka. Ka san Allah da kuma wanda ya aiko, Yesu Kristi. Ka yi ƙoƙari ka yi rayuwa da ta jitu da mizanan Allah kuma ka nuna kasancewarka a shirye ka yi biyayya ga ikon mallakarsa. Irin wannan mataki zai kawo maka farin ciki mai yawa yanzu duk da gwadi da kake fuskanta. A nan gaba, za ka more rayuwa cikin duniya da babu wahala.—Yohanna 17:3.

[Hasiya]

a A hasiyarsa domin Farawa 2:17, The Jerusalem Bible ya bayyana “sanin nagarta da mugunta” cewa “ikon tsai da shawarar . . . abin da ke nagarta da mugunta ne kuma aikata daidai da wannan, zaman ’yancin kai da mutum ya ƙi ya san matsayinsa na cewa shi halitta ne.” Ya daɗa: “Zunubi na farko farmaki ne a kan ikon mallaka na Allah.”

b Domin cikakken bayani na annabcin Littafi Mai Tsarki da ke game da shekara ta 1914, dubi babobi 10 da 11 na littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, Shaidun Jehovah ne suka buga.

[Akwati a shafi nas 4, 5]

TA YAYA ZA MU JURE WA WAHALA?

“Kuna zuba dukan alhininku a bisa [Allah].” (1 Bitrus 5:7) Ɗimaucewa, fushi, da kuma jin an yi banza da mutum halin ’yan Adam ne yayin da muke jure wa wahala ko kuma muka ga wani da muke ƙauna yana shan wahala. Duk da haka, ka tabbata cewa Jehovah ya fahimci yadda muke ji. (Fitowa 3:7; Ishaya 63:9) Kamar ubanni masu aminci na dā, za mu iya buɗe zukatanmu gare shi kuma mu furta masa shakkarmu da kuma alhini. (Fitowa 5:22; Ayuba 10:1-3; Irmiya 14:19; Habakkuk 1:13) Hakika ba zai kawar da gwadinmu ta wurin mu’ujiza ba, amma zai saurara ga addu’o’inmu daga zuci, ya ba mu hikima da ƙarfi mu jure musu.—Yaƙub 1:5, 6.

“Kada ku yi mamakin irin gwadi mai tsanani da kuke sha, kamar wani sabon abu ne ke faruwa a gare ku.” (1 Bitrus 4:12, New International Version) A nan Bitrus yana zancen tsanani ne, amma ana iya amfani da kalmominsa ma ga duk wahalar da wani mai bi ke jurewa. ’Yan Adam suna wahala da rashin biyan bukata, ciwo, da kuma rashin waɗanda suke ƙauna. Littafi Mai Tsarki ya ce ‘sa’a da tsausayi’ sukan sami kowannenmu. (Mai-Wa’azi 9:11) Irin waɗannan abubuwa sashen yanayin mutane ne yanzu. Sanin wannan zai taimake mu mu bi da wahala da kuma tsausayi sa’ad da suka auku. (1 Bitrus 5:9) Fiye da kome, tunawa da tabbacin cewa “idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙararsu,” lallai zai zama abin ta’aziyya ƙwarai.—Zabura 34:15; Misalai 15:3; 1 Bitrus 3:12.

“Kuna murna cikin bege.” (Romawa 12:12) Maimakon mu yi ta tunanin yadda muke farin ciki dā, za mu iya yin bimbini a kan alkawarin Allah ya kawo ƙarshen dukan wahala. (Mai-Wa’azi 7:10) Wannan bege tabbatacce zai kāre mu kamar kwalkwali. Bege yana sauƙaƙa tsausayi da ke faɗa mana a rayuwa kuma yana taimakonmu kada su yi mana lahani ainun ga hankali, motsin rai, ko kuma lafiyarmu ta ruhaniya.—1 Tassalunikawa 5:8.

[Hoto a shafi na 4]

Adamu da Hauwa’u sun ƙi sarautar Allah

[Hoto a shafi na 6]

Allah ya yi alkawarin duniya da babu wahala

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba